Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 42 of 86

"Ina take baƙar 'yar iska munafuka, wadda ba ta san ciwon kanta ba, wallahi muddin ba ki daina zuwa gidan nan ba, sai an sabauta miki rayuwa a kan baƙin kwaɗayi irin naku ke da uwarki."

_Gabaɗaya muka fito tsakar gidan, Kakar ta ci gaba da zagin ta tana ƙoƙarin kai mata duka da wata ƙatuwar sandar da ke hannunta. Zagayen gidan suka fara yi kafin ta yi nasarar kora ta tana ci gaba da bala'i, ta inda take shiga ba tan take fita ba har ta fice ba ta daina masifa ba._
_Shiru kawai na yi ina tunanin abin da maganganunta suke nufi, saboda iya sanina ko ƙannen Mukhtar maza ba su zuwa gidan su zauna. Balle na ce maza suke zama gidan shi ya sa Kakarta take gudun a lalace ta._
_Duk da korar da Kakar take yi mata bai hana ta zuwa jefi-jefi muna gaisawa ba, amma ni ma da kaina na zaunar da ita na nuna mata cewa; Ta daina zuwa kamar yadda Kakarta ta gindaya mata doka, ni kuma duk abin da Allah ya hore mini ko ba ta zo ba zan aika mata. Saboda har raina ina jin daɗin yadda take ƙaunar Ummu Salma, amma tun da abin ya zo da haka dole na yi ƙoƙarin ɗora ta a kan abin da Kakarta take so. Da haka ta daina zuwa sai ranar da kakar ba ta nan ta leƙo mu gaisa tsaitsaye, sannan ta miƙa wa Ummu Salma abin da ta zo mata da shi ta fice._

_Wata safiya bayan Mukhtar ya fita Mamarta ta zo gidan, mun gaisa a mutumce ta ce da ni wurina ta zo. Zama na gyara ina murmushi ta ce da ni,_
"Na ji duk abin da Inna Huse ta yi, kuma Jamila ta sanar da ni yadda kuka yi da ita. Ubangiji ya saka miki da alheri Allah ya bar zumunci."

_Cike da jin daÉ—i nake ta faÉ—in amin amin. Sannan ta yi shiru na É—an lokacin kafin ta sake cewa,_
"Don Allah akwai wani taimakon da nake so ki yi mana Maman Salma."
"Kamar wane fa?"
"Yawwa! Ai kin san Nura mai son Jamila ko? To zancen auren ne ya ƙi fitowa da gaske sai ja baya yake yi. Ga mutane suna son shigowa amma shi ya ƙi gaba ya ƙi yin baya, don haka nake so ki kira mini shi don Allah ki yi masa magana a kan matsalar. Saboda na gaji da ganin ta a gabana, idan bai tashi ba sai a tsayar da wanda ya shirya, tun da abin na shi ya zama rainin hankali da shiririta."

_Ban yi tunanin komai ba na karɓi lambarsa gare ta na danna masa kira. Babu wani jinkiri ya ɗauka tare da yin sallama. Na amsa masa sannan na sanar da shi wace ce ni, tare da maƙasudin da ya sa na kira shi a fakaice ba tare da na nuna masa Mamar Jamila ce ta saka ni ba. Buɗar bakin shi ya ce da ni,_

"E kam! Idan ma ban shirya ba ai sai ki yi mata auren gida a matsayinki na uwar ɗakinta. Don haka idan kun matsu ina jiran goron ɗaurin auren domin ya ƙarasa ɓarnar da ya aikata."

_Sororo na yi da waya a hannu, domin tun da ya gama faɗin maganar cikin ɗaga murya ya katse kiran, da sanyin jiki na sauke wayar daga kunnena. Sannan na yi mata bayanin abin da ya ce ba tare da na gano inda zancen shi ya dosa ba. Jikinta yana rawa ta miƙe tana yi mini godiya ta fice gidan, yanayinta da maganganun Nuran suka ƙara cukurkuɗe mini kwanya._

'Shin me yake nufi da jefa mini wannan magana? Kuma me ya sa Mamar Jamila ta shiga tashin hankalin da na gani kwance a kan fuskarta.'

_Tambayoyin da na yi wa kaina kenan, waÉ—anda ban san amsar su ba sai daga baya, a lokacin da na ji abin da ya hasko mini ma'anarsu da inda suka dosa._

Ni dai kam ban gane komai ba😼 wanda ya sani ya sanar da ni plss🙁

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*ASHIRIN DA SHIDA.*

"Hmmmmm! Tabbas tarihinki shi ne makarantar aure, mai kwasa-kwasai ɗauke da tarin aji-aji, waɗanda ke ƙumshe da darussa iri-iri wani bayan wani. Dole ki kalli matsalata kamar an ɗebi ruwan rijiya da sirinji. Haƙiƙa kin yi gwagwarmayar aure, duk da har yanzu ban gama shanye romon labarin ba. Amma ni kam ko iya haka ma ba zan yi kwatar jarumtarki ba. Saboda zuciyata ba ta da ƙarfin shanye waɗannan tarin matsalolin, masu ƙoƙarin yi wa mutum kisan mummuƙe ba tare da an san mafari ba."

Maganganun Amina kenan a lokacin da na tsayar da labarin, murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Za ki iya! Domin ni kaina a yadda nake da masifar zuciya a baya, ban taɓa tunanin zan iya shanye tarin damuwowin ba. Sai ga shi Allah ya ɗora mini kuma ya ba ni ikon ɗauke komai a saman kaina, ba tare da sun yi nauyin da za su karya mini wuya ba."
"Danƙari! Waton dai ƙalubalen rayuwar aure hawa-hawa ne kuma kala-kala. Amma duk da haka taki ta zamo shakundum! Domin ta haɗe ɓangarora da yawa."
Shiru na yi kawai ina mata dariya, saboda yanayin da take kallo na tana jinjina kai tare da faÉ—in,
"Hu'ummm! Lalle! CabÉ—ijam!"
Sai da ta É—auki mintuna a haka sannan ta cire tagumin da ta yi tare da jefo mini wata tambaya.
"Yanzu kina nufin duk wannan badaƙalar babu wanda ya sani a cikin familynki a lokacin?"
Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, murmushi a kan fuskata na ce da ita, "Babu wanda ya sani daga dangin Ummata har dangin Babana da ke Birnin Kebbi. Saboda na riƙe sirrin aurena da kyau, kuma na ɗauke shi abu mai muhimmancin da za mu rayu mu kaɗai a cikinsa ba tare da kowa ba. Ba a fara sanin tsakanina da shi ba har sai da ya yi mini wata gagarumar cin amanar da na kasa shanye baƙincikinta a zuciyata, na fara yi masa bore. Kuma ko fashewar ƙwan ma ba daga hannuna ya fito ba, shi da kansa ya yi kururuwa ya luma wa kansa wuƙar da ta yi barazanar ɓurma masa baya."

Shiru na yi bayan na tsahirta da maganar ina duba agogon da ke tsintsiyar hannuna. Na fara haÉ—a kayan da ke saman teburina ina faÉ—in,
"Babu time, da na sanar da ke abin da ya yi mini a lokacin, wanda ya yi sanadin yanke ƙaƙƙarfar alaƙar da ke tsakanina da ƙawata Hafsa. Domin har yau da nake yi miki wannan magana babu jituwar kirki a tsakaninmu. Saɓanin baya da nake yi mata kallon 'yar'uwa kuma abokiyar haihuwa, duk da maƙotaka ce ta haɗa mu tsakanin gidan Kawu Sale da gidansu. Sannan Mamarta ƙawar Ummata ce, haka ma Babanta abokin Kawu Sale ne na ƙud-da-ƙud."
"Tabbas! Akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninku."
Zancen Amina kenan a lokacin da muke ƙoƙarin fitowa daga offis ɗin.
"A hakan kuma ta rufe idon sani ita da Mukhtar, suka so jefa ni rami su binne da rai ba tare da sun jira na mutu ba."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.