Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 48 of 86

Sanyin daɗi na ji ya tsirga mini, domin labarin da Maman Taufiƙ ta faɗa mini ba ƙaramin faranta zuciyata ya yi ba. Shiru kawai na yi ina ta murmushi, sai da ta yi 'yar kuwwar jin daɗi sannan ta sake cewa,
"A gaskiya Maman Haidar ke ƙwaro ce! A tashi guda kin hargitsa musu lissafi sun fita da ke a bakinsu."

Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Ai shi yaƙi ɗan zamba ne, idan ba ka iya shi ba za ka sha wahalar kashe abokan gaba, kuma za a yi saurin gano maɓoyarka domin a kawo maka farmaki. Don haka ta wannan hanyar kaɗai zan iya rama abin da ake ƙoƙarin yi mini a fakaice. Saboda faɗa da tashin hankali ba zai kawo gyara ba, kuma ba zai sa a fasa abin da aka yi niyya ba. A ƙarshe ma biyu babu ake yi a rasa mutunci kuma a ɓarar da ƙima."
"Kai jama'a! Maman Haidar ke ta daban ce a cikin dubban mutane. Ban taɓa cin karo da macen da za a yi wa kishiya ta yi juriya irin taki ba. Wai don Allah da gaske ba kya jin komai a cikin ranki? Ni fa na kasa gasgata wannan lamari naki mai kama da almara."
Tambayar da ta yi mini ba ƙaramar dariya ta saka ni ba, saboda yanayin da ta yi maganar tamkar wata zautacciya. Sai da na gama dariyar sannan na ce da ita,

"Kowace mace tana da kalar nata kishin Maman Taufiƙ! Amma da a ce za a yi koyi da kalar kishin da magabata suka yi; Da mata da yawa ba su ɓarar da damar da Allah ya mallaka musu ba. Don sau da yawa namiji ba don ba ya son matarsa yake ƙara aure ba, ke wani lokaci ma ba ya ƙara ƙaunarki; har sai ya jera ki da wata ya gano akwai tazara a tsakaninki da sauran mata. Saboda haka da a ce za mu gane mu daina zafafa kishin maza idan za su ƙaro aure, da mun taimaki kanmu mun rage nauyin wahalar da muke ɗaukar wa kanmu a kan ɗa namiji. Ni kin ga ma a ranar da ya zo mini da zancen auren..."
Na kwashe duk yadda muka yi da Mukhtar na faɗa mata, dariya ta shiga sheƙawa har da riƙe ciki. Sai da ta gaji don kanta tana goge ƙwallar dariyar ta ce da ni,
"Wallahi ba ki da kirki Maman Haidar! Wannan tura haushin har ina saboda Allah?"

"Da a ce ban yi masa hakan ba, hauka zai siyo kasuwa ya manna mini ban ji ban gani ba. Saboda duk wani tashin hankalin da zan yi a lokacin; kai-tsaye zai ɗora shi a mizanin taɓin hankali. A ƙarshen ma zagina mutane za su dinga yi ba tare da sun yi duba da ƙunar da zuciyata ke yi, su tausaya mini ba."

"Wallahi zancenki gaskiya ne Maman Haidar! Amma kin san me? Ni ba zan iya wannan dauriyar ba. Allah kada ka jarrabe ni da irin wannan musibar mai wuyar shanyewa, don na san duk ranar da Amini ya sanar da ni zai yi aure; ba zan É—aga daga inda nake ba zan mutu."

😱cab!🤭 Na yi nan🏃🏻‍♀️

D.AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*ASHIRIN DA TARA.*

"Ba za ki mutu ba!"
Zancen da na faɗa mata kenan cike da karsashin da ke cikin raina. Wani kallo take yi mini ko ƙyaftawa babu, kafin ta muskuta kaɗan tare da sauke ajiyar zuciya ta ce,
"Ni kaɗai na san yadda nake jin zafin abin a cikin raina. Yanzu haka ke za a yi wa kishiyar nan, amma wallahi har zuciyata nake jin ƙunar kishin a haɗa ki da wata, a matsayin abokiyar zama a cikin gidan nan."
"To ki ma daina, don ni babu wani abu da zan gani yanzu a gidan nan, wanda zai ɗaga ni sama balle ya buga ni a ƙasa na ji zafinsa. Ke ma da za ki sauke tulin nauyin da kike ƙoƙarin lodawa, da kin taimaki kanki kin huta da tashin hankalin da zai iya bijiro miki a gaba."
Na faɗa mata maganar ne daga zuciyata, don na fara ƙosawa da ɗora ta a kan hanya tana zamewa. Shiru ya ratsa tsakani ba tare da mun sake cewa komai ba.
Girgizar ƙafar da take yi, tare da haɗe fuska da cizon leɓe; ya tabbatar mini da ba ta ji daɗin maganar da na yi ba. Hakan ya sa na yi hanzarin faɗin,
"Ki yi haƙuri da ni Maman Taufiƙ! Amma Allah ya gani ba na son wannan zaƙewar da kike yi wa kishi, maimakon ki yi masa rigakafi tun kafin ya riske ki; amma ke kullum sai ƙara taryar gabansa kike yi domin ku yi arangama."
Na tsahirta da maganar ina karantar yanayinta, sannan na É—ora da cewa,
"Ina faɗa miki wannan maganar ne a matsayinki na wadda na yarda da ita, kuma nake yi mata kallon ƙawa, aminiya, kuma abokiyar shawara. Don haka ki yi haƙuri da gaskiyar da nake faɗa miki tsakani da Allah babu rufa-rufa."

"Na san gaskiya kike faɗa mini, amma zancenki na ƙarshe ya yi matuƙar taɓa mini zuciya. Domin ina ji a raina tamkar kina mini bushara da zuwan tawa kishiya bayan taki."
"Maganar da na faɗa ko kaɗan ba ta danganci hakan ba, don ba na fatar a yi miki kishiya ko don wannan zazzafan kishin naki. Amma ina miki hannuka mai sanda ne saboda ki karɓi abin da ya shiga gabanki; ko don kare kanki daga matsalar da ke biye da ke, ba tare da kin shirya wa zuwan ta ba."
Miƙewa ta yi tana dakan ƙasa da ƙafafuwanta tamkar wata yarinya, fuskar tausayi ta yi tare da langaɓe kai ta ce,
"Oh my God! Kin sake kwatawa Maman Haidar. Ni wallahi shi ya sa ban cika son muna zancen kishiya da ke ba. Saboda kina bar mini zantukanki koyaushe suna mini zillo a zuciya."
"To na daina mu zubar da zancen duka! Gobe idan Allah ya kai mu za a yi wa amarya jere. Me kike ganin ya dace a yi musu a matsayin abincin da za su ci idan sun zo."
Zama ta yi tana haÉ—e rai tare da aiko mini harara ta ce,
"Wannan nauyin ai ba naki ba ne Hajiya! Ki jira idan angon ya zo ku yi shawarar abin da za a yi musu. Don haƙƙinsa ne, kuma shi zai bayar da duk abin da za a dafa daidai ƙarfinsa."

Murmushi na yi mai sauti sannan na ce, "Yo to ni ina na san yadda abin yake? Na É—auka kamar yadda muke dafa abincin gida haka za a ba su su kora da ruwa. Ashe abin babba ne ba yadda na zata ba?"
"Idan ya zo kuka gama shawara, sai ki kira ni a waya ki sanar da ni. Saboda goben a yi komai da wuri ba sai sun zauna jira ba."
Natsuwata na shiga sosai ina É—aga mata kai tamkar wata doluwa, saboda tunanin da zuciyata ta faÉ—a. A kan yadda za mu kwashe da shi hanyar 'yan barkono idan na yi masa zancen. Na so ko bai sani ba na yi musu girkin na fita kunyar idonsu, saboda ba za su yi zaton shi ne da laifin ba idan an hana su abincin. A kaina komai zai juye su je su yi ta zagi na a banza ban ji ban gani ba.
Daga haka muka kitse zancen na rako ta har bakin ƙofar gidan, muna ci gaba da tattaunawa su Ummu Salma suka dawo makaranta.
Cikin sa'a shi ma mai mashin ya dire shi a ƙofar gidan yana shan ƙamshi, Maman Taufiƙ ta yi hanzarin shigewa gidanta ni ma na koma cikin gida. Tsakar gidan na ja na tsaya bayan yaran sun shige ciki.
Ya shigo gidan ko sallama bai yi ba zai wuce buguzum! Na yi hanzarin bin sa a baya ina faÉ—in,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.