Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 79 of 86

"Wannan ai ƙazanta ce wallahi! Amma idan kika gan shi fes-fes da shi kamar bai san wani abu ƙazanta ba." Cewar Inna Kulu kenan suna ƙoƙarin ɓalle gado bayan an fitar da katifu. Dariya na fashe da ita ina faɗin,

"To wallahi Inna har da majina yake kaftawa ƙasan toilet ɗin sai na zo takawa na ji santsinta ya kwashe ni. Sannan ko a gidan nan haka yake duk da ɗakinsa daban nawa daban, amma warin da toilet ɗinsa yake yi wani lokaci har cikin falon nan gabaɗaya gamewa yake. Saboda ba ya flooshing tsawon kwanaki, warin kashin ya haɗe da warin tabarsa wuri ɗaya, ana tura kai ɗakinsa dole sai an fito ana toshe hanci. Da ƙyar na samu ya daina rashin zuba ruwa ko shi sai da na fara yi masa gorin; a gan shi a hanya tsaf-tsaf! Ɗakinsa kamar shekar ɓeraye. A haka nake ta jifar sa da maganganun da zai suke sa yana jin haushi har ya gyara dolensa. Saboda na yi iya ƙoƙarina wurin ci gaba da wanke masa toilet ɗin amma na kasa, Ummu Salma ma da nake sakawa tana wanke masa, duk ranar da ta yi aikin ƙyanƙyaminta nake yi ko kusa da ni hana ta zuwa nake yi."

"Tsakani da Allah ko nawa za a ba ni ba zan iya zama da Mukhtar ba!" Umma ta faɗa tana buɗe window ta furzar da yawu tana yatsina fuska. Dariya ta suɓuce mini na ce,
"Ai yanzu ya daina, yana wanke kayansa amma fa wallahi ba koyaushe yake flooshing ba. Saboda ɗabi'ar ta bi jikinsa ba ya iya aikin komai sai ci da kwanciya. Amma shara ma idan ba an yi sa'a ya bar ɗakinsa a buɗe mun share masa ba; sai ya fi ƙarfin wata ɗaya har biyu bai nemi a gyara masa ko ya gyara da kansa ba. Amma babu laifi sharar ma yanzu yana yi da kansa idan ya gaji da zama cikin datti."

"Wannan kuma kin fi shi laifi gaskiya! Don ke ya dace a ce kullum kina share masa É—akin, ko da ba za ki yi hidimar kashinsa ba!" Umma ta faÉ—a tana haÉ—e fuska, sannan ta fitar da hanjin gadon waje ta dawo. Cikin sanyin jiki na ce da ita,
"Ai ke Umma a baya yana barin É—akin buÉ—e ya tafiyarsa, amma yanzu kullum rufewa yake yi sai an ci sa'a yake barin shi buÉ—e ya fita. Ko na ce ya ba da makulli a buÉ—e É—akin a share masa, sai ya ce a bar masa kayansa haka nan sai ya tashi."
"To wannan kam daga ke har shi kuna da laifi! Tun da ba makulli ɗaya ba ne sai ki zari wani ki ɓoye. Duk lokacin da ya fita sai ki buɗe ki share masa ɗakin ki mayar ki rufe. Saboda irin Mukhtar ko haƙƙin kansa ma ba ya iya saukewa balle na abokin zamansa. Don wallahi a yadda yaken nan ko dabba aka ba shi kiwo sai ta mutu bai san ta mutu na, saboda rashin kulawa balle ɗan mutum mai buƙatu da yawa. Allah dai ya sauya miki da alheri, amma shi kam ba mijin aure ba ne ga duk macen da ta san ciwon kanta."

Ta ƙare maganar tana goge gumin fuskarta, Inna Kulu ta yi tsaki sannan ta ce, "Ni fa tun inda lamarinsa ya fara ba ni tsoro; da na ji ta ce duk inda za ta je a faɗin garin nan don ta daɗe ba zai neme ta ba. Haka ma idan ta dawo ba zai tambaya ya ji lafiya ba, wannan ai ba aure ba ne kuma rashin sanin ciwon kai ne kawai wallahi. Na ga ni nan tsohuwa ce ba yarinya ba, amma idan fita ta kama ni Sale ya dingà shimfiɗa mini dokoki kenan. Idan ma na yi fitar waya bisa waya a kan na dawo, hankalinsa ba zai kwanta ba har sai ya ga na dawo gidan nan na zauna."

Umma ta riga ni faɗar maganar da nake ƙoƙarin fitarwa a bakina, ta yi hanzarin cewa da ita,
"To ai shi Salenmu na daban ne kowa ma ya sani wallahi."
Inna Kulu tana dariya ta ce,
"Daman can aikinku kenan kuri da nuna kun fi kowa iya zaman aure!"
"Kin dai ga zahiri don ke ma kin san ba kowane namiji ne irin Salenmu ba!"
Umma ta faɗa kanta tsaye, Inna Kulu ta riƙe baki tana kallon ta murmushi a kan fuskarta bakinta ya ƙi rufuwa, saboda ta san gaskiya ce Umma ta faɗa. Don ni kaina rayuwar Kawu Sale tana burge ni matuƙa, musamman da bai haɗa komai da Inna Kulu ba. A gaban kowa yana iya nuna mata ƙauna da kulawa babu ruwansa da sun tsufa, ko 'ya'ya da jikoki ba za su saka shi jin nauyin ɗaura mata ɗankwali ba, ko kuma ya kakkaɓe mata ƙurar hayaƙi a saman kai idan ya ga ta ɓata mata jiki. Nama ma idan ya siyo wani lokaci idan ya ɗauki yanka ɗaya kafin a raba ya ci, to ita ma sai ya ɗauki ɗaya ya kai mata a baki, mu yi ta dariya.
Zancen Inna Kulun ne ya katse mini tunanin rayuwar aurensu mai É—auke da kulawa tare da fahimtar juna.

"Tabbas! Sale mutum ne, don ko ina zan iya bugun ƙirji na ce na yi sa'ar aure. Don duk macen da mijinta bai damu da yawan fitar da take yi ba; gaskiya yana da rangwamen ƙaunarta. Saboda ke kanki macen da kike tambayar fitar kullum yana barin ki babu musu, wallahi watarana sai kin ji wani iri, matuƙar kin san kanki."

Dariya na fashe da ita ina faɗin, "Zancenki haka yake Inna! Saboda ni kaina haushi nake ji a lokacin da nake tambayarsa fita. Wani lokaci ma ba ya bari na kai ƙarshen zancen balle na faɗi abin da zai kai ni; yake cewa da ni sai kin dawo. Watarana ma idan na ji haushi na ce, wai kai ba za ka ce da ni ban zuwa ba, kullum da na faɗa ko bakina ba na rufewa kake cewa sai na dawo. Sai ya ce idan tafiyar ce ba na so na yi zamana kawai, ya fita ya bar ni cike da mamakin murɗaɗɗen halinsa."
"Ai duk macen da ke tambayar fita koyaushe a ce mata tafi, ba ta yi sa'a ba. Gara a dingà nuna miki iko da isa a wasu lokutan. Ta hakan kike gane an damu da ke, kuma ana kishinki."

Shiru kawai na yi a kitchen bayan na gama saka kulolina a buhuhuwa, ina nazarin maganganun Inna Kulu masu É—auke da zallar gaskiya. Musamman da na tuno faÉ—an da na ji MD yana yi wa matarsa a waya, a kan yawan fitar da take yi tare da kashedin kada ya dawo ya iske ba ta gidan.

'Kenan dai shi ma yana son matarsa?'

Tambayar da na yi wa kaina kenan, kafin na É—ora Umma ta shigo kitchen É—in ta sa masu É—aukar kayan suka É—auki buhuhuwan. Kallo na ta yi cike da sakin fuska ta ce,
"Sai me kuma ya rage? Duk an fitar da kayan waje har an je kai wasu a dawo."
Murmushin yaƙe na yi, wanda iyakacin shi kan fuskata, sannan na dudduba drowowin babu komai nawa sai na Barira da na bar mata. Na ce da ita,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.