Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 25 of 86
Ajiyar zuciya Inna Kulu ta sauke sannan ta ce, "Ni wannan zama naku Zaituna, ban taɓa ganin irin shi ba sai gare ku. A ce ko kaɗan babu jituwa tsakanin mace da mijinta; to ya ya za ku fahimci juna balle ku nemo hanyar gyara domin ku gyara zamantakew...?"
"Ita ma ai tana da matsala, babbar matsalar Zaituna a rayuwa bai wuce kafiya ba. Da tana bin shawarar da muke ba ta da tuni ta zauna lafiya mu ma ta bar mu mun huta. Amma duk abin da kika ce ta yi sai ta nuna miki ta fi iyawa. To zama da Mukhtar ya zama dole ko don 'ya'yanta, tun da tun farko ba ta bayyana mana matsalar shi da wuri ba. Balle a taro tun kafin ta yi tsanani, har sai da komai ya lalace sannan ta faÉ—a bayan ta fara tara zuri'a da shi."
Maganar Umma kenan da muka ji a sama ba tare da mun ji shigowar ta É—akin ba, sai da ta ja numfashi sannan ta sake cewa,
"Na sani Mukhtar bai yi mata halacci ba mu ma bai yi mana ba, amma babbar matsalar shi ne yaran da ke tsakaninsu. Mahaifiyar shi ba ta duniya balle a miƙa mata yaran, domin ta san yadda za ta yi da su, shi kuma ba ɗa ba ne balle a ce za a bar masa su hannun shi. Sannan kaf dangin shi babu mai zuciyar riƙa masa 'ya'ya tsakani da Allah balle a kai musu su karɓa, saboda zuri'arsu kaf babu haɗin kan taimakon juna balle a share wa ɗan'uwa kuka. Babbar matsalar ita ce a cikin gidan ma tarbiyyar yaran za ta fara gurɓacewa ba sai an je nesa ba. Domin idan kin manta na tuna miki, sau nawa suna neman 'ya'yanki da lalata Allah yana tsarewa kafin ki baro gidan?"
Ta ƙare maganar a fusace cikin ɗaga murya, saboda fuskarta ta nuna kai wa ƙoluwar ɓacin rai. Kafin na ba ta amsa ta ƙara da cewa,
"Lokacin da kika daka yaji kika zo gidan nan, watanki biyu ana faɗi-tashi da yaran, nawa Mukhtar ya kawo mana domin mu ciyar da su ko a yi musu wata lalura? To a haka kike so na kawo ki gidan nan ke da yaranki ya bar mu ciyar da ku da sauran laluro, shi ya rungume hannun shi ya zuba mana ido? To ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa. Sawunki a likkafa ki ɗauki jakarki ki koma tun kafin wankin hula ya kai ki dare, baƙincikin ɗa namiji ba a kanki aka fara ba kuma ba za a ƙare kanki ba. Kula da tarbiyyar yaranki ya fi miki alkhairi da neman wani matsugunnin da kike yi. Saboda inda kika sani kin raina shi, shi kuma inda za ki je an raina ki."
Tana ƙare faɗar hakan ta fice, mintuna a tsakani na ji tana magana a waya. "A kawo yaran nan idan ta tashi ta koma tare da su. To idan sun dawo a kawo mata su."
Daga ni har Inna Kulu babu wanda ya yi motsin kirki balle mu samu kuzarin cigaba da bitar maganganun. Domin har zuciyata na gamsu da zancenta ɗari bisa ɗari, saboda ta tunanar da ni wasu abubuwan da na manta a baya. Hakan ya sa na yi ammana da Mukhtar ne ƙaddarata a cikin duniya, wanda ban da ikon gyara ƙaddarar ta dawo mini daidai yadda nake so; har sai ranar da Allah ya kawo mini sassauci da mafita a cikin rayuwata da ta 'ya'yana.
Inna Kulu ta tashi ta fice, mintina a tsakani ta dawo ɗauke da kofin kunu da ƙosai a ƙaramin faratin silba. Gabana ta ajiye tana faɗin,
"ÆŠauki ki karya sannan ki bar wa Allah lamarinki, in Sha Allah za ki ga haske a gaba muddin kika cusa wa zuciyarki dangana, kuma kika bi abin da Mahaifiyarki take so."
Ban musa ba na sauko daga kan gadon na fara shan kunun, domin shi kaɗai nake jin zai iya shiga cikina. Ko shi saboda yunwar da nake ji maƙoshina har ya fara bushewa.
Kasancewar yaran sun je makaranta, bai kawo su ba har sai da aka gama sallar juma'a. Sannan suka shigo da gudu suna ihun murna tare da ƙwala mini kira, tarbon su na yi fuskata ɗauke da mayalwacin murmushi. Jikina suka faɗo dukansu suka rungume ni, ni ma na rungume su ƙam-ƙam. Nan take damuwa ta ziyarce ni har ta bayyana kan fuskata.
Saboda kukan da Ummu Salma da Iman suke yi. Jan su na yi muka ƙarasa cikin ɗakin ina faɗin,
"Ya isa, ku daina kukan haka."
Haidar riƙe da hannuna ya ce, "Mama wai da gaske kin ce ba za ki sake zama gidan Abbanmu ba?"
Kallo na ƙura wa fuskar shi kafin na ce, "Wa ya faɗa maka?"
"Abbanmu ne ya ce dama mun daina kuka don kin ce ba za ki sake zama da mu gidan ba, shi ya sa da dare kika tafiyar ki kika bar mu."
Amsar da Ummu Salma ta yi hanzarin ba da ni kenan tun kafin Haidar ya faÉ—a.
Ajiyar zuciya na sauke sannan na ce, "Ko ma dai mene ne ina tare da ku abadan in Sha Allah! Ku je ku gayar da Umma." Har sun fice Iman ta dawo tana goge hawaye ta ce, "Abbanmu yana wurin Umma da Baba Sale suna magana."
Zumbur na miƙe saboda na san sharri da ƙage irin na Mukhtar, abu kaɗan zai iya juya shi zuwa babba. Balle ganin da ya yi mini tare da MD komai zai iya faɗa domin ya jaza mini wani sabon tashin hankali na daban.
"Wallahi Umma da idona na gan ta tare da shi a ƙofar wani gida, kuma a gabana ta shiga motar shi suka tafi tare da 'yansan..."
"Ban katsi hanzarinka ba Mukhtar! Amma mutumin nan ya faɗa mini duk abin da ya faru a lokacin da ya kawo ta gidan nan. Asali ma ban da shi; da tuni an cutar mana da ita saboda sakacinka. Kada ka ga ina zuba maka ido kana zaluntar mini yarinya ka ɗauka ba na son ta. Wallahi duk girman mutuncin da kake gani ina yi maka albarcin 'ya'yanka kake ci. Domin ni ba ki yi mini halacci ba kuma ba ka yi wa Zaituna adalci ba. Saboda ta nuna maka ƙauna kuma ta yi maka rufin asirin da a tara mata dubu ba za su iya yi maka irin shi ba. Mutumin da kake aibatawa kuma, mahaifiyar shi ya kai asibiti a daidai lokacin da taƙadarun suka biyo ta. Saboda ciwon asma gare ta wanda tashin shi cikin daren ya yi sanadin ceton Zaituna. Domin ba don ta ya fito ba, kuma ita ma ba wurin shi ta je ba, amma idan har ba ka yarda da zancen ba; kana da damar ɗaukar mataki daidai da laifin da kake ganin ta yi maka."
Maganganun da na ji kenan a lokacin da na durfafi É—akin Kawu Sale, saboda a can ne mahaÉ—armu a duk lokacin da aka zo sansancin rikicinmu ni da shi.
Hawayen daɗi na goge a fuskata na sha jinin jikina a bakin ƙofar, saboda ba ƙaramin farinciki zancen Ummata ya saka ni ba.
'Ashe har yanzu Umma tana so na.'
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.