Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 32 of 86
Ajiyar zuciya na sauke a lokacin da aka ajiye ni ƙofar gidan. Tunani fal zuciyata na shiga gidan, da sassarfa na faɗa falon saboda kukan Haidar da na ji yana tashi.
Ummu Salma da Iman suka yi kaina da gudu suna ihun murnar gani na. Mamakina da na hango Haidar ya ƙara shan jinin jikin shi, sai matsar ƙwalla yake yi tare da goge hawayen da ya jiƙa masa fuska.
Da sanyin jiki na nufo shi da nufin na ji wa taɓa shi, sai dai kafin na isa wurin shi ya yi hanzarin tashi da gudu ya yi ɗakinsu ya rufe. Baki a sake na bi ƙofar da kallo kafin na dawo da kallona a kan fuskar Ummu Salma, wadda ke wasa da yatsun hannunta tana so ta yi magana tana shayi.
"Me aka yi wa Haidar?"
Tambayar da na jefo mata kenan don na san Iman ba gwanar magana ba ce.
"Don Allah Mama kada ki dake shi don Abbanmu ma ya dake shi."
Gabana ya ƙire ya faɗi cikin sauri bakina yana rawa na ce, "To me ya yi aka sake shi?"
"Taba ya ɗauko ɗakin Abbanmu ya kunna ya sha, ni da Iman ba mu sani ba sai da muka jiyo ihun shi cikin toilet sannan muka je da gudu. A nan muka ga tabar a hannun shi yana ta tari kamar zai mutu. Na fara zuba masa ruwa a fuska ni da Iman muna ta kuka, na ce da ita ta kira Abbanmu kada ya mutu mu shiga uku. Ko da Abban ya zo na faɗa masa taba ya sha shi ne fa ya yi ta dukan shi, da ƙyar ya ƙyale shi saboda ganin muna ta kuka ni da Iman."
Zaman na yi babu shiri tare da furta kalmar, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun!" Saboda ita kaÉ—ai ce kalmar da zan iya furtawa a lokacin.
Ni ma dai jikina ya yi sanyi😰🚶ðŸ»â€â™€ï¸
D. AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*LAMBA ASHIRIN.*
Shiru na yi na ɗan lokaci dafe da kaina da ke ta sarawa, sannan na miƙe su Ummu Salma suka fara kuka tare da roƙo na don Allah kada na buge shi.
Ban bi ta kansu ba balle ta kan Haidar da ke kulle cikin ɗakinsu. Ɗakina na nufa yaraf na zauna bakin gado saboda jirin da ke kwasa ta, mintuna a tsakani na miƙe na ɗoro arwala. Sallah na gabatarwar tare da ɗaga hannuwana sama ina roƙon Allah shiriya zuwa ga 'ya'yana. Ruwan hawaye yana zarya a kan dandamalin fuskata cikin ƙanƙan da kai tare da tawassuli da haƙurin da nake yi a gidan Mukhtar.
Ummu Salma ta shigo ɗauke da kula ta ajiye gefena, tana ƙoƙarin ficewa cikin sanyin murya na ce da ita,
"Kira mini Haidar ku zo tare."
"To" Ta faɗa sannan ta fice jim kaɗan ta dawo riƙe da hannun Haidar yana tirjiya tana janyo shi, Iman ta yi hanzarin zuwa inda nake tana matsar hawaye ta ce,
"Don Allah Mama ki yafe masa Abbanmu ya dake shi sosai."
Kallo na bi fuskar shi tare da tsuke tawa fuskar na ce,
"Zo nan!"
Ya tako yana É—ari-É—ari tare da haÉ—a hannuwan shi wuri É—aya yana faÉ—in,
"Don Allah! Don Allah Mama wallahi ba zan sake ba."
Har ga Allah jikina ya yi sanyi da zancen shi, uwa-uba yanayinsu duka da ya koma kalar tausayi. Wuri na nuna masa da nufin ya zauna, zama ya yi a É—arare yana tsiyayar hawaye daga idanuwan shi da suka yi jawur saboda kuka.
"Kana so na mutu?"
Tambayar da na fara jefa masa kenan ina ƙoƙarin goge hawayen da ke ta ambaliya a cikin idona, kai ya shiga girgizawa tare da faɗin,
"Ba na so!"
"Kana so Allah ya ƙona ka?"
A nan ma ya girgiza kai, "To idan har kana so na ci gaba da zama tare da ku, to kada ka sake shan taba daga yau har ranar tashin duniya. Domin duk ranar da ka sake shan tabar nan, ina tabbatar maka da cewa a ranar zan mutu, kuma muddin ka sake sha har na mutu kai ma za ka mutu ka je lahira a saka ka wuta. Kana so Allah ya ƙone ka saboda shan taba?"
Girgiza kai ya shiga yi hawaye yana zarya kan fuskar shi har yana feso mini. Hannuna ya riƙe da hannunsa biyu yana faɗin,
"Wallahi na yi alƙawari ba zan sake sha ba. Idan kuma na sake ki ce Allah ya kashe ni Mama."
"Allah ya ba ka ikon dainawa. Kuma ya sa daga wannan shi kenan har abada. Idan kuma ka sake shi kenan da ni da kai duka za mu mutu a rana É—aya."
Rungume ni ya yi tare da fashewa da kuka yana faÉ—in, "Ba na so ki mutu don Allah kada ki mutu."
Daga haka na cire shi jikina saboda warin tabar da nake ji yana tashi a hannunwansa. Wanka na ce ya je ya yi kuma dukansu su yi shirin zuwa islamiya. Sannan na fito É—akin ba tare da na bi ta kan abincin da Ummu Salma ta kawo mini ba.
Ɗakin Mukhtar na nufa, na ga ƙofar a rufe alamun ya fita. Sannan na dawo na yi wanka zuciyata a cunkushe da zallar nadamar auren Mukhtar a raina. Cike da takaicin haihuwar 'ya'yana ga wanda bai cancanta ba.
'Ashe ba namiji kaÉ—ai ya dace ya nemar wa yaran shi uwa tagari ba har da mace.'
Zancen zucin da na yi kenan a zuciyata cike da tausayin matan da ke zumuɗin yin auren. Saboda da sun san tarin ƙalubalen da ke cikin auren, maimakon murna kuka za su yi.
Shigowar su Ummu Salma ya katse mini tunanin da na lula, saboda ko kayan da na fitar daga wardrobe ina riƙe da su ban saka ba. "Allah ya tsare na ce musu, tare da Addu'ar kariyar da nake yi musu koyaushe."
Har sun fita Haidar ya dawo ya durƙusa gabana tare da haɗa hannuwansa wuri ɗaya yana faɗin, "Ki yafe mini Mama. Na yi miki alƙawarin ba zan sake ba daga wannan."
"Na yafe maka Haidar, tashi ka je Allah ya yi muku albarka dukanku."
Ya fice yana yi mini bye-bye ina yi masa tare da murmushin jin daÉ—in farincikin Allah ya mallaka mini yarana, ba don iyawata ba kuma ba don na fi kowa ba.
"Alhmdulillah!"
Ita ce kalmar da na faɗa sannan na miƙe na saka kayana, abincin na janyo na cakula kaɗan na ture. Sannan na fito falo mintuna kaɗan na fara jin ƙarnin taba yana tashi.
Na miƙe na nufi ƙofar ɗakin inda hayaƙin da ke fitowa ta kusufar makullin ɗakin Mukhtar, haksn ya tabbatar mini da yana ciki. Tura ƙofar na yi babu shiri na ja baya ina toshe hanci, saboda gabaɗaya ɗakin ya turnuƙe babu abin da ke fitowa sai hayaƙin tabar.
Tari na fara yi ina kaɗe hayaƙin a fuskata har ya lafa, sannan na yi ƙarfin halin faɗin,
"Idan ka gama ina son magana da kai."
Da hanzari na koma falon na zauna ina sauke numfashi a wahale, don na kasa sabawa da warin tabar duk tsawon lokacin da muka ɗauka da shi. Bai fito ba tsawon lokaci sannan ya fito yana zuba ƙamshin turare, tare da haɗe fuska ya yi tsaye nesa da ni, fuskata babu yabo babu fallasa na ce da shi,
"Zama za ka yi, don maganar ba ta tsaye ba ce."
Ya zauna yana shan ƙamshi tare da faɗin, "Sauri nake yi akwai inda zan je. Idan maganar mai tsayi ce ki bari na dawo kawai."
"Yanzu ya dace mu yi maganar, don haka yana da kyau ka san illar da ke cikin shan tabar da kake yanzu. Domin idan can baya ka yi babu yara, yanzu da suka fara mallakar hankalin kansu yana da kyau a ce ka daina. Saboda ci gaba da sha zai iya gurɓata mini tarbiyar da nake ƙoƙarin ɗora su a..."
"Me kike nufi? Kina zaton ni na koya masa shan tabar? Ko kuma ni na ce ya zo ya É—auka ya sha!?"
Tambayar da ya jefo mini kenan a fusace, wanda alamu ya tabbatar ba za mu kwashe ta daɗi ni da shi ba. Saboda ba ƙaramar danna nake yi wa zuciyata ba, dalilin da ya sa ban zo da zafi ba saboda ina so ya fahimci abin da nake son nuna masa.
"Ban ce ka ba shi ba, amma tabbas kai ka koya masa. Saboda kai ya ga kana sha shi ya sa shi ma ya fara gwadawa, domin ƙaramar ƙwaƙwalwarsa ba ta hango masa illar abin, saboda ganin kana sha tunaninsa zai ba shi babu matsala a ciki. Don da akwai illa a ciki matsayinka na babba ba za ka dinga sha ba."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.