Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 39 of 86
ðŸ¤ðŸ˜‚
D. AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ASHIRIN DA HUÆŠU.*
_Miƙewa ya yi ya shige toilet, a gurguje ya yi wanka ya shirya. Ina nan inda ya bar ni kwance ko motsin kirki na kasa yi, saboda tsabar takaici da baƙincikin da ya turnuƙe mini zuciya. Wurina ya zo yana faman murmushi ya sauke mini kiss a goshi, sannan ya nufi hanyar fita yana faɗin,_
"Ni zan tafi Makaranta, zan aiko da cefane."
_Murmushin yaƙe na yi masa ya fice yana yi wa Ummu Salma bye-bye, wadda ke ta wutsil-wutsil da ƙafafuwa tana tsotson hannu. Shiru na yi ina tunanin abin a raina, a ƙarshe na miƙe babu kuzari na tsarkake jikina ina jera tsakin haushin wanka ba tare da na mori komai ba._
****
_Haka rayuwa ta ci gaba tafiya kullum abin yana damuna a zuciya, ga shi ina jin kunyar sanar da shi meke damuna balle na yi masa bayanin abin da yake yi mini ba na jin daɗin shi. Saboda kunya da kuma nauyin ta yadda zan fito masa da abin da ke zuciyata, amma a raina kullum muka haɗa shimfiɗa sai na ji kamar na kuwata don haushi da takaici. Saboda ko kaɗan bai damu da nemar mini gamsuwa ba, da ya tsiyayar da ruwansa cikin minti biyu, uku zuwa biyar ya gama. Kuma babu wata wasar kirki da yake yi mini balle na ɗan rage zafin abin da ke damuna, ga shi da yawan buƙatuwa a lokacin kai-da-kai yake nema na kuma da buƙatarsa ta biya shi kenan._
_Haka ma dangane da kayan ɗakina babu wani tarnaƙin da ya fuskanta, saboda na bi na toshe duk wata ƙofar da za a ganin laifin Mukhtar. Domin da labarin canjin kayana ya je kunnen Umma, ta kira ni tana faɗan me ya sa aka canza mini kayan ɗaki ba tare da na sanar da ita ba. Na ce da ita ta yi haƙuri saboda ba na so ta yi mini faɗa shi ya sa ban sanar da ita ba, maganata ba ƙaramin ɓata wa Umma rai ta yi ba. Saboda faɗan da na ce ina gudu ta yi mini shi ta balbale ni da shi tamkar ta kamo ni cikin wayar ta yi ta jigba. Ban da haƙurin da nake jera mata babu abin da nake yi a lokacin, saboda jikina ya yi sanyi musamman da ta nuna don ba ta isa da ni ba ne shi ya sa ban yi sanar da ita ba._
_Ranar da ta zo ta ganar wa idanuwanta kayan, da ɓacin rai ta fice gidan tare da yi mini kashedi a kan; Duk lalurar da ta taso mini a gaba kada na neme ta. Saboda na sanar da ita wata lalura ce ta sa na sayar da kayan dole ba don na so b, ta tambaye ni to me na yi da kuɗin. Na fara kame-kame haushi ya sa ta kwaɗa mini mari tare da nuna ni da hannu ta ce,_
"Daga yau ki zamo uwar kanki da uban kanki, domin na zare hannuna a cikin duk wata buƙatar da za ta taso miki a gaba. Tun da har kina iya sayar da kayanki ina cikin gari ba tare da kin sanar da ni ba. Ke ko ba na garin nan idan kina mini kallon daraja ba za ki rasa ɗaga waya ki kira ni ba. Don haka yanzu na yarda kin ishe kanki, ki je ki yi duk abin da kike so babu hannuna babu ƙafata, balle abin da zai fito daga aljihuna."
_Na yi kuka sosai ranar, saboda fushin da ta yi da ni, ya fi komai tsaya mini a zuciya. Amma duk da hakan bai sa na ji haushin Mukhtar dangane da abin da ya yi mini ba, saboda na gamsu da abin da ya sanar da ni don a lokacin ma har ya fara zuwa makarantar. Kuma na sa a raina idan ya zamo wani abu ta sanadin karatun ita ma za ta ji daÉ—i, a lokacin zan sanar da ita yadda kayan suka yi na san za ta ji daÉ—i, kuma za ta yaba mini a kan rufin asirin da mijina ya samu ta sanadina._
_Akwai wata matashiyar budurwa mai suna Jamila, wadda ke cikin unguwar kuma muke maƙotaka da gidansu. Tana shigowa sosai gidan saboda ƙaunar Ummu Salma da take yi, kullum tana hannunta na yi ta aikina tana yi mata wasa ko ta goya ta. Wani lokaci kuma har aikin gidan tana taya ni don ba ta da ƙiuya ko kaɗan, hakan ya sa na saki jikina da ita sosai tamkar ƙanwata uwa ɗaya uba ɗaya. Ba na baƙincikin ba ta komai daga na ci har wanda za ta je da shi gida bayan na amfanin rayuwa._
_Matsalar da na fara fuskanta dangane da zaman da take yi da ni; Yawan damuwa da lamurranta da Mukhtar yake yi, ita ma idan ya zo gidan idanuwanta a kan shi ko ƙyaftawa ba ta yi. Sai ta ga ina haɗe rai sannan za ta shiga taitayinta._
_Ba na manta watarana yana tsaka da cin shinkafa da wake, ya shiga zuzuta yajin yana faÉ—in,_
"A gaskiya wannan yajin ya yi mini daÉ—i, ke kika daka shi kuwa?"
"Jamila ce ta daka. Kuma yadda nake dakan yajin kullum haka na sa ta yi mini."
"To gaskiya ta samo shi da kyau."
_Ban sake cewa da shi komai ba, duk da ban ji daÉ—in yabon da ya yi ba. Amma ban kawo komai a raina ba, sai da na nutsa nazari sannan na tuna ai ya shigo ya taras da ita tana dakan yajin, to kuma me ya sa ya tambaye ni bayan ya san ita ce ta daka. Haka kawai na tsinci kaina da ce masa,_
"Yanzu shi dakan yaji har wani abu ne mai girman da za a yi ta zuzutawa haka?"
"Allah ya ba ki haƙuri! Daɗin shi da na ji ne shi ya sa na yaba."
"To ba na son yabon tun da ba a yi maka dole sai ka yi ba, idan kuma ita kake so ka jinjina ma to ka bari idan ta zo gidan ka yi mata godiya. Ko kuma ka same ta gidansu idan abin ya dame ka."
"Can kika nufa kuma? To ni kin ga fita ta Allah ya huci zuciyarki!"
_Ya fice ya bar ni ina aika wa robar yajin harara tamkar shi ne nake kallo. Tun daga lokacin na hana ta taya ni duk wani aikin da ya shafi girki ko abin da za a ci. Sai dai ta kula mini da Ummu Salma ko shara da wanke-wanke, amma na katange ta da yin abin da Mukhtar zai yaba saboda masifar kishin shi da nake yi. Wanda in da ina da iko a lokacin, kallon wata ma ba zai yi ba balle ya hango kyawunta, don ko waya na ji yana yi cikin siririyar murya sai na ji haushi da kishi ya kama ni, kuma sai na zargi da wata yake yi. Wani lokaci ma har kiran waɗanda suka yi wayar yake yi domin na ji gaskiya a bakinsu, musamman idan ya yi ta rantsuwar ba da wata yake ba na ƙi yarda._
_Akwai watarana da na ji yana waya cikin toilet yana kashe murya, na je jikin toilet ɗin na lafe ina sauraron hirar da yake yi da wata. Raina a ɓace na dinga dukan ƙofar ina faɗin sai na kashe ko wace ce yake waya da ita cikin ɗakina. Hankalin shi a tashe ya fito yana ta rantsuwar babu macen da yake waya da ita. Idan kuma ban yarda ba sai ya kira mini wanda suke wayar na ji da kunnena. Ban ce da shi komai ba sai hucin da nake yi riƙe da ƙugu ina aika masa harara, ina sauraron ringing ɗin da wayar take yi saboda ya saka ta hands free domin na ji komai._
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.