Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 58 of 86

Kai jama'a🤭Ni dai babu luwana yasin🏃🏻‍♀️

D.AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*TALATIN DA HUÆŠU.*

Ƙwafa kawai ya yi sannan ya juya yana ƙoƙarin barin wurin, na bi bayansa da hanzari ina faɗin,
"Ka ba ni wayata!"

"Ba zan bayar ba! Idan akwai wanda zai ƙwatar miki ki kira shi ya zo yanzu!"
"Babu mai ƙwatar mini don ba yau ka saba cin haramun ba, don haka ka ba ni wayata tun muna shaida juna!"
Banza ya yi da ni ya nufi É—akinsa Barira ta bi shi tana faÉ—in,
"Don Allah Romiyo ka ba ta wayarta mu je ka ƙarasa cin abincinka."

Juyowa ya yi yana huci tare da nuna wayar a sama yana cewa, "In dai wannan wayar ce! To ba zan bayar da ita ba, gobe ma idan na sake ganin tana waya da wani ɗan iskan; sai na sake ƙwace wata."
Wurinsa isa a fusace na yi tsalle zan cafke wayar, ya yi hanzarin saukar da hannun tare da tura wayar aljihunsa. Raina a ɓace na ce,
"Ba ni wayata wallahi ko yanzu na yi abin da bai dace ba!"

"Ba zan bayar ba ki yi abin da za ki iya."

Cikinsa na yi na mamaye shi na cafko jarumarsa na murɗe iya ƙarfina, ihu ya saki tare da faɗin,

"Wayyo! Za ta kashe ni!"

Jikinsa yana rawa ya fiddo wayar daga aljihu ya miƙo mini sannan na sake shi, barin wurin na yi a fusace ina faɗin,
"Ai da kada ka bayar! Da na tsinke ta na dafa maka a tukunya ka cinye ƙazantarka."
"Ta Allah ba taki ba wallahi! Idan burin ki nakasa ni ki yi wa Barcy asara, to gani nan bari nan! A gabanki za mu shimfiɗa rayuwa mai daɗi sai dai baƙinciki ya kashe ki."
"Soloɓiyo mai aiki irin na matan ne zai iya rayuwa mai daɗi da mace? Ka bari sai ka samu cikakkiyar lafiya sannan ka yi alfakhari da burgar da iyakarta cikin baki."

"Gaskiya Aunty wallahi abin da kike yi kwata-kwata ba kya kyautawa. Ai Romiyo ko ba mijinki ba ne ya dace ki girmama shi balle yana matsayin uban 'ya'yanki."
Barira ta yi maganar tare da isa wurinsa ta lafe jikinsa tana faÉ—in,
"Ka yi haƙuri Romiyo, wasu matan haka suke yi wa mazajensu komai a tsaitsaye, tamkar tsararrrakinsu."

Kallon ta kawai nake yi saboda gaskiya ta yi mini yawan da ban san me zan faÉ—a mata na huce ba, dawowa na yi gabansu ina nuna ta da hannu na ce,
"Kada ki sake shiga sabgata idan kika ga ina yi da shi! Idan kuma kika sake zan bambance miki tsakanin aya da tsakuwa."
Shiru kawai ta yi tana turo baki bayan muimui É—in da take yi ban san me take faÉ—a ba. Sannan ta É—age kanta sama ta ja hannunsa suka yi É—akinsa.
Bayansu na bi da kallo ina wassafa irin bugun wahalar da zan yi mata idan ta kai ni bango. Ban san ya suka yi ba, ina zaune kan kujerar na ga ta fito É—akin a fusace ta yi É—akinta.

Sallamar Sajida da su Ummu Salma ta katse mini tunanin da na shiga tsawon lokaci, sannan ganin su ya kore mini rabin damuwar da Mukhtar da Barcynsa suka cusa mini a zuciya.
Riƙe da hannun Haidar ta iso tana gaishe ni a ladafce, sannan ta zauna tana faɗin,
"Tun É—azu na so zuwa bazawarina ne ya zo!"

"Sannu Sajiji! Gaskiya ki fito da miji haka nan mu aurad da ke."

Shiru ta yi sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Wallahi Aunty har yanzu ban daina jin mutuwar Abbakar cikin raina ba. Shi ya sa duk wanda ya zo nake jin kamar ba zan iya rayuwa da shi ba."

"Haƙuri za ki yi, don Allah ba ya barin mutum don wani ya ji daɗi. Lokacinsa ne ya yi, kuma Allah ya tsara ba za ku yi rayuwa mai tsawo da shi ba. Allah dai ya ƙara haske cikin ƙabarinsa"
"Hmmmmm! Haka ne gaskiya, amin Ya Allah. Wai kin san wani abu Aunty?"

"A'a sai kin faÉ—a"

Na ba ta amsa cike da ƙaguwar na ji me za ta faɗa mini. Tagumi ta yi sannan ta ce da ni,
"Mijin maƙociyar nan taki ne yake ta damuna da zancen aure. Ni kuma wallahi kirkin da na ga kuna yi da ita, ya sa ba na son na rufta. Amma ke ya kike ganin lamarin? Don na ga matarsa da shegen kishin tsiya."

"Wace maƙociyar daga ciki?"

"Wannan Maman TaufiÆ™ É—in."

Daram-dam! Shi ne sautin bugun da ƙirjina ya yi zuciyata ta hau bugawa.

"Ina ya gan ki?"

Na jefo mata tambayar a ruɗe bakina yana rawa. "Bari kawai Aunty! Tun ranar bikin da muka je gidanta dafa abincin baƙinki. Ina hankalce da shi yana satar kallo na, hakan ya sa na mayar da hijabina da na cire saboda aiki. Ban san ya aka yi ya samu lambata ba, kawai da dare bayan na koma gida sai ga kiransa a wayata. Bai ɓoye mini komai ba ya sanar da ni so na yake yi da aure, saboda wadda zai aura tsohon mijinta ya dawo Iyayenta sun matsa mata sai ta koma gidansa, ko don yaran da ke tsakaninsu. To ni kuma wallahi ina tsoron kishin matarsa, ga shi mun yi mutunci da ita sosai a lokacin hidimar bikin nan. Har ga Allah ina jin kunyar na auri mijinta, ga shi kuma ya nace mini da kira dole sai na faɗa masa ra'ayina. Shi ya sa na ce zan yi shawara da ke duk yadda kika ce shi kenan."
"Cabɗijam! Akwai matsala Sajida! Don wallahi matar nan ta shi ba dai kishi ba. Hmmm! Kin san me? Kawai ki ce da shi ya yi haƙuri kina da wanda za ki aura."

"Haka za a yi Aunty! Don ni ma dai ina jin nauyi wallahi. Sannan É—an banzan kishin nan na matarsa ma ba zai bari mutum ya ji daÉ—in auren ba."
"Kin gane karatun! Allah ya ba ki wani nagari ki yi auren ki ki huta."

"Amin wallahi!"

Shiru muka yi dukanmu kafin muryar Barira ta katse mana tunanin zucin da muke yi, saboda waƙar da take yi cikin ɗaga murya tana faɗin,
"Allah ya aika munafukinmu ƙarshen nesa."
"Tafiyar ƙasa ko da lafiya ko babu."
"Na sha tabara na sha yasin."

Ƙaƙƙarfan tsaki Sajida ta buga mata sannan ta ce da ni,
"Aunty kawo wayarki na saka miki hotunan biki da aka yi mana. Na so tura miki ta WhatsApp, ganin zan zo gidan ya sa na fasa"

Na miƙa mata wayar ta loda mini su duka. Ta miƙo mini wayar tana faɗin,
"Hotunan sun yi kyau duba ki gani. Na ma saka miki wasu status É—inki."

Ras na ji gabana ya faÉ—i, saboda ban so ta É—ora wanda muke da Mukhtar ba. Na goge inda nake da shi duk da na san masu GB dole sai sun gan shi.
Hira muka ci gaba da yi, da ta tashi tafiya muka yi sallama na raka ta har bakin ƙofar gida. Daidai lokacin da Baban Taufiƙ ya danno kan motarsa ya durfafi ƙofar gidansa.
Juyawa kawai na yi don ba na so ma na ga abin da zai biyo baya. Saboda har ga Allah ba na fatar Sajida ta aure shi ko don Maman TaufiÆ™ da halinta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.