Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 81 of 86
"Amin-amin."
Ko da muka isa ƙofar gidan ana shigar da kayan da aka fara kawowa. Ɗaki sukutum aka ware wa kayana, wanda daman can tarkace ne a ciki. Wasu kuma aka saka ƙarƙashin gadon Umma da na Inna Kulun. Wanɗanda zan yi amfani da su kuma na ajiye su kusa.
"Haidar sai tsalle yake yi cike da murnar jin mun dawo gidan gabaÉ—aya."
Ummu Salma ce kawai na ga damuwa a kan fuskarta, na yi kamar ban gano ta ba. Har sai da ta gaji da ƙuncinta ta same ni a kan sallaya, bayan na gama sallar Isha ina jan carbi ta zauna gefena, cikin sanyin murya ta ce,
"Wai yanzu shi kenan mun bar gidan Abbanmu?"
Wani kallo na yi mata sannan na ce, "Idan kuma kina son zama gidan ki koma can kawai! Amma ni dai na gama zama cikinsa da yardar Allah!"
"Ni ba na so mu bar gidan ne kawai! Amma abin da Abbanmu yake kwata-kwata ba na jin daÉ—insa. Shi kenan da gidanmu za mu bar wa wata shi ita kaÉ—ai ta zauna?"
"Ok! Ki ce damuwarki duka tana kan amaryarsa! Kuma tun da shi ya ji ya gani ke miye naki a ciki?"
"Kawai dai haushi nake ji wallahi! A ce saboda ita mun bar gidan Abbanmu!"
"Ba saboda ita muka bar gidan ba! Don ba yau ya fara yi mana cin kashi a cikin gidan ba! Sai dai idan kina so ki É—ora mata laifin da ba nata ba, don kawai kina so ki wanke mahaifinki"
Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, na ci gaba da jan carbina ban sake bi ta kanta ba. Saboda na daÉ—e da fahimtar ba ta so a faÉ—i laifin Mukhtar, da an fara zancensa komai take walwala sai fuskarta ta sauya.
Nan take na ji raina ya ɓaci, saboda tunanin da zuciyata ta ɗarsa mini, a kan ta fi son mahaifinta a kaina. Kira na ƙwala mata cikin sauri bayan ta fita ɗakin, ta dawo ta tsugunna gabana, yanayin fuskata da ta gani ta sha jinin jikinta. A fusace na da ita,
"Tattara kayanki gobe idan Allah ya kai mu ki koma gidanku!"
"Don Allah ki yi haƙuri! Wallahi ba da wata manufa na yi maganar ba, kawai dai ba na so ki bar gidan ne saboda wata banza!"
Ta ƙare maganar bayan ta fashe da kuka, cikin ɗaga murya na ce da ita,
"Sai fa kin koma gidan ubanki, tun da na gano kin fi son shi da ni."
Umma ta shigo É—akin tana faÉ—in,
"Babu inda za ta je matuƙar ina cikin gidan nan! Ubanta kuma dole ta so shi komai mugun halinsa tana son kayanta a haka. Don babu wanda ya fi mata shi kaf faɗin duniya, saboda naka naka ne komai muninsa. Ke za ki iya canza miji amma ita ba za ta iya canza uba ba! Idan kuma kika matsa ke ma zan ce ki koma Birnin Kebbi don nan ba gidan ubanki ba ne."
"Yanzu Umma a kanta za ki yi mini gorin gida?"
"ke a tunaninki kin fi ta matsayi a wurina ne?"
"Ai ni kika haifa ba ita ba!"
"Abin cikin ƙwai ya fi ƙwan daɗi. Don haka daga yau kada na sake jin kina yi mata faɗa don ta nuna damuwa a kan mahaifinta. Saboda ko mu ba shi muke ƙi ba halinsa ne ba ma so, amma tun da zuri'a ta haɗa dole ne mu yi haƙuri da duk abin da za mu gani."
Haka Umma ta dingà yi mini faɗa cikin kwantar da murya, har ta wanke mini haushin da Ummu Salma ta cusa mini. Saboda kishin ganin ta fi son gidan Mukhtar da gidan Kawu Sale. Haƙuri ta dingà ba ni cikin kuka bayan Umma ta fita, tana roƙon na yi haƙuri na yafe mata.
Fuskata a haÉ—e na ce da ita, muddin ta sake nuna ba ta son zaman gidan sai ta koma gidan Mukhtar. Kuma daga lokacin da ta koma babu ruwana da ita, kada ta sake zuwa gidan ta bar shi kenan.
Na yi hakan ne saboda tsoron wauta ta sa ta koma gidan ban sani ba. Gudun ta janyo mini gorinsa, ko kuma sabon tashin hankalin da zan shiga sanadin komawar ta hannunsa.
"Gobe dai za mu koma kotun, duk da ya yi sakin yana da kyau mu koma kamar yadda aka umuce mu."
Zancen Umma kenan a lokacin da take ƙoƙarin zama kan gadonta bayan ta fito daga wanka. Ƙirjina na ji ya buga dam-dam! Ina murmushin yaƙe na ce,
"Allah ya kai mu! Amma fa Umma rubutun sakin nan; kamar ba Mukhtar ne ya rubuta shi ba!"
"Saboda me kika ce hakan?" Tambayar da ta jefo mini kenan idonta a kaina ko ƙyaftawa babu, fuskarta a haɗe.
"Rubutun na gani kamar ba nasa ba!"
"To ko ba shi ya rubuta ba kin saku kenan! Babu wanda zai sake mayar da ke gidansa. Idan kuma ke ce ba ki gama fige kazar wa kanki kazar wahalar da ya yanka miki ba; ƙofa a buɗe take kin san hanya kina iya komawa!"
"Innalillahi Umma! Wallahi ba nufina kenan ba! Rubutun ne kawai na gani kamar ba nasa ba!"
"Ummmh!" Bayan hakan ƙanzil ba ta ce da ni ba, illa shirin kwanciya da ta yi ta kwanta tana tofe ɗakin da addu'o'i. Shiru kawai na yi ina nazarin halin Umma, wani lokaci idan ta yi wani abu kamar tana jiran mutum, da ya yi magana ta ga laifinsa.
Haka na kwana ina ta juya abubuwa da yawa a cikin zuciyata har bacci ya É—auke ni ban tantance ba.
****
Tun da safe na ga shigowar alert a wayata, ganin salary'na ya faranta mini rai sosai. Na tashi da kuzari na share gidan tas sannan na gyara É—akin Umma ko'ina tsaf-tsaf!
A gurguje na shirya muka fito ni da yaran bayan Najib ya ajiye su; na yi masa transfer'r kuÉ—in jingar da muka yi da shi duk wata, har da É—orin wasu canjin don ya ji daÉ—in É—awainiyar da yake yi da mu .
Ya ajiye ni yana ta godiya da nufin sha biyu na rana zai dawo ya ɗauke ni, kasancewar ranar jumu'a ce da wuri muke tashi. Fuskata babu yabo babu fallasa na gaisa da mutane, sannan na karɓi makulli a hannun masinjanmu na buɗe na shiga.
Ko zama ban yi ba Inna mai shara ta shigo na fito ofishin bayan mun gaisa a mutunce. Ina zaune saman dogon bencin ƙarfe da ke bakin ofishin saboda baƙi masu zuwa. Kaina duƙe ina latsa waya na ji ƙamshin turaren MD cikin hancina, cikin sauri na ɗago kaina muka yi four eyes da shi ya fito daga ofis ɗinsa.
Murmushin yaƙe na yi masa saboda ƙirjina da ke ta bugawa sanadin ganin shi, ban tashi daga zaunen ba har ya iso inda nake yana shan ƙamshi ya ce,
"Kwanan nan ki gane fashin zuwa aiki. Yana da kyau ki gyara saboda akwai ayukanki sosai da nake bai wa wasu suna yi. Ba na so mutane su hankalta a fara surutun ba ki san aikinki ba, bayan na gama bugun ƙirji a kan jajircewar da kike yi tuƙuru a cikin aikin naki."
Shiru na yi kawai, saboda tunanin da nake yi ai ya san rabin matsalolin da nake ciki. Kuma idan zai yi mini adalci ba zai ga laifina don na yi fashin zuwa aikin ba, saboda ina ƙoƙarin ba da abin da ake so, kafin zuwan matsalolin da suka taushe kuzarina.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.