Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 72 of 86

Dam-dam! Shi ne bugun da ƙirjina ya yi, musamman sakin da na ji ta ambata, da kuma yarana da suka faɗo mini a rai.

"A kan me kike so a sake ta?"

"Saboda zaluncin da yake yi mata tsawon zaman da suka yi ba ta mori komai ba sai ƙunci. Domin tun da ta aure shi shekara goma sha uku har yanzu ba ta ji daɗin auren shi ba, balle ta yi farinciki da zama da shi."

Shiru mutumin ya yi na É—an lokaci bai ce komai ba, sai daga baya ya nemo wani sabon file ya fara rubutu. Sunanta ya nema da sunana har da na Mukhtar duka, sannan ya tambayi yaranmu nawa duka ta faÉ—a masa.
Bayan ya ƙare rubutun ya sake cire gilashin idonsa ya ce,
"Kotu kike so a tura ku a yi shari'a? Ko kuma sulhu kuke so a yi bayan fage ba tare da kowa ya sani ba?"

"A shiga kotun kawai!"

Zancen da na yi kenan cikin sauri ba tare da na jira na ji cewar Umma da hukuncinta ba. Saboda yadda nake jin tsanarsa ta linku sosai a kan sace mini yarana da ya yi, domin tun da na ji Umma ta faÉ—i ya sace su zuciyata ta gamsu da shi ne ya É—auke su.
Duba da yadda suka yi a lokacin da ta je É—auko mini kaya ita da Sajida, domin ya ce ba zai sake ni ba sai an ba shi yaransa.

'Waton suna wurin Barira?'

Tambayar da na yi kenan, kafin na tsinkayo muryar Umma tana faɗin, "Ba sai an shiga kotu ba! Ko iya sulhun aka yi ya wadatar. Matuƙar zai sake ta, kuma zai bar ta da yaranta."

Rubutu mutumin ya sake yi sannan ya ce da Umma, ta faÉ—i sunan unguwar da yake za a tura masa takardar sammaci.

"Runjin Sambo, kusa da layin gidan Hassan ÆŠangote!"

Bayani ta yi tiryan-tiryan aka rubuta a jikin takarda, sannan aka tayar da manzo takanas a kan ya zo tare da yaran ana buƙatar ganin shi. Sannan mutumin ya miƙe ya ce mu jira shi ya sanar wa Ogansa, ya fice bayan ya rufo ƙofa na sauke ƙatuwar ajiyar zuciya.

Umma ta É—ora kallonta a kaina tana faÉ—in, "Duk abin da kika sani ki faÉ—a, tun daga farkon aurenku har zuwa yanzu."
Kai na ɗaga mata ba tare da na iya furta ko kalma ɗaya ba, har mutumin ya dawo ya ce da mu mu biyo shi. Yana gaba muna bayansa har wani babban ofishi, wanda tun da muka jefa ƙafafuwanmu sanyin A.c ya fara bugar mana fuska.
Wani kamilin farin tsoho na gani a kan kujera, fuskarsa a sake saɓanin wanda muka fara gani. Wuri ya nuna mana muka zauna, sannan ya sallami wanda ya kawo mu a kan ya tafi idan Mukhtar ya zo a kai shi ɗakin sulhu.

Idonsa ƙur a kanmu ni da Umma sannan ya ce, "Me ke faruwa tsakaninki da mijin naki?"

Zama na gyara sannan na fara zayyano masa tun farkon aurenmu har zuwa lokacin da ya sayar mini da kayan É—aki. A nan ya ce na tsaya ya ci gaba da rubuce-rubuce a jikin wasu takardu sannan ya ce na É—ora, bayan an gabatar mana da lemu mai sanyi ni da Umma da ruwan gora guda biyu.

Bayani tiryan-tiryan na shiga yi ko waƙafi babu balle aya, har na gangaro inda ya sa aka zubar mini da cikina. A nan ma dakatar da ni ya yi bayan ya rintse idonsa yana jijjiga kai. Shiru ya ratsa tsakani sai ga sallamar mutumin da ya kawo mu ya dawo, bayani ya yi masa a kan ga Mukhtar can a ɗakin sulhu tare da yaran duka.

Zumbur na miƙe tun kafin a ba ni umurni na nemi ƙofar ficewa, farin dattijon ya ce,

"Ina za ki je?"

Kunya ta kama ni a lokacin da na yi ido biyu da Ummata, saboda kallon da take yi mini ya sa na ji kaina ya zama ƙatoto. Dawowa na yi na zauna sai da dajjiton ya ba mu umrnin mu je can kafin ya zo sannan muka fice ni da Umma.
ÆŠakin sulhun babba ne mai É—auke da kujerun roba farare za su kai guda ashirin. Tun daga nesa na hango su Umma Salma makure tamkar a ce 'kyat' su arce da gudu.
Suna hango mu suka zo da gudu suka rungume ni dukansu suna kuka. Tsabar tausayinsu ya sa na fara kukan ina dudduba fuskokinsu ina share musu ruwan hawaye. Umma Salma ta sake ni ta yi wurin Umma ta fashe da kuka. Saboda ni kaina na hango hawayen da Ummata take sharewa da gefen hijabinta. Hakan ya sa ta nemi kujera ta zauna ba tare da ta ce ƙanzil ba.

Ta gefen ido na saci kallon Mukhtar zaune a kan kujera fuskarsa a haÉ—e yana kallon bangon É—akin. Yarana na ja muka yi kan kujeru muka zauna ina ci gaba da rarrashinsu a kan su daina kukan da suke yi.

Mun É—auki minti goma kafin farin dattijon ya shigo, tare da wasu da ke take masa baya, cikinsu har da mutumin da ya kai mu wurinsa.
Zama ya yi a kan kujerar da ke fuskantarmu ya yi gyaran murya sannan ya ce,

"Mukhtar Sa'adu mai shadda!"

Sunan da farin dattijon ya faɗa kenan da ƙarfi, wanda na gama tantance shi ne alƙalin babbar kotun. Mukhtar ya fara zarar ido tare da faɗin,

"Na!am! Ranka ya daÉ—e!"

"Me ke tsakaninka da matarka, kuma uwar 'ya'yanka, mai suna Zaituna Aliyu?"

Fiki-fiki ya fara yi da ido sannan ya ce, "Wallahi ranka ya daÉ—e, duk matsalolin da ke faruwa ita ce take janyo su."

"Matsaloli! Kamar me da me!?"

Alƙalin ya sake jefo masa wata tambayar cikin ɗaga murya. Mukhtar ya fara rawar murya yana cewa,
"Ita da ƙawarta suka haɗa kai suka yi wa matata ɗan banzan duka har suka tsige mata kitson da ke kanta. Yanzu haka sai da aka yi mata allurai na fito bayan an sake wanke raunin da suka yi mata."

"Idan waccan ta gida ka kira ta da matarka; ita wannan da ke zaune tare da yaranka miye matsayinta a wurinka?"

Tambayar alƙali kenan ga Mukhtar cikin sigar sargafo masa wuya da igiya, ba tare da ya hankalta ba.
"Eee to! Ita ma matata ce! Duk da kullum tana faÉ—ar ita ba matata ce ba!"

"Mace tana saki ne?"

"A'a ranka shi daɗe! Amma ita tuni tana iƙirarin babu aurena a saman kanta."

"Saboda me?"

"Saboda shekara huÉ—u ba tare da ya haÉ—a shimfiÉ—arsa da ni ba!"

Amsar da na cafke kenan ba tare da na jira Mukhtar ya amsa ba. Kafin ya furzo na shi kalaman da ke ƙoƙarin kore maganata da gangan.

"Ko na neme ta, ba ta yarda da ni ranka ya daÉ—e tsawon shekaru!"

"Ƙarya kake yi baƙin munafuki! Kuma ƙaryarka ta gama shan ƙarya!"

Zancen Ummata kenan, bayan ta yi kukan kura ta cafko wuyan shi. Duka ta shiga kai masa tana ƙarajin faɗin ƙarya yake yi. Da ƙyar aka raba ta da shi bayan ta kai shi ƙasa ta danne wuyan shi da kujerar robar.
Tarin wahala ya dinga yi yana jujjuya wuya bayan an taɓe shi a hannun Umma, ita kuma sai surutai take yi cikin wani yaren da ban taɓa ji ba, daga baya kuma ta dawo fillanci bakinta yana kumfa.
Kasancewar shi ma alƙalin bafulatani ne, tare da shi suka yi ta maganganun da ban san me suke faɗa da fulatanci ba. Don iya sani na ita kanta Ummata ba ta iya yaren ba, amma zar-zar take ta zubo shi ko nunfasawa babu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.