Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 65 of 86

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'uun! Me ya sa ba ku nemo ni tun wuri ba?"

"Share da ita kawai duk ita ce ta ƙulla komai! Kuma ko za ta mutu wallahi ban ce ka janye ƙudurinka ba! Ita kuma Barira; ki sani duk abin da aka yi mata danginta suna tafe gun ki, domin su ɗaukar mata fansa a kan abin da kika sa aka yi mata."

Hannuna na rungume a ƙirji bakina yana rawa na ce, "Idan har sun fasa zuwa Allah ya tsine musu albarka. Idan sun zo ka ce kada su bar ni da raina tun da kai ba ka taɓa sanin mene ne adalci ba!"

"Haka kika ce!?"

"Haka na ce!"

Ina ƙare maganar na kai kallona a kan Baban Taufiƙ cikin matsancin fushi na ce,
"Ko ka janye zancen auren nan! Ko ka yi sanadin salwantar rayuwaka da yawa, ciki kuma har da kai idan ka nace wa abin tun da ku maza ba za ku damu da damuwar mace ba; muddin kuna son faranta wa zukatanku babu ruwanku."

Ina gama faɗar hakan na yi cikin gida da sauri tamkar zan tashi sama saboda tsananin ɓacin ran da nake ciki.

Ummata na kira a waya bayan na saita kaina na ce, "Su Ummu Salma su kwana a can, saboda gidan babu kwanciyar hankali."

"Me ya faru!?"

Ta jefo mini tambayar cikin sauri tare da É—aga murya.
"Mijin Maman Taufiƙ ne yake son auren Sajida, shi ne Mukhtar da Yaya Maimuna da amaryarsa suke ƙoƙarin haɗa mini tuggu a wurinta. Garin tsegumtawa Maman Taufiƙ da Amaryar tasa ta yi ƙoƙarin yi. Ta shaƙe ta har da cire mata tsoro uku, kuma Mukhtar ya ƙi tsayawa na yi masa bayanin yadda abin yake. Sai sanar da ni yake yi dangin amaryar za su zo su ɗauki fansa kaina."

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un! To ki dawo gida kawai tun kafin hakan ta kasance. Don wallahi duk uban da ya taɓa ki a faɗin garin nan sai na nuna masa kina da gatanki. Shi kuma Mukhtar ki bar ni da shi zan ci uban shi a wannan gaɓar."
"Kwantar da hankalinki Umma, wallahi babu inda zan je! Don za su zargi tsoro ne ya sa ni guduwa."

"To ki jira ni gani nan zuwa yanzu!"

Tana ƙare maganar ra kashe wayar, wanka na sake yi saboda gabaɗaya jikina ciwo yake yi. Domin ba ƙaramin gumurzu na yi da aljanun Maman Taufiƙ ba, don ni kaina ban san ina da irin wannan ƙarfin halin ba sai a lokacin.

Ina ƙare sallar magrib ko tashi ban yi daga kan sallaya ba, na fara jiyo sautin mata da maza suna aiko mini zagi tare da faɗin ina nake na fito.
Tsam na miƙe na fito cikin jarumta kamar yadda suke umurta ta, sai da na rufe ɗakina da makulli sannan na fara faɗin,

"Ga ni ta nan! Idan akwai abin da za ku yi mini; don Allah kada ku bar ni da raina!"

Wani matashin saurayin da a kallo ɗaya na gano ɗan daba ne, ya fara buga zabgegiyar bulalar da ke hannunsa ƙasa yana faɗin,

"Jarkutumar babakeren alllin karmatakon..."

Ya ƙare da lailayo wata uwar ashariya ya sauke mini, tare da yin ihu yana ƙoƙarin kai mini duka aka rirriƙe shi. Ya fara yunƙurin kufce taron dangin riƙon da suka yi masa, yana ta zillo domin ya dake ni.
Sai ga jiniyar 'yansanda wiwi tamkar unguwar za ta tashi, saboda dirin motocin da na ji har cikin gidan. Mintuna a tsakani sai harbi muka jiyo.

'ÆŠwa-É—wa!!'

Babu shiri dukansu suka fara ihu tare da gude-guden neman maɓoya. Rungume hannuwa na yi a ƙirji ina yar dariyar mugunta tare da komawa cikin kujeruna na hakimce.
Sai ga ɗan wiwin ya zo kusa da ni yana dafa tafin ƙafata, tare da duƙar da ƙansa ƙasa yana faɗin,

"Don Allah ki yi mini rai! Wallahi ko sati ban yi ba da dawowa kurkuku. Idan na koma ban san loakacin da zan fito ba!"

Ƙafa na saka na kai masa harbi a muƙamuƙi, ya yi saurin dafe gefen bakinsa yana muzurai. Fuskata a haɗe na ce da shi,
"Gara ka koma can ka ci gaba da rayuwa don har yanzu ba ka san Annabi ya faku ba!"

Ummata na ga ta shigo gaba 'yansandan a bayanta fuskarta a cure cikin takun taƙama. Sannan ta ja ta tsaya inda nake tana dudduba kujerun jikina, wanda kai-tsaye na gano raunin da take zaton sun yi mini take dubawa.
Ganin ina murmushin ƙarfin hali har da gaishe ta, hakan ya sa ta ce,
"Alhmdulillah!"

Sannan ta juya wurin 'yansandan tana faÉ—in, "Ofisa! A tafi da su dukansu har matan babu wanda za ku bari!"

Haka aka dinga tasa ƙeyarsu ana dukan ɗuwawunsu da kan bindiga har aka fice da su dukansu. Sannan Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce da ni,

"Tashi mu je gida!"

Kallonta na dinga yi kamar ba ita ba, saboda umurnin da take ba ni a kan mu je gida tamkar almara.
Domin wannan ne karo na biyu da ta ba ni umurnin zuwa gida da kanta ba tare da na nema ba. Na farko lokacin da Mukhtar ya faÉ—a wa danginsa da mutanen unguwar na ce sai na kashe shi, ko na kashe kaina idan bai sake ni ba.

Tana gaba ina bayanta muka fice gidan, adaidaitar da ta zo da ita muka shiga. Bayan Yansandan sun tafi da dangin Barira. Sai dai har muka je gidan Kawu Sale ba ta sake cewa da ni komai ba.
Domin na fahimci fushinta ya gama kai wa maƙurar, tun daga fuskarta da yanayin iskan da take furzarwa. Bayan ajiyar zuciyar da take saukewa lokaci bayan lokaci.

Manage plss😢 ni da yarona duka babu lafiya.

D. AUTA CE✍🏼

*ABOKIN AIKINA*

*@HADIZA D. AUTA*

*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*

*Alhamdullah! Jiki da sauƙi. Na gode sosai da addu'o'inku. Allah ya saka da alheri. Luv u all😘*

*TALATIN DA TAKWAS.*

Shiga muka yi gidan tare da Umma tana gaba ina bayanta, yaran suka zo da gudu suna murnar gani na. Rungume ni suka yi dukansu tare da faÉ—in,
"Oyoyo Mama!"
Babu shiri na yi hanzarin shanye ƙwallar tausayin su da ta cika mini ido. Saboda har kullum ina tausaya musu a raina, a kan zaɓen tumun daren da na yi musu, wurin nemar musu kamilin uba kuma majinginarsu. Inna Kulu ta fara tsokanar su da cewa,
"Lalle ɗan aro ba ɗa ne ba, waton saboda ganin uwarku har kuna ƙoƙarin ture Kakarku. To ke Habi ki san zaman da kike yi da su, duk wani daɗin bakin da suke yi miki na rashin ganin ta ne a kusa da su.
"Kai Inna Kulu! Kada ki haÉ—a mu da Umma, ki sa gobe ta ce ba za ta yi mana É—an malele ba."

Abin da Ummu Salma ta faÉ—a kenan tana dariya tare da tsalle tana son rufe wa Inna Kulu baki, a kan ta yi shiru.
"Daina rufe mini baki sai na faÉ—i gaskiya."

"To ai muna son Umma ita ma ta sani."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.