Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 50 of 86
Ko da Maman Taufiƙ ta shigo har mun fara cin ƙarfin aikin, tare da ita aka dafa jallop ɗin shinkafa. Sannan aka yi musu tuwon da za su je da shi gida bayan jinjer drink.
Najib mai adaidatana na kira a waya ya siyo mana ƙanƙara da nufin idan ya zo na ba shi kuɗin. Babu ɓata lokaci ya siyo mini ya kawo na biya shi, aka baza ta cikin jinjar da aka shaƙe kula biyu da ƙullinta.
Muna tsaka da haɗa kayan Mukhtar ya shigo gidan ya kira Mamar Sajida, wasu manyan ledodi biyu ya miƙa mata yana faɗin,
"Don Allah a saka musu yadda na bayar kada a bari a taɓa musu komai."
Ban bari na sake kallon inda yake ba ma balle abin da yake faɗin kada a taɓa. Sajida kawai ta kira tana faɗin ta samo wata kula a kitchen a saka musu naman kajin a ciki.
Shock na yi da jin maganar kajin, nan take raina ya ɓaci ta yadda har na kasa ɓoye damuwa a kan fuskata. Miƙewa na yi ina faɗin,
"Bari na kawo miki don kulolin suna É—akina kuma na rufe."
Ba ƙaramar jarumta na yi wurin haɗa kalmomin ba, saboda muryar kuka da ke ƙoƙarin tona asirin zuciyata. Toilet na shige na yi kukan rabin lokaci, sannan na wanke fuskata na fito na ƙara goga mai na bi da 'yar hoda sama.
Kulolin na ɗauko a cikin durowar Kitchen ɗina da na kulle da makulli. Sannan na rufe ina ƙoƙarin ɗagowa na ga Sajida a saman kaina, murmushi ta yi mini tana ƙoƙarin goge hawayen fuskarta ta ce,
"Ki yi haƙuri Aunty! Duk da na san ba a kyauta miki. Amma kuma hakan ba zai hana na ba ki haƙurin ba, don na fahimci ba ki ji daɗin abin da Baba Mukhtar ya ce ba."
"Kada ki damu! Na saba da halinsa ko kaɗan ban ji komai a kan zancensa ba. Kuma ai yana da gaskiya, idan ba mu ƙara ba ba zai yiyu mu rage musu ba."
Ina ƙare faɗar hakan muka fito kitchen ɗin muka koma tsakar gidan. A nan na ji Mamar Sajidar sun haɗa kai da wata 'yar'uwarsu, suna ta gulmar kayan ɗakin amarya.
"Ni fa ina ganin kamar ba sababbi ba ne fenti ne."
"Da gaskiyarki Maimuna! Don ko kujerun gyaransu aka yi ba sabon katako ba ne."
Murmushi na yi mai sauti sannan na matso kusa da su na ce,
"Kaya ba su ne aure ba Yaya Maimuna, ku yi musu fatan zaman lafiya sai ya fi yi da sun da kuke yi."
Kallon juna suka fara yi a muzance, kafin Yaya Maimunar ta ja kular da Sajida ta ajiye gefenta tana faÉ—in,
"Iyayi ne fa saka suruka makarantar boko. Tun da ya samu mai son sa tsakani da Allah ko yau ya mutu ya bar tarihi. Don ya ƙwaci wuyan hannunsa daga muguwar damƙar da aka yi masa."
Murmushi kawai na yi mata na bar wurin, saboda idon Sajida da ke kanmu. Kuma na tabbatar da duk abin da zan faɗa a wannan lokacin ba mai daɗi ba ne, kuma dole sai ta ji zafi domin ba zan yi ƙasa a gwiwa wurin rama daidai abin da ta faɗa mini ba, wataƙila ma na zarce awa wurin ƙoƙarin mayar da raddin na ci zarafinta a banza wofi."
Hmmmmm! Shiru ma ai magana ce Zaituna.😢
D.AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*LAMBA TALATIN.*
Abincin Sajida ta zuba mana a ƙaton tire, ni da ita da Maman Taufik muka yi ɗakina. Yayin da muka bar Yaya Maimuna da sauran dangin Mukhtar a nan suna cin nasu.
Muna ɗakina muna ta hira bayan mun gama cin abincin. Ban san ya aka ƙare da 'yan jeren ba, har sai da suka zo ƙofar ɗakina suna yi mini godiya, tare da sallama a kan sun ƙare za su tafi.
Sauka lafiya na yi musu a bakin ƙofar ɗakin ban fita ba, a gabana suka fice ɗauke da kulolin abincin da aka ba su. Na dawo ɗakin inda su Maman Taufiƙ da Sajida suke ta hirar amaryar da kayan ɗakinta.
Zama na yi ina 'yar dariyar yaƙe na ce da su,
"Idan ba ku daina gulmar matar mutane ba, zan faÉ—a wa mijinta ya É—auki mataki kanku."
Maman TaufiÆ™ ta maka mini jar harara tana faÉ—in, "Gaskiya ce muke faÉ—a kuma ke ma kin sani, don duk wanda ya gan ki ya san zaman boranci kawai amaryar ta zo yi a gidan Abban su Haidar."
"Kin taɓa ganin inda namiji zai zuba kuɗinsa ya yi auren so don huce haushi; sannan a kira amaryar da boranci a gidansa?"
Na ƙare maganar tare da kafe ta da ido ina murmushi, Sajida ce ta yi hanzarin ba ni amsa da cewa,
"To ita dai wannan amarya Aunty; babu abin da zai tsinta a jikinta face kayan haushi da takaici. Ba ki gan ta ba fa! Yar firit da ita babu kumarin jiki balle gaba ko baya. Ta tafi 1 tamkar taɓaryar da ta shekara jingine cikin rana, ta bi duk ta ƙarmashe sai ɗan banzan son kuɗi ga surutun masifa."
Baki na rufe ina dariya saboda yadda Sajida take maganar tana yatsinar fuskar, tamkar ta hango wani abin ƙyama. Maman Taufiƙ kuma dariyar mugunta kawai take yi saboda an mata abin da take so.
Ina ƙoƙarin yin magana kiran Amina ya shigo wayata, da hanzari na ɗauka saboda tuno ban sanar da ita labarin auren ba. Ƙorafi ta fara yi mini a kan rashin zuwana ofis, sannan ta ƙare da tambayar lafiya ko jikina ne ya motsa. Ina murmushi kamar a gabanta na ce,
"Hidimar amaryar Mukhtar muke yi. Gobe za a yi walima jibi a kawo amarya, idan da hali ki zo mana bikin ko na rana É—aya ne."
'Aure!!!?'
Tambayar da ta yi kenan cikin É—aga murya, domin sautin da ta yi maganar da shi ya tabbatar mini; da mamakin auren da ta ji na ambata. Gaskiyar hasashena ya fito a cikin amsar da ta ba ni kai-tsaye muryarta tana rawa.
'CabÉ—ijam! Daman can kin san da batun auren ne? Ko kuwa yadda kika sanar da ni a sama haka ke ma kika ji shi?'
"Na san da batun auren tuni, kawai dai ke ce Allah ya mantar da ni ban faÉ—a miki ba."
Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi sannan ta ce, "Ba zan samu zuwa gobe ba sai ranar bikin. Allah ya ƙara miki haƙuri da juriya. Mutanen wurinmu suna ta tambayar lafiya ba ki fito aiki ba jiya da yau. Na faɗa musu abin da MD yake sanar musu cewar ba kya jin daɗin jikinki."
"Yawwa! Mutuniyata! Kin kyauta da yawa, ki gaishe da kowa don gobe ma da wuya na fito."
Na ƙare maganar ina rufe baki don na san sai ta yi wani ƙorafin bayan wanda ta yi.
"Gaskiya dai ki daure ki zo ko ba ki daÉ—e ba ki koma, saboda aikinki ya yi wa MD yawa ko yau sai da na rage masa wani a madadinki."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.