Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 11 of 86

Ina wasa da yatsun hannuna na ce "Alhmdulillah!" Bai sake cewa komai ba ya fara tattara files ɗin wuri ɗaya sannan ya miƙo mini, kan shi a duƙe ya ce "Akwai mutanen da suke jiran ki, file ɗinsu ne duk wanda ya bayar da kuɗin sai ki cike masa idan kin gama ki dawo mini da su".
Karɓa kawai na yi ina ƙoƙarin juyawa, sai dai kafin na yi wani dogon motsi na tsinkayo muryar shi cikin kunnuwana a sarƙe yana cewa, "Ki daina amfani da turare mai ƙarfi idan za ki zo offis".
Daga haka bai sake cewa komai ba ya janyo wasu takardun yana rubutu, nan take ƙirjina ya buga jikina ya fara rawa cikin saurin murya na ce "In Sha Allah zan kiyaye".
Ina gama faÉ—ar hakan na fice cikin sauri, saboda har cikin raina na ji kunyar abin kuma na ji daÉ—in kulawar da ya yi a kan hakan. Duk da bai yaba turaren a zahiri ba, amma Hausawa sun ce,

'Tankawa yabawa ne'.

Cike da tsantsar farinciki na fara aikin da ya saka ni, domin har wani ƙarfi na samu da kuzarin yin aikin cikin nishaɗi. Kuɗin haraji na shiga karɓa ina haɗa kansu bayan na cike takardun shaidar an biya.
Ban samu kaina ba har sha biyun rana, sannan na tattara kuÉ—in da files É—in na nufi ofishin shi. Sai dai ko da na shiga da sallamata a baki dole na yi turus, saboda ban hango shi a kan kujerar shi ba kamar yadda na tsammata. Nufar teburin shi na yi da nufin ajiye masa takardun da kuÉ—in na juya, sai ga muryar shi na ji tana tashi a cikin toilet É—in da ke Offishin kamar yana faÉ—a.
"Wai ke Fatima har yaushe za ki yi hankali ne? Yanzu abincin da zan ci ma kin kasa tashi ki girka sannan ki zo da zancen fita? To babu inda za ki je, kuma na dawo na tarad da ba kya gidan sai kin gane kin yi wauta, mitsssss! Aikin banza kawai. Mace har ma mace amma ta kasa sanin yadda ake tattalin miji. Sai baƙin yawon masifa daga wannan biki sai wancan..."

Da sauri na ajiye masa takardun da kuɗin na nufi hanyar ficewa offis ɗin, saboda na ji takun shi alamun zai fitowa kuma ba na so ya same ni. Har na riƙe handle ɗin ƙofar da nufin ficewa a ƙoƙarina na son arcewa kafin ya fito. Cikin sauri na juyo jikina yana rawa na yi jarumtar ɓoye tsoro kada ya bayyane a kan fuskata, saboda ba na so ya zargi na yi masa laɓe domin na ji wani abu daga cikin sirrin shi.
A take ya musa tunanina ta hanyar faɗar, "Karɓi waɗannan ki haɗa list ɗin wuri ɗaya. Amma ki bar su a hannunki har zuwa gobe, don na san ba lalle ne ki kammala su a yau ba".

Karɓar takardun na yi na fice, zuciyata a cunkushe na nufi offis ɗina. Saboda muryar da na ji ya yi amfani da ita wurin yi mini maganar ƙumshe take da damuwa. Haka kawai na ji ina jin haushin matar shi a raina, domin ganin Allah ya ba ta dama amma tana wasa da ita cikin izgilanci.
Shiga ta offis ke da wuya na hango Amina zaune a kan kujerar baƙi ta yi tagumi. Murmushi na yi babu shiri maimakon na ji tausayin halin da na gan ta, kuma na san tana ciki. Amma sai na ji dariya ta zo mini, saboda kallon da nake yi mata har yanzu ba ta san komai a cikin ƙalubalen aure ba, idan na auna shekarun aurenta da ta sanar da ni, da shekarun aurena da kuma matsalolin da nake ciki. Waɗanda nake hangen ko rabin kwatar ba ta kai ba balle ta kamo ƙafata.

Zama na yi tare da faÉ—in "Wash Allah!" Ta É—ago da kanta tana kallo na hawaye kwance a kan fuskarta. Mamaki ya so kama ni saboda tunanin me ya saka ta kuka a lokacin...
"Ina cikin tashin hankali Zaituna. Wallahi zuciyata gaf take da bugawa matuƙar Mama ba ta canza tsarin da ta yi ba.."
Zancen da ta tarye ni da shi kenan cikin rawar murya hawaye suna kwarara a kan fuskarta. Kafin ni ma na tari hanzarinta da cewa "Haba Amina! Har zuwa yaushe ne za ki saba wa zuciyarki shanye damuwa a kan halin Mama...?"
"Wannan karon daban yake da sauran abubuwan da take yi mini. Ta ya za a ce ta ɗauki kwanana ta bai wa kishiyata? Na rantse da Allah ba zan iya jurar ganin wannan kayan baƙincikin ba. Na fi so na je gidanmu da dai a ce na zuba ido Sanusi ya kwana ɗakin Sadiya".

Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi, sannan na kira sunanta cikin sanyin murya na ce "Amina! Idan na tambaye ki za ki ba ni amsa?"
"Me zai hana idan na sani?". Ta ba ni amsa a gatsali kuma ta da dawo mini da tambayar kaina.

"Don me Mama ta nemi yi miki haka.."
"Saboda ta ƙuntata rayuwata ta ɓata mini rai. Idan ma mutuwa zan yi na je na yi ita babu ruwanta".
Ta ƙare maganar cikin kuka wanda ya ƙara tona asirin ƙunar da zuciyarta take yi. Gajeren murmushi na yi sannan na ce,
"Kin san da hakan kuma kike ta wahalar da kanki a banza? A tunanina tun da har kin gano da gayya ta yi don ta ɓata miki rai. To ya dace ke ma ki ci maganin abin ki nuna mata hakan bai dame ki ba..."

"Ta ya zan iya jure wannan cin kashin Zaituna? A gaban idona ya kwana ɗakin Sadiya kuma a ranar kwanana a ce ba zan damu ba? Wace irin juriya ce zan yi a kan dokarta? Bayan ita ta saka ƙafa ta yi fatali da faɗar Allah Manzonsa, ta halasta haram ta haramta halas. Sai dai ana so na yi juriyar zuwan mala'ikan ɗaukar rai, domin ya zo ya karɓi raina cikin gaggawa na huta da wannan rayuwar baƙincikin ba. To ni wallahi ba zan iya ganin wannan kayan takaicin ba gidanmu zan je..."

Maganar da katse ni da ita kenan cikin matsanancin fushi na zahiri da ya tona asirin zaman shi a kan fuskarta. Da kai wa ƙololuwar ɓacin ran da ya fito har a cikin lafuzzan bakinta. A fusace ta miƙe ta ja jakarta da nufin ficewa, sanin idan ta fita a irin wannan halin da take ciki komai za ta iya aikatawa. Na yi hanzarin miƙewa na sha gabanta sannan na rufe offis ɗin da key na zare. Ƙasa ta durƙushe tana gunjin kuka mara sauti, na yi saurin isa inda take cikin tausayawa na fara rarrashinta.
Ganin da gaske take ba za ta iya juriya a kan shanye damuwarta ba. Na miƙe cikin tsananin ɓacin rai tare da rugume hannuwana a ƙirji, cikin wata kausasshiyar murya na ce "Da a ce zan iya, da na sanar da ke labarina. Wanda nake da tabbacin ya linka naki baƙinciki sau goma, wataƙila ki gano ba ke kaɗai ce igiyar aure take wahalarwa ba. Domin ina da tabbacin taki matsala tamkar shafin mai take idan kika ji tarihina".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.