Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 46 of 86
A haka muka kai ƙarshe ta turo da account na yi mata transfer, sannan Maman Taufiƙ ta kira mini mai ɗinkinta ya zo muka ba shi kayan, Bayan mun zaɓi wanda zai yi mana a wayarsa. Shi ma na ba shi 10k deposit ta account ɗinsa, ya tafi bayan ya yi mana alƙawarin zai haɗa ɗinkin a cikin kwana uku.
Sauran kayan na saka a leda na yi gida, zuciyata cike da nishaÉ—in. Ko babu komai zan yi wa Mukhtar barazana tare da gayyar danginsa da zugar mutanen amarya.
Yaran ma da na sanar da su suka shiga tsalle suna murnar sun yi sababbin kaya. Ummu Salma kaÉ—ai ce na hango damuwa a kan fuskarta, hakan ya sa na tattara kayan na mayar a leda na bai wa Iman ta kai É—akinmu. Sannan na zaunar da ita na gyara zamana na ce,
"Damuwar me ce na gani a kan fuskarki?"
Hawaye ta goge sannan ta ce, "Wai da gaske Abbanmu aure zai yi?"
"E gaske ne! Me ya faru?"
Amsar da na ba ta kenan ina haÉ—e fuska, domin ba na so ta É—ora wa kanta takaicin auren. Ta hana kanta sukuni a banza a kan abin da ko ni ban da ikon hanawa balle ita.
"Wace ce zai aura?"
"Ko ma wace ce, idan ta zo ai za mu gan ta. Don haka idan ma damuwa kike yi a kan auren nan da Abbanku zai yi ki daina tun wuri, saboda babu wanda ya isa ya sauya abin da Allah ya ƙaddara. Shi ya ke sa a yi, kuma shi yake hanawa, idan ya nufa babu wata damuwar da zai sauya abin da aka rubuta. Idan kuma bai ƙaddara ba, duk yadda aka kai ƙololuwar son abin sai an bar shi dole."
"To Allah ya sa tana da kirki."
"Ko tsiya take yawo a jikinta babu abin da ya shalle mu, don ba a kanmu za ta zauna ba."
Amsar da na ba ta kenan raina a ɓace, saboda maganganunta sun dawo mini da jin zafin auren sabo. Cikin tsananin ɓacin rai na fara nuna su da hannu na ce,
"Duk wanda ya yi gangancin shiga shirgin amaryar nan, sai na saɓa masa. Ku tsaya inda Allah ya ajiye ku, hakan sai ya fi mini alheri da ku shiga hurumin da ba naku ba. Sannan ku yi nesa da duk abin da zai sa a ga laifinku, don ta wannan hanyar ne kawai za mu tattara komatsan matsalar duka mu wurgar gefe, domin a zauna lafiya mu huta da hayaniya."
Yanayin fuskokinsu ya tabbatar mini da maganganuna da kashedin da na yi musu, sun shiga kansu da kyau sun zauna. Na miƙe da ledar kayan da Maman Taufiƙ ta ba ni na yi ɗaki, zuciyata sai zafi take yi mini a kan tsananin kishin auren da nake ji a raina.
Ina É—akin na jiyo sallamar TaufiÆ™ yana faÉ—in,
"Ku bai wa Mamarku in ji Mamata."
Haidar ya shigo da leda baƙa ya miƙo mini, tun kafin na karɓa na ji ƙamshin naman kaji. Na karɓa na ce ya yi masa godiya, ya ce da ni ai ya wuce, na buɗe ledar na ɗauki yanka ɗaya na miƙa masa sauran na ce su je su raba.
Duk ƙaunata da naman kaji, haka na ajiye shi a kan bed side na kwanta ina ta ƙuncin rai. Saboda tunanin lefen da ya yi bai faɗa mini ba balle ya nuna mini na gani, sannan ni bai ba ni ko falle ɗaya ba balle na rage takaicin da yake ƙoƙarin cusa mini.
Wayata da ke ruri ta katse mini tunanin da nake yi, da hanzari na É—auka ina sauraron abin da Ummata take cewa,
"Yanzu Zaituna Mukhtar zai yi aure amma ba ki sanar da mu ba?"
"Ki yi haƙuri!"
Abin da na iya cewa kenan bayan na sauke ajiyar zuciya mai fito da feshin iska 'Huuuuuu!'
"Shi kenan! Allah ya ba ku zaman lafiya. Zuwa gobe zan aiko miki da sababbin kujeru, idan an zo za a É—auki naki a kawo mini."
"Na gode sosai Allah ya ƙara buɗi."
Iya maganar da na yi kenan ta kashe wayar, hawaye ya dinga fareti daga kwarmin idona zuwa gefe da gefen fuskata. Motsin shigowar yaran ya sa na yi jarumtar gogewa tare da gyara kwanciyata, don ba na so su gano damuwar da nake ciki balle hakan ya saka su rashin walwala.
Kishiya akwai zafi. Amma idan an saka haƙuri da juriya komai zai zamo kamar ba komai ba.🥲
D.AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ASHIRIN DA TAKWAS.*
Da sanyin jiki na wayi safiya, domin kuwa ban yi wani baccin kirki ba a daren ranar. Hakan ya janyo mini ciwon jiki da ciwon kan da na ji ba na ra'ayin fita ranar. Kai-tsaye na tura wa MD saƙon ba na samun damar zuwa offis.
Bayan mun karya ni da yaran muka fara ƙoƙarin fitar da kujeru a tsakar gida, kafin mai adaidaita ya zo ɗaukar su.
Muna tsaka da fito da su Mukhtar ya fito daga É—akinsa yana waya.
"Ki kwantar da hankalinki, ba ni na ce zan ba ki ba? Zan ba ki... Yawwa! Ko ke fa! Ki jira ni anjima kaÉ—an zan aiko mi..."
Wani tuƙuƙin baƙinciki ya taso mini, nan take hawaye mai zafi ya cika mini ido. Na fakaici idon yaran na goge, sannan na bar tsakar gidan na koma ɗakina. Kwanciya ta kenan yaran suka shigo da gudu, suna sanar da ni ga Najib mai adaidaita ya zo ɗaukar mu, na ce su tafi kawai Allah ya tsare hanya.
Bayan fitar su na ji kuka mai ƙarfi ya suɓuce mini ba tare da na shirya wa zuwansa ba. Na jima ina kukan kafin na ji sassaucin nauyin da nake ji a cikin zuciyata. Na shiga tunane-tunanen matsayin aurena da kalar zaman da nake yi a gidan Mukhtar.
Ban san lokacin da bacci ya kwashe ni ba sai da na ji yana rafka mini sallama a saman kai. Firgigit na farka tare da zabura saboda ganin shi a saman kaina, da hanzari ya juya zai fice É—akin yana cewa,
"Umma ce ta aiko da kaya, ki tashi ki je ke yaran suke jira tun É—azu."
Na miƙe ƙasusuwan jikina suna ƙara na fito ɗakin jikina liƙis, taku nake yi babu kuzari na yi tsakar gidan. Inda na ga yaran tsaye cirko-cirko da sababbin kujerun da suka kawo a gabansu, waɗanda muka ajiye kuma har sun fitar da su waje ban sani ba.
Umurni na ba su a kan su shigo da kujerun, na nuna musu inda za su ajiye da yadda za su jera mini su. Yadda na faɗa haka suka yi, nan take wurin ya fito fes ma sha Allah gwanin burgewa. Musamman da suka maƙala mini sababbin labulan da suka zo da su masu matching da kalar kujerun.
Farinciki ya ziyarci zuciyata, a lokacin da suka tafi na zauna saman kujerun ina goge ruwan hawayena.
'Umma ta kasa fahimtar gundurar da na yi da rayuwar auren Mukhtar. Ta kasa gano inda matsalata ta fuskanta ba zama da shi ne damuwata ba. Yaushe zan fita daga ƙangin wannan aure na kama-karyar da nake yi?'
Shiru na yi daga zancen zucin saboda amsar da zuciyata ta ƙara kitsa mini wadda ta sa ƙirjina bugawa dam-dam!
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.