Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 53 of 86
Sajida ta isa wurin shi tana faÉ—in, "Don Allah Abban Haidar ka zo a yi hoton nan da kai."
Har ya yi gaba yana 'yar dariya mutane suka fara roƙonsa a kan ya zo a yi da shi, fuskarsa a washe ya zo wurinmu ya tsaya gefen Iman. Mai hoton ya ce ya dawo kusa da ni Ummu Salma a gefensa, Iman gefena Haidar ya tsaya ta gabansa.
Ma sha Allah kawai mutane suke ta faɗa saboda babu ƙarya mun ɗauki na kuti. Bayan an gama mana hoton in group aka ce ya tsaya a yi muna ni da shi, yana shan ƙamshi aka yi mana hoton yayin da na ƙawata fuskata da mayalwacin murmushi.
Ana gama É—aukar hoton ya yi ciki ya bar mu muna ci gaba da hotunan, ba tare da ya yi mini kallon tsanaki ba balle mu haÉ—a ido ya ga kwalliyata. Mintuna a tsakani ya fito ya fice gidan, jim kaÉ—an da fitar shi wata Yayarsa ta zo kira na.
"Mukhtar ne a ƙofar gida yake so ku gaisa da abokansa."
Mayafina na ɗora a saman kai duk da ɗaurin da aka yi mini mai tozo sama. Ina gaf da fita sabon tunani ya shiga kaina, saboda burin da nake da shi a kan na ɓata masa kamar yadda yake ƙoƙarin yi mini a bikin.
Mayafin na sauke a kafaÉ—a, na fara taku irin na isa na doshi inda abokan nasa suka yi dandazo. Fuskata a sake na fara gayar da su, waÉ—anda suka san ni suna tsokana ta da sunan uwargida sarautar mata.
"Gaskiya Mukhtar ka yi sa'ar mata, domin kuwa na kasa tantance ita ce uwargidan taka ko kuma amaryar ce?"
Murmushin yaƙe kawai yake yi yana kallona, fari da ido na yi wa mai maganar, duk da ban waye shi ba na ce,
"Ai duk macen da ta yi saurin zama jagwaf daga ita ne. Domin babu inda aka ce shi kaɗai ne da haƙƙin gyara ta koyaushe. Yana da kyau ita ma ta taimaki kanta da 'ya'yanta domin ta rufa wa kanta asiri da mijinta."
Kallona kawai Mukhtar yake yi, domin ya kasa É—auke idonsa daga kaina. ni ma idona cikin nasa nake jefa masa murmushin,
'Ya ka ji kafcen?'
"Gaskiya abokina ka yi sa'ar aure, domin kuwa ka auri macen da ta dace kuma wadda ta san kanta. Congratulations bros"
Abin da wani ya faɗa kenan yana bubbuga kafaɗarsa, bai ce ƙanzil ba ya bar wurin, yana ƙoƙarin tare wani mai mashin da zai wuce ta gabanmu.
Karantar yanayinsa da halin da ya shiga ya sa na yi musu sallama na juya, zuciyata cike taf da farincikin abin da na yi. Don na san shi ya gano inda zantukana suka nufa, waÉ—anda ba lalle ba ne su abokansa su fahimci inda na dosa, balle su hankalta da bugun gorar da na yi masa a fakaice cikin siyasa.
Har aka watse taron bikin ban daina jin farinciki a zuciyata ba, bayan magriba wasu daga cikin danginsa suka je É—auko amarya.
A lokacin da na ji dirar motocin 'yan kawo amarya, ƙirjina ya buga daram-dam-dum! Kafin zuciyata ta karɓa tana ta harbawa ɓal-ɓal sauri-sauri gudu-gudu. Ga uwar guɗar da ake jerawa wata bayan wata a lokacin da aka shigo gidan
"Ayyururui!!!!"
Na daburce na ji ina ma na samu ƙafar tserewa na ɓoye, domin kada na yi kukan da zan fallasa kaina a gaban mutane. Firdausi ta taso daga mazauninta ta zauna tare da yi mini raɗa a kunne.
"Ki natsu da kyau kada ki bari a gano ki plsss!"
Babu shiri wa'azinta ya shiga kaina na mazge, tare da miƙewa na tarbo amaryar. Jikina na saka ta na rungume tare da riƙo hannunta na zaunar da ita a kan kujera.
Zama na yi kusa da ita ina faÉ—in,
"Yau dai ga amarya a cikin gidanta. Allah ya ba ku zaman lafiya ke da angonki."
"Amin-amin!"
GabaÉ—aya mutanen da ke falon suka amsa cikin É—aga sauti. Wata daga cikin danginta ta matso kusa da mu tana faÉ—in,
"Ga Barira nan mun kawo muku, sannan mun damƙa ta hannunki amanar Allah!"
Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Daga ni har ita amanar junanmu muke, saboda zama ya haɗa mu dole ne mu yi haƙuri da juna. Don haka ni a wurina babu wata damuwa, ina mata fatan alheri, zaman lafiyar aurenta da zuri'a ɗayyiba."
"Allahu Akbar! Sannu 'yar aljanna!"
Maganar da na ji wata ta faɗa kenan a cikin matan da suka zagaye mu, ba tare da na ga fuskarta ba balle na gano wace ce. Cike da ƙwarin gwiwa na karɓi kuɗi a hannun Firdausi na ɗora a saman cinyar Barira.
"Ga nawa kuÉ—in sayen bakin, tun kafin ango ya riga ni jin muryar amarya."
"Na gode Aunty!"
Ita ce maganar da ta fito bakin Barira bayan ta damƙe kuɗinta a hannu, tamkar wadda aka ce za a yi wa ƙwace. Dariya aka shiga yi da ihun murna, Na riƙa ta har zuwa ɗakinta, bayan na saka ta yin basmala da shiga ɗakin da ƙafar dama.
Sai da na zaunar da ita kan gadonta, sannan na baro É—akin da ban gama tantance tsarinsa ba. Saboda ko da wasa ban ji ina sha'awar shiga ba bayan an gama jeren, haka ma duk zaryar da danginta suke yi kawo kaya da gyare-gyare ban bi ta kan É—akin ba, balle na ga kalar kayan gadonta da su Yaya Maimuna suke gulma.
Su Firdausi suka ja ni ɗakina, haƙuri suka shiga ba ni sosai irin wanda ya sa na ji kuka ya zo mini babu shiri. Sannan suka tafi kowa ya watse aka bar ni daga ni sai yarana da amarya Barira a cikin ɗakinta.
Ƙarfe goma da mintuna na ji Mukhtar yana rufe gida, sannan ya turo ƙofar ɗakina ya shigo kamar an jefo shi. Ledar da ke hannunsa ya ajiye a kan bed side, sannan ya zo daidai kaina yana faɗin,
"Yanzu ke abin da kika yi mini a gaban abokaina kin kyauta kike gani? To wallahi duk abin da kike taƙama da shi na fi ki."
"Ni ce shaida! Domin kuwa ko rashin adalcin da ka fara da shi; ya nuna mini zahirin wane ne kai a yanzu ko da ban san ka a baya ba."
Amsar da na ba shi kenan ina ƙoƙarin tashi daga kwanciyar da nake. Duk da a raina ba na so mu yi abin da zai raba mana hali, gudun amarya ta jiyo mu.
"Idan ma don ban ba ki kayan da aka ce ana bayarwa ba ne kike son tozarta ni; to ki yi duk abin da za ki iya. Amma wallahi ba zan ƙara wa mai ƙarfi ƙarfi ba, don kina da kuɗin albashinki, wanda kaɗan ne za a ƙara a kan wanda nake karɓa. Kuma ina da hidimar da ta fi zama dole fiye da saya miki kayan dannar ƙirjin."
A harzuƙe na ce da shi, "To da ba ka saya ba sai me!? Ai dai ba ka gan ni a wulaƙance ba ko?"
"Kanki ake ji! Ga kazar amarya nan ki sa albarka. Ni na shige! Kuma idan an ga ban fito da wuri ba kada a neme ni, don ba ɓata zan yi a cikin gidan ba."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.