Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 17 of 86
_Rayuwar amarcina da Mukhtar gwanin ban daɗi, duk da ina shan mamakin yadda ba ya barin kuɗi a hannuna. Duk abin da aka ba ni shi yake karɓewa, kuma ba na jin ko ɗar haka zan miƙa masa. Saboda ina tunani tara mini yake yi gudun a sace, duba da yadda gidan yake cika da mutane koyaushe ana zaryar zuwa ganin amarya da muhallinta. Domin babu abin da ba a yi mini na 'ya'yan gata ba, kayan ɗakina ma abin kallo ne bayan ƙattin kujeruna da suka canye filin falon. Bayan firij da sabuwar telar da aka haɗo ni da ita, domin na nemi na kaina kafin na fara aiki._
_Har a raina ina so na yi alheri ko da kuÉ—in abin hawa ne idan dangin Ummata suka zo wurina, amma babu ko ficika a hannuna. Sai idan an yi katari yana gidan na tambaye shi ya ba ni na ba su._
_Ashanar da nake tsinta a cikin É—akina ko falo lokaci bayan lokaci, ita ce abu na farko da ya fara É—aure mini kai a gidan Mukhtar. Tun ba na kula har na fara tambayar shi ko shi yake ajiye ta, amma ya nuna mini shi ma bai san da ita ba. Cikin tsoro nake tofe ashanar da addu'a sannan na É—auke ta na kai na ajiye, abin mamaki kuma sai na nemi ashanar inda na ajiye na rasa. Idan na tambaye shi shi ya É—auka ya ce da ni a'a, tun ina bi ta kai har na watsar ina ci gaba da addu'o'in tsari saboda ina da tsoro sosai._
_Matsala ta farko da na fara cin karo da ita a wurin Mukhtar ita ce rashin tashi sallar asuba. Ba ya yin salla sai ya yi wanka idan zai fita wurin aiki, wani lokaci har ƙarfe takwas da rabi yana kai wa bai yi sallar asuba ba. Abin ya fara damuna na fara yi masa ƙorafi a kan hakan, saboda duk na tashi sallar asuba sai na tayar da shi amma ya ƙi tashi. Wani lokaci ma tsaki yake yi ya juya kwanciyar shi ba tare da ya tashi ba._
_Tun yana jin haushin takurar da nake yi masa har ya fara tashi yana yi ba don yana so ba, don wani lokaci ma har ya tafi wurin aikin shi yana fushi ba ya sake mini fuska. Abin yana ba ni mamaki sosai duba da masallacin da ke ƙofar gidansu, wanda kira da Sallar shi duka ina ji tar-tar har cikin ɗakina._
***
_Watana ɗaya da sati biyu gidan Ummata da matar Yayanta suka zo ganin ɗakina. Saboda tsabar murnar ganin su bakina har kunnena, na tarye su da abin da nake da shi sannan na kira shi na sanar da shi zuwan su. Mintuna a tsakani ya zo da kayan marmari da jiƙa maƙoshi, na saka musu a tire na ajiye gabansu suna gaisawa da shi. Kan shi a duƙe cikin tsantsar ladabi har suka gama ya fice, na gabatar musu da abin taɓa bakin muka fara hira. Matar Kawuna ta shiga binciken zamanmu a fakaice na sanar da su komai lafiya, domin su tabbatar da abin da suka ce sun ji a bakin mutane. Dangane da zaman lafiyar da ke tsakanina da Mukhtar. Domin duk wanda ya zo ba ya gani na cikin baƙar fuska balle rashin walwala, hakan ne yake nuna zaman lafiya da jin daɗin aurena a zahiri._
"Zaituna ya zancen lefenki! Mun yi ta jira mu ji kin kira mu zo mu gani amma har yanzu babu labari. Ko dai ya ba ki mu ne ba ki faÉ—a ma ba?"
_Maganar Inna Kulu kenan domin ta ji ba'asi a kan lefen da ni ma nake bitar zancen shi cikin raina koyaushe. Domin na kasa yi wa Mukhtar tuni a kan lefen, saboda ba na so ya ga na cika zalama. Shi ya sa na dakata domin na ga zurfin gudun ruwan shi. Tambayar da Inna Kulu ta yi ta fama mini damuwar abin a raina, amma na bagayar da faÉ—ar,_
"Ko jiya mun yi zancen ya ce na ƙara haƙuri kwanan nan Iyayen shi za su kawo mini".
"Ma Sha Allah! To Ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna. Idan suka kawo ki sanar da mu cikin lokaci domin a san me za a bayar tukuici".
_Dariyar yaƙe kawai na yi tare da ɗaga kai, cike da fargaban kada Mukhtar ya sa na ji kunya a kan ƙaryar da na yi musu, domin na ƙare masa martabar shi a idanuwansu. Lokacin da za su tafi na kira shi ya ba ni ɗari biyar na ba su, shi kuma ya ba su dubu biyu suka ce ba za su karɓa ba. Da ƙyar na matsa suka karɓa ko shi sai da ya fice sannan suka karɓa a hannuna._
_Da dare lokacin da muka kwanta bacci yana wasa da jikina nake yi masa tambaya a kan lefen, nesa da ni ya koma ya juya mini baya bai ce da ni komai ba. Shiru ya ratsa tsakani sai tashin minsharin shi na ji alamun ya yi bacci. Na É—auki lokaci ina tunanin abin da ya sa ya yi mini haka daga tambaya, ban san lokacin da bacci ya yi awon gaba da ni ba._
Hmmmm! Labari ya soma😅
D. AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
_*Littafina free ne ban yarda a sayar da shi ba, ko a juya shi ta wani ɓangare ba tare da izina na ba😒*_
*LAMBA SHA BIYU.*
_Da safe ma haka muka tashi yana haɗe fuska, shirin fita ofis ya yi yana ƙoƙarin ficewa na sha gaban shi tare da riƙo hannun shi. Cikin damuwar da ta bayyana kanta a saman fuskata na ce da shi,_
"Wai me hakan yake nufi ne? Ban san me na yi maka ba jiya daga magana ka yi fushi da ni. Yanzu ma ga shi kana ƙoƙarin ficewa babu walwala. Don haka don Allah ka yi haƙuri idan har akwai abin da na yi maka ban sani ba"
_Bai ce da ni komai ba, ya zare hannuna daga riƙon da na yi masa ya fice. Zama na yi cikin sanyin jiki tare da yin tagumi hannu biyu ina tunani, da zancen zucin da na shiga yi ni kaɗai ina bai wa kaina amsa. Domin jikina ya ba ni kamar akwai wata matsala dangane da lefen, shi ya sa ba ya son maganar kuma ba ya son tattauna maganar da ni. Ajiyar zuciya na sauke tare da cin alwashi a raina, ba zan sake yi masa maganar lefen ba._
_Domin matuƙar tayar da zancen zai kawo mana rashin jituwa to babu amfanin dawo da hannun agogo baya.Tun daga lokacin ban sake yi masa maganar ba, shi ma bai ce da ni komai a kan hakan ba. Ummata ma tun tana tambaya ta har ta daina, wataƙila kame-kamen da nake yi wurin kare Mukhtar, ya sa ta gano abin da nake ƙoƙarin ɓoye mata._
_Wata uku da aurenmu na samu ciki, wanda ni ban ma san da shi ba, har sai da Mamar shi ta turo mini abokiyar zamanta tana tambayar, yaushe rabon da na ga al'adata. Shiru kawai na yi ina tunani kafin na yi mata bayanin wata ɗaya ne kawai ban gani ba. Farinciki kwance a kan fuskarta ta fice, na bi ta da kallon mamaki domin kaina ya ƙulle da tambayar. Saboda na manta shaf da wani zancen ciki."
_A lokacin da Mukhtar ya dawo gidan da yamma, na fahimci kamar yana cikin damuwa duba da yadda ya yi zaune shiru yana tunani. Domin ko abincin da na kawo masa bai ci ba sai cizon haƙoran shi yake yi. Zama na yi kusa da shi cikin kulawa na ce da shi,_
"Fatan dai lafiya?"
_Shiru ya yi mini ba tare da ya ce da ni komai ba, ya duƙar da kan shi ƙasa yana kallon ledar da ke malale cikin falon nawa. Ni ma ganin haka ban sake cewa da shi komai ba na yi shiru ina tunanin wa ya taɓo shi._
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.