Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 64 of 86

"E, kuma ba ta son mutumin."

"Kuma shi ne za a zo wurinki takakkiya miye naki a ciki?"

"Su dai suka sani."

"Hayaniya na ji shi ya sa na zo na gani lafiya? Ashe Mamarta ce take abin da ta saba. Ni na rasa laifin me kika yi wa wannan matar da ta saka ki gaba irin haka."

"Mijinki ake so a manna wa Sajida ba ki da labari."
Maganar Barira kenan da muka jiyo daga ni har Maman Taufiƙa saman kanmu.

"Mijina kuma?"

"E, shi! Kuma babu mai son ta ga auren nan ya ƙullu face wadda kuke zaune da ita yanzu. Don a gabana take saka Sajida ta manne wa mijinki, domin kawai ta ga ƙarshen kishinki."

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun!"

Ita ce kalmar da muka haɗa baki wurin faɗa ni da Maman Taufiƙ, tare da miƙewa tsaye dukanmu muna kallon Barira.

"To wasa ce nake yi! Ku yi haƙuri don Allah kada ku cinye ni da raina."

Barcy lamarinki sai ke 🤔😂

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*TALATIN DA BAKWAI.*

Ban san ya aka yi ba, sai hango Maman Taufiƙ na yi maƙare da wuyan Barira tana kakarin mutuwa. Cikin wani sabon tashin hankali na yi kansu ina ƙoƙarin ɓanɓare hannun Maman Taufiƙ, daga muguwar shaƙar da ta yi wa Barira. Wadda azaba ta sa ta gwalalo ido waje gulu-gulu tamkar idanun mota.
Ganin ba zan iya ni kaÉ—ai ba na fasa ihu saboda gabaÉ—aya sun fita hayyacinsu, tamkar wasu sababbin halitta. Mukhtar ya iso wurin a É—ari yana faÉ—in,

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"

Ya ja Barira na samu na ƙwace hannun Mama Taufiƙ, sai dai hakan bai yi mata ba ta koma ta cafko ta iya ƙarfinta. Mukhtar ya yi hanzarin ture ta gefe ta faɗi sannan ya rungume Barira yana ƙwala mata kira a haukace, saboda alamunsa ya nuna tsantsar kiɗima da ruɗewar da ya shiga. Ganin halin da Barira take ciki riƙe da wuyanta tana juye-juye tare da kakari a lokaci ɗaya.
Domin a kallo ɗaya za a kira shi da kakarin mutuwa saboda shure-shuren da take yi. Maman Taufiƙ kuma ta baje ƙasa tana gumza tamkar wata raƙuma. Bayan furzar da yawun da take yi yana baltsi a kan fuskarta.
Ruwa na ɗebo da gudu na dawo a firgice saboda na gama kai wa ƙololuwar ruɗewa. Sai dai tun kafin na iso na hango ta zabura tamkar wata zakanya ta yi kan Mukhtar da ke rungume da Barira.
Cakumo shi ta yi ta wurgar gefe tamkar a cikin shirin horror, sannan ta fisgo tsorayen Barira sai ga ta da su a hannu ta jefar ƙasa.
Kukan kura na yi tamkar wata ifirituwa na kai wa Maman Taufiƙ raruma ta baya. Saboda ƙoƙarin fisgo wasu tsorayen da take yi ta sauke su ƙasa kamar yadda ta yi wa na farkon. Kokawa muka shiga da ita tsakiyar falon tana so na sake ta ina damƙe ta iya ƙarfina. Tun muna faɗawa kujeru har muka faɗi ƙasa a tare muna mulmula tamkar wasu macizai.
Addu'a na dinga karanta mata a bakina cikin sauti tun tana fisge-fisgen har ta yi luf! Na ci gaba da karanta mata surorin tsari da kore shaiɗanun aljanu. Saboda na gamsu da cewa ba ta cikin hayyacinta balle hankalin kanta, shi ya sa take ƙoƙarin aikata aika-aikar da dukanmu sai mun yi da-na-sani.

Ganin ta lafa na hango Mukhtar ya nufi inda Barira da jini ya gama wanke mata jiki kaca-kaca. Ihu ya yi tare da kinkimarta tamkar 'yar tsana ya fice da gudu yana faman kiran sunanta.
Fitar su da ɗan lokaci na saki Maman Taufiƙ na miƙe ina kiran sunanta tare bubbuga jikinta. Firgigit ta miƙe idonta a zare sun yi jawur tana ƙare wa falon kallo, tamkar wadda aka bai wa aikin ƙididdige abin da ke cikin falon duka.

Hannunta na riƙa ta miƙe tana kakkaɓe kayan jikinta ta ce,
"Me ya kawo ni gidan nan?"
Fuskata ɗauke da mamaki na ce, "Kina nufin ba ki ma san kin zo gidan ba?" Na ƙare maganar tare da zuba mata idanuwa domin na tantance ita ce ko sarakan aljanunta masu neman ɗaukar rai.
"Wallahi Maman Haidar ban san na zo gidan nan ba! Iya abin da kawai zan ƙaras tuƙin tuwon da nake yi a kitchen.

"Cabɗijam! To mu je na raka ki gida kada ya ƙone a yi biyu babu"

Hijabinta na mayar mata sannan takalminta na ja nawa hijabin muka nufi gidanta. Abin mamaki tun a ƙofar gidan na fara jiyo ƙaurin ƙonewar shinkafa. Da sauri na sake ta na yi kitchen ɗinta da gudu na saukar da tukunyar tuwon. Wadda ta turnuƙe Kitchen ɗin da hayaƙi ko gabana da ƙyar na gani, har na samu sararin sauke tukunyar a kan gawayin da take girkin da shi.
Na fito ina tari tamkar na shiɗe, saboda ulcer ta ko kaɗan ba ta buƙatar hayaƙi. Dalilin da ya sa na daina aiki da komai sai gass, duk da a lokacin da na saye shi ba ƙaramar rigima muka yi da Mukhtar ba. Saboda ya buga kansa a ƙasa shi ba zai iya wahalar shi ba, na ce masa na ji na ɗauka ni zan ɗauki nauyin komai ko don lafiyata.

Gida na koma na rufe, sannan na dawo na kankare tuwon da fiye da rabinsa ya gama ƙonewa. A gurguje na canza tukunya na ɗora mata wani sabon tuwon, ganin garin semo a buhu ya sa na fara talga tuwon na rufe. Sannan na fito na nufi ƙofar gidan saboda sallamar da na ji Mukhtar yana bugawa.
Hankalina a tashe na isa ina tambayar shi Barira da halin da take ciki, harara ya kwaÉ—a mini tamkar idonsa su faÉ—o ya ce,
"Ba ni makulli!"

Na ciro daga aljihun riga ta na miƙa masa ya wuce fuu, duk da alhinin da nake ciki sai da na tuno lokacin da aka jefar da shi ƙasa ya yi zaman 'yan bori. Bayan ya fasa ƙara tare da faɗin,

"Wayyo Allahna uwata!!!!"

Komawa ciki na yi ina 'yar dariya har tuwon ya yi na kwashe mata, a ledodin da na gani an gama buÉ—ewa. Sannan na kashe gawayin na tafi falonta ina kiran sunanta, hango ta da na yi a kan kujera 3seater tana bacci sharkaf. Hakan ya sa na ji wani sanyin daÉ—i ya ratsa zuciyata.

Ficewa na yi gidan ina ƙoƙarin shigewa gida na hango motar Baban Taufiƙ ya doso. Na dawo baya jikina yana tsuma na isa inda ya yi parking motarsa yana ƙoƙarin fitowa.

"Don Allah! Wata alfarma na zo wurinka a kanta. Na san kana son Sajida, amma ka taimaki rayuwaka da yawa ka janye wannan maganar!"

Tsayuwarsa ya gyara sannan cikin murmushi ya ce da ni, "Allah fa bai haramta mini ba, don haka ban ga abin tashin hankali a cikin lamarin ba. Idan ma matsalar Aminiya ne ku bar komai a hannuna na san yadda zan tafiyar da ita har ta amince."

"Ba za ta amince ba! Don yanzu haka da ƙyar amaryar Mukhtar ta sha a hannunta. Saboda ta yi gangancin sanar da ita shi ne ta shaƙe ta har da cire mata tsoro uku."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.