Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 76 of 86
"Kishi masifa ne kam! Amma wani kishin ya wuce haddin musulunci. Haka kawai ka cinna wa kishiya da mijinka wuta saboda tsabar hauka?"
"Ba ta san halin maza ba ne shi ya sa! Duk kishin da zai sa a salwantar da rayuwaka rashin imani ya shiga ciki ya zauna. Haka fa na taɓa ganin wani labari da daɗewa a tashar talabijin ta RTV Sokoto, kuma na ji an maimata shi a gidan Radio BISHIM FM ana hira da wanda abin ya faru da shi. Wata ce ta cinna wa mijinta wuta, tare da yaronta da ke kwance kusa da shi yana barci, don kawai zai yi mata kishiya. Da ƙyar ya samu ƙofar tsira ya diro ta taga tun daga saman bene ya karairaye. Wutar ta canye yaron ƙurmus kuma bayan ya gama jinya ya yi aurensa, ita kuma ya sake ta. Yanzu wannan wa gari ya waya?"
"Ita!"
Na ba ta amsa a gajarce saboda sanyin da jikina ya yi, Inna Kulu ta ƙara da cewa,
"Kuma idan ba Allah ya tsare ba, ita da aure a nan duniya sun yi hannun riga. Saboda duk wanda ya ji tarihinta ba zai taɓa auren ta ba, don ko an so yin jahadi dangin mutum ba za su bari a auro musu annoba ba."
Jiniyar motar 'yansanda da muka jiyo ta karaÉ—e unguwar, hakan ya sa muka yi shiru dukanmu muna sauraro. Sai ga Kawu Sale kamar an jefo shi ya faÉ—o gidan yana gyara zaman babbar rigarsa yana faÉ—in,
"Ke duniya ina za ki da mu?"
"Lafiya!?" Tambayar da muka yi masa kenan, buta ya ja da gudu ya faɗa bayi. Dukanmu muka bi shi da kallo, kafin mu ji dirin mota a ƙofar gida, ana rafka mana sallama. Cikin tashin hankali Umma ta zari Hijabi ta yi waje ni ma na bi bayanta da sassarfa ƙirjina yana bugawa.
Ganin 'yansanda reras a ƙofar gidan, hakan ya sa na gwalalo ido waje cike da matsanancin tsoro. Bayanin da na ji wani ɗan sandan yana yi wa Umma; ya sa hantar cikina kaɗawa, 'yan hanjina suka murɗa na koma cikin gidan da gudu. Hannuna a kai ina salati, wanda sai na kamo shi ya kufce na ƙara janyo wani.
Jikina yana rawa na fara tura wa MD gajeren saƙon da bai fi layi ɗaya da rabi ba. Saboda shi kaɗai ne mutumin da ya faɗo mini a rai a daidai lokacin, kuma shi nake da cikakken tabbaci a kan zai fitar da ni matsin rayuwa duk rintsi.
Umma ta shigo gidan cikin matsanancin tashin hankali bakinta yana rawa ta ce da ni,
"Shirya mu je da kaina zan kai ki. Babu wata motar 'yansanda da za ki shiga, don ba kisan kai, ko sata kika yi ba."
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"
Ita ce kalmar da muka haɗa baki wurin faɗa daga ni har Inna Kulu da Kawu Sale da ke ƙoƙarin fitowa bayi.
"To mu tafi gabaɗayanmu a rufe mu ɗan makulli ya ɓace."
Zancensa kenan sannan ya yi gaba cikin ƙunar zuciya muka bi bayansa ni da Umma. Duk da matsanancin tsoron da nake ciki, amma hakan bai hana ni bin Umma ba cikin sauri 'yan sandan suka bi mu da motarsu.
Adaidaitasahu muka shiga mu duka uku, tare da wani ɗan sanda a gaban da mai adaidaitasahun. Ƙirjina ya hau bugawa fal-fal tamkar zuciyata ta ɓalle ta fito waje. Babu wanda ya ce komai har aka kai matattarar 'yansanda da ke polo.
Yaya Maimuna na fara hangowa sai wasu daga cikin danginsu maza. Fuskata na cure saboda jikina ya ba ni da wuya a kwashe ta daÉ—i, musamman ganin fuskokinsu babu alamun rahama balle sassauci.
Ankwa aka saka mini ina kuka Ummata tana yaɓa wa su Yaya Maimuna maganganu masu zafi, tare da kira musu Allah ya isa ta fi cikon kwando Kawu Sale yana tausar ta.
Gaba wani ɗansanda ya saka ni Ummata ta riƙe ni tana faɗin, "Babu inda za a je mini da yarinya, a tsaya gaban kowa a yi magana idan abin ya ƙi a tura mu babbar kotun ƙoli, don daman can case ɗinmu yana hannunsu."
Wani ɗan sanda na ga ya yi wa wani ƙus-ƙus sannan aka zare mini ankwa suka ce mu shiga daga ciki. Dogon benci muka zazzauna yayin da wasu suka zauna ƙasa. Babban jami'in da muka taras kan kujera shi ya fara yin magana, bayan ya kira Yaya Maimuna a kan ta ƙara yin bayanin abin da ya kawo su wurinsu.
"Haƙƙin ɗan'uwanmu muke nema a bi mana ranka ya daɗe. Saboda har asibiti ta je a gaban kowa ta kai masa harbi da ƙafarta. Kuma tun da ya faɗi ƙasa har yanzu bai tashi ba yana can gadon asibitin, ana ta ƙoƙarin shawo kan matsalar da ta haifar masa amma abin ya ci tura."
"Waiii! Sannu Zita azurari uwar zuba! To ba gadon asibiti ba ko cikin ƙabari ne; Mukhtar ya cancanci fiye da haka a hannun Zaituna."
Zancen Umma kenan kafin wani jami'in tsaron ya katsa mata tsawa, a kan ta yi shiru kada ta sake magana har sai an ba ta umurni. Umma ta yi muƙus tana harare-harare bakinta yana mui-mui.
"To yanzu dai kun ji abin da suke nema a yi musu. Don haka za mu ajiye ta a nan, har sai an yanke mata hukuncin da ya dace da ita, sannan ku dawo mu san yadda za a shawo kan lamarin."
"Tsakani da Allah ranka ya daɗe ba a yi wa yarinyar nan adalci ba! Mun ji ta yi masa ba daidai ba. Amma bai dace a ce za a riƙe ta a nan ba, don wannan rigima ta cikin gida ce bai dace a ja ta da tsauri haka ba. Saboda faɗa ne tsakanin mata da miji kuma kowa ya sani ana samun matsala."
"Za ka koya mana yadda ake aiki ne!?"
Wani É—ansanda ya yi wa Kawu Sale magana cikin É—aga murya, shi ma ya ba da amsa cikin kwantar da kai ya ce,
"Ba haka ba ne ranka ya daÉ—e! Amma dai don Allah a duba lamarin da kyau yarinyar marainiya ce!"
"Mu ma dukanmu nan marayu ne... Kofur Musa!"
"Yes ser!"
"Kai ta É—akin ajiya, idan kuka shirya sai ku dawo a yi magana."
Zumbur Umma ta miƙe tare da riƙe ni tana faɗin,
"Don girman Allah ranku ya daÉ—e kada ku rufe mini yarinya. Wallahi shi ya janyo ta yi masa abin da ta yi, don kowa ya san babu ruwanta shi ne da matsala."
"Idan ma kowa ya sani mu ba mu sani ba! Kofur Musa je da ita kawai."
Umma ta ƙara damƙe ni ina ta kuka na ƙanƙame ta, wanda aka kira kofur Musa ya zo zai taɓa ni Umma ta buge masa hannu tana faɗin,
"Wallahi sai dai a kashe mu daga ni har ita! Amma ba zan bari ku rufe mini yarinya ba!"
Wata 'yarsanda mace aka kira ta saka kulki ta fara dukan hannun Umma, amma ta kasa raba ni da ita kamar yadda take so. Ana tsaka da haka wani jami'in ya shigo ya sara wa babban jami'in ya ƙame, sannan ya yi masa ƙus-ƙus suka fice ofishin tare. Bayan ya ce da 'yar sandar ta dakatar da dukan da take yi wa Umma, a ƙoƙarinta na son ta ɓanɓare ni daga jikinta ta ƙarfi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.