Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 34 of 86
Amina na bai wa ta karanta, sannan ta dawo mini da wayar tana faÉ—in.
"Sannu gwanar hikima da azanci. Allah ya ba ki iya tsara magana da hangen nesa. Ina ma kaso mafi rinjaye na mutanen duniya haka suke. Da an samu rangwamen cakwalkwalin cakwakiyar da ya baibaye mutane a wannan lokacin da muke ciki. Ubangiji ya kawo miki mafita a cikin rayuwarki."
Amin Amina. Tare da sauran masu Matsala irin taku da ma wadda ta fi.ðŸ‘ðŸ»
D. AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ASHIRIN DA ÆŠAYA.*
Mun tattauna sosai da Amina, tana sanar da ni matsalar Basiru mijin Sara. Da irin tataɓurzar da aka yi da su a lokacin da suke ganiyar rashin mutuncinsu. Bayan an tashi muka fito bakin ma'aikatar muka tsaya, da niyyar neman adaidaita amma muka buge da hira.
Amina ta kalli agogon da ke hannunta ta ce da ni, "Yau dai na yi missing ba a tsakura mini komai daga cikin labarin ba. Ga shi na matsu na ji yadda ta kaya a lokacin da kika shiga É—akin, domin ina so na ji me ya ba ki tsoro wanda ya sa kika yi salatin da, har yanzu ban daina jin sautinsa cikin kunnuwana ba."
Baki kawai na riƙe cike da mamakin sharotan da take ƙoƙarin yi, domin kawai ta yi mini daɗin bakin da zai sa na ɗora mata labarin, daga inda na tsaya ban shirya ba. Cike da zolaya na ce da ita,
"To ko za mu tsaya ki ji sauran kanun labarin ne?"
Cikin sauri ta dawo daga bakin titin da ta nufa tana ƙoƙarin tare wani ɗan adaidaitan da zai wuce. "Wallahi in dai za ki ƙarasa mini labarin yanzu, to na yarda mu kai wata safiya a nan ba tare da na ƙosa ba."
"Rufa mini asiri kada ki sa Mama ta zo har wurin nan ta ci ubanmu."
Dariya muka fashe da ita dukanmu, kafin na shammace ta na shige adaidaitan. Da hanzari ta matso inda nake tana faÉ—in, "Ji nake kamar na biyo ki mu je tare wallahi. Domin har ga Allah matse nake da jin labarin nan, kamar na yi tsuntsuwa na dira tsakiyar É—akin domin na ga komai ba sai na jira an sanar da ni ba."
"Ai kuwa dole ki jira har lokacin da za a sanar da ke, don haka mu haÉ—u goben kawai Hajiya ko shi idan da rabon ki. Domin haka kawai ba za ki janyo mini fushin Mama ba. Tsautsayi ya sa a binciko mata inda nake ta ci kwakwata, ni kin ga tafiya ta mu kwana lafiya ki gaishe da my boy."
Daga haka muka tafi muka bar ta a tsaye tana aika mini harara har da ƙwafa. Hakan ya sa ko da muka yi nisa ban rufe bakina daga dariyar da ta ba ni ba, sosai nake tsintar kaina cikin farincikin a duk lokacin da muna tare, domin tana ɗebe mini kewar 'yar uwa macen da na rasa kuma ƙawa makusanciya.
***
Mamaki fal raina a lokacin da na shiga gidan na yi tozali da kayansu Ummu Salma tsibe , na bi kayan da kallo cike da tunanin me ya kawo jakunkunan su a ƙofar ɗakina. Duk da oyoyon da suke mini bai sa na ɗauke kallona daga kan kayan ba.
Da sassarfa na isa bakin ƙofar ɗakinsu ina murɗa handle idona ƙur a kansu, tare neman ba'asin dalilin da ya janyo hakan, tambayar da tun kafin na furta ta fito da kanta cikin ƙwayar idona.
"Mu ma ko da muka dawo mun taras da kayan a wurin. Kuma har yanzu Abbanmu bai dawo ba balle mu ji ko shi ne ya fito mana da su."
Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi sannan na ce, "Ku ɗauko kayan mu je ɗakina, idan ya dawo mu ji me yake nufi."
Da ƙyar na yi maganar saboda hadarin baƙincikin da ya taso ya rufe idona. Guguwar takaici ta sa ban iya ɗaukar komai daga cikin kayan ba. Domin har da katifunsu biyu tasu ita da Iman da ta Haidar.
Sun shigar da kayan duka a lokacin da na kammala sallah, a kan kayan na ɗora idona saboda tunanin abin da yake nufi da abin da ya aikata. A take zuciyata ta hasko mini zallar manufar shi duk da bai faɗa mini ba, duba da kalaman barazanar da ya yi mini a ranar da ya tuna da haƙƙinsa da ke kaina.
'Wallahi duk abin da ya biyo baya kada ki ga laifina. Ba dai kin hana ni haƙƙina ba? To ke kuma ki jira me zai faru cikin kwanan..'
Maganar shi kenan da ta faÉ—o mini rai, kuma ta shiga kunnena tamkar a lokacin yake furta mini ita.
"Waton aure zai yi?"
Tambayar da na jefi kaina da ita kenan a fili, sannan wani murmushi mai sauti ya suɓuce mini ba tare da na shirya ba, saboda tabbacin da zuciyata ta ba ni a kan hasashen da nake yi. Nan take wani sabon kuzari ya ziyarce ni, wanda ya kore rabin damuwar da ya haifar mini a lokacin.
Ummu Salma na ƙwala wa kira, ta shigo ido tsakar ka bayan ta amsa kiran, sallayata na shiga naɗewa ina cewa, "Zo mu saita kayan nan. Kafin lokacin makaranta ya yi."
Da Mamaki ta bi ni da kallo wanda ya nuna tambayar da take son yi mini, ina mata 'yar dariya na ce, "A nan za ku dawo da zama dukanku. Don daman can ina ta so ku dawo nan mu dinga kwana tare. Kafin lokacin da Haidar zai ƙara girman da za a ware masa makwancinsa daban."
Farinciki mayalwaci ya ziyarci fuskarta, ta fara murna tana ƙwala wa su Haidar kira bakinta har kunne, ko da suka shigo ta fesa musu labari suka hau ihu, domin alamunsu ya bayyana jin daɗinsu a kan sabon tsarin da nake ƙoƙarin zartarwa.
Tare da su duka muka gyara ɗakin tsaf komai muka tanadar masa a muhallinsa, duk da katifar Haidar ba ta samu wuri ba dole jingine ta muka yi. Saboda an laƙume ɗan filin ɗakin da katifar su Ummu Salma, sannan da jakunkunan kayansu. Don ma na cire wasu na saka a wardrobe domin a rage tarkacen kayan.
Saboda suna da sutura sosai domin ba na ɗaukar lokaci ban yi musu ba, musamman Haidar da ko kan hanya na zo wucewa na hango yadin da ya burge ni, sai na saka an yanka masa ko da iya kuɗin jakata kenan. Wani kuma idan ban da kuɗin, cewa nake yi a yanka a ajiye mini. Daga baya na dawo na karɓa tun a lokacin da yake cin yadi ɗaya, har yanzu da yake shekara bakwai ya fara laƙume yadi ɗaya da rabi.
Su ma atamfa É—aya nake saya a É—inka musu su biyu, saboda Ummu Salma shekararta goma sha biyu, Iman ce mai shekara tara. Domin tsakaninta da Haidar babu tazara mai yawa, kuma yana da jikin girma, don ya kusa kamo tsawon Iman.
Bayan sun tafi makaranta da murna, na shirya na nufi gidan maƙociyata Maman Taufiƙ. Saboda na yi sha'awar ganin ta kwana biyu ba mu haɗu ba, daman can makulli ke sa ina shiga gidan idan yara sun bar mata. Ita ma halin Mukhtar da zargin da yake yi mata, a kan tana zuga ni ya sa ta rage zuwa gidanmu.
Da fara'a ta tarbe ni muka zauna murmushi a kan fuskata muka gaisa, ta kawo mini molt da ruwa a faranti, sannan da doghnut a gefe. Domin É—abi'arta ce da wuya a shiga gidanta a fito ba ta karrama mutum da abin da take da shi ba. Su Ummu Salma har É—okin suke yi na aiko su wurinta, domin ba za su fita hannu rabbana ba sai ta musu alheri ko da babu yawa.
Saboda kaf unguwar babu inda nake zuwa sai wurinta, haka su ma babu inda nake bari su je sai gidan. Ko shi iya aiken da ya kai su kawai suke yi su fito, saboda maigidanta kullum yana gidan. Sannan a gaban kowa ba ta shayin nuna masa ƙauna sai dai shi mutumin da ya zo ya ji kunya, saboda yaronta ɗaya Taufiƙ kuma ya yi shekara sha huɗu har yanzu ba ta sake haihuwa ba.
Rayuwarsu tana burge ni sosai, saboda ta yi dacen mijin ƙwarai kuma wanda ya san muhimmancin aure. Dalilin da ya sa ba ta gano matsalar Mukhtar a yadda nake sanar da ita, ta fi ɗora mini laifi a kan wasu abubuwa ko da ta gani da idonta. Ganin take yi rashin tattalin miji ne yake janyo mini abubuwan da ke faruwa. Kayan mata babu kalar da ba ta ba ni, amma sai dai na ajiye ko na kyautar don ni babu amfanin da za su yi mini.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.