Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 21 of 86

*LAMBA SHA HUÆŠU.*

Tafe nake ina sharɓen kuka tare da jan jakata har na fita unguwarmu. Babu motsin komai da kowa, garin ya tsit illa karnukan da nake jin kukansu nesa da ni jefi-jefi.
Sai da na yi tafiya mai nisa sannan na fara jin wani ƙugi da gurnani a bayana, cikin sauri na juya tare da dakan luguden da zuciyata ke yi. Ido na zare ina ƙoƙarin tafiya da baya-baya saboda wani Mahaukacin karen da na yi tozali da shi yana zaro harshe. Jefar da jakar kayana na yi cikin matsanancin tsoro na zunduma da gudu. Shi ma ƙaton baƙin karen ya biyo ni aguje yana ta haushi "Wu! Wu!" Tamkar an ba shi kwangilar cinye ni da raina.
Gudu nake yi iya ƙarfina yana bi na da ihu tamkar yana ƙoƙarin kama ɓarauniyar da ta yi gagarumar sata. Cikin sa'a na afka wani gida da na hango ƙofar shi a buɗe. Saboda duka gidajen da ke unguwar a rufe suke ruf, kuma ban yi Hausar samun wata kwana ko lungun da zan ɓoye masa ba.
Sakata na danna wa ƙofar gidan jikina yana rawa, ga numfashina da ke ta hawa da sauka cikin sauri saboda tsabar tashin hankalin da na shiga. Haushin da karen yake yi a bakin gidan yana yagar ƙofar ya sa na ƙara ɗimaucewa. Na bazama da gudu na yi ƙofar da na hango ta miƙe, na zarce cikin gidan a miliyan ina ihun a kawo mini agaji.
Mutanen da na gani suna fitowa daga É—akunan gidan babu suturar kirki a jikinsu, hakan ya sa na fara rabon ido ina neman wurin wanda zan nufa da sigar taimako. Domin kuwa a kallo É—aya na gano ba gidan mutanen kirki ba ne, duba da yadda dukansu suke tamkar tsirara kuma ba su ji nauyin fitowa a yadda suken ba.
Kuka na fashe da shi ina ja da baya saboda mugun kallon da na ga suna bi na da shi, a ruÉ—e na fara faÉ—in,
"Don Allah ku yi haƙuri Wallahi kare ne ya biyo ni zai cije ni, ga shi can ma yana ƙoƙarin haurowa ta katanga domin ya illata ni."

Kallon juna na ga suna yi kafin su fashe da dariya, wani É—an gajeren cikinsu ya nufo ni yana wasar baki. Na fara ja da baya ina faÉ—in,
"Don Allah ku yi haƙuri Wallahi ban san lokacin da na shigo gidan nan ba".

Daga mazan har matan dariya suka fashe da ita, sannan dukansu suka zagaye ni duk da ƙoƙarin guduwar da nake yi sai da suka yi nasarar hana ni. Wata tsamurmurar yarinya ta nufo ni daga ita sai towel a jikinta, ganin yanayinta ya sa na ƙura mata kallo har ta iso gabana ta tsaya. Hijabin da ke jikina ta fara ɗagawa na yi hanzarin buge mata hannu, ta yi mini wata munafukar dariya tana faɗin,
"Fuskarki ta nuna za mu ci abinci da ke. Don haka ki bari mu gama tantance ki kafin mu yarda da ke, don ba na raba É—aya biyu a kan cewa rashin gaskiya kika fito yi a cikin daren nan, da aka zo kama ki shi ne kika gudo kika zo gidan nan domin mu cece..."

"Ba rashin gaskiya ta fito da ni daga gida ba, asali ma baƙincikin da nake ciki ne ya sa na kasa haƙuri na fito zan koma gidanmu."
Ban yi aune ba na ji ta kai hannunta ta taɓo ƙirjina, da azama na sake buge mata hannun. Cike da jarumta na fara nuna ta da hannu cikin ƙololuwar ɓacin rai na ce, "Ban zo gidan nan don ku wulaƙanta mutuncina ba, taimako na zo ku yi mini saboda tsoron karen da ya biyo ni. Don haka ku yi haƙuri yanzu zan tafi ba sai kun nemi tozarta martabata ba."
Ina ƙare faɗar hakan na juya da nufin raɓa waɗanda ke bayana na wuce. Caraf na ji an janyo hijabina ta baya babu shiri na juya cike da tsoron da ya cika mini zuciya, kallon mamaki da rashin mutumci na hango kwance a kan fuskokinsu, ya san natsure. Nan take hantar cikina ta kaɗa na fara rawar murya ina faɗin,
"Don Allah ku yi haƙuri Wallahi mijina ne ya koro ni cikin daren nan."
"Mu dama irinki muke nema, waɗanda ake cewa je-ki-kya-gani. Domin da kin fito mu ne za ki taras. Ummita tuɓe mana ita yanzun nan mu albarkaci daren nan da kalacinta."
Abin da na ji ya faɗa ya sa fitsari kufce mini, jikina ya hau rawa tamkar mazari hakan ya bai wa fitsarin damar tsiyaya daga jikina yana sauka ƙasa. Ja da baya na fara yi saboda ganin wadda aka kira Ummitar tana nufo ni, waɗanda ke bayana kuma suka rirriƙe ni ta fara kiciniyar cire mini hijabi ina ƙoƙarin hana ta.
Mahaukacin mari na ji ya sauka kan fuskata har sai da na hango taurari, kafin na dawo cikin hayyacina na ji an fisge hijabin nawa. Abin bai tsaya iya nan ba suka fara ɗaga doguwar rigar dake jikina aka yi sama da ita za a cire mini. Hannuna na fara ƙoƙarin ƙwata da nufin na hana su tuɓe ni.
Wani saukar wani marin na ji a gefen fuskata har saman idona. Azabar da ta ziyarce ni ta sa na fasa ƙara tare da kukan kura da niyyar ƙwatar kaina. Muka fara kokawa ni da su har suka yi nasarar raba ni da doguwar rigata, suka bar ni daga wata guntuwar vest mai kama da bra, sai dogon wandon legis da ke sanye a jikina.
Idona a rufe na zille daga riƙon da aka yi mini na duƙe, hakan ya ba su damar rufe ni da duka. A duƙen da nake na yi sa'ar damƙo ƙasa, da hannuna biyu na kwaso na watsa musu a idanuwa. Ban yi jinkirin komai ba na nufi hanyar fita gidan da gudu suka biyo ni, cikin sa'a na zare sakatar na fice ina ta gudu. Biyo ni suka yi suna mini ihun ɓarawo har muka hau babban titi, a daidai lokacin d wata mota ta haske ni da ƙwan fitilarta mai mugun haske, wanda ya sa na ja na tsaya saboda na kasa gaba balle baya.

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" Ita ce kalmar da na ji an ambata cikin kunnuwana. Muryar da na ji ta sa na hau rarraba ido ina neman ta ina zan hango shi, domin ko a cikin mafarki na jiyo sautin ina shaidar muryar MD balle a farke.
Abu na ji an ɗora mini a jiki ana ƙoƙarin yi mini lulluɓi, saboda har lokacin hasken yana kan fuskata ina ƙoƙarin karewa da hannuna. Ja na na ji an fara yi ina tirjiya tare da faɗin don Allah ku yi haƙuri, saboda ban da tabbacin masu bi na ne ko kuma MD da na ji muryar shi da ƙamshin turaren shi.
Lallausan hannun da na ji an riƙa ni da shi ya sa na yi ammana da shi ne kai-tsaye na bi shi. Sai da ya saka ni cikin motar ya rufe sannan ya shiga ya tayar aguje ya bar wurin. Tafiya mai nisa ya yi kafin na ji ya sauke ajiyar zuciya mai sauti, a lokacin ganina ya dawo daidai ina sharɓen hawaye tare da shesshekar kuka cikin sauti.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.