Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 84 of 86
"Tun da na aure shi, idan aka cire farkon aurenmu da yake nema na sosai. Yana kwashe wata biyu, uku, har zuwa biyar, shida bai neme ni ba. Idan ma ni na neme shi kai-tsaye yake nuna mini bacci yake ji. Wani lokaci kuma idan ana sanyi, yana cewa da ni asuba yake son tashi kuma ba ya son yin wanka sanyi yake ji. Tun ina neman haƙƙina a wurinsa yana hana ni, har ta kai idan na matsa masa ya yi mini kamar an yi masa dole. Yana ɓata fuska yake haiƙe mini babu wani ɗan saƙo, sannan minti biyu ya yi masa yawa ya zubar da ruwansa ya bar ni haka nan! Na sha kuka a kan wannan matsalar a ɓoye ba tare da ya sani ba, da na ga bai damu da damuwata ba na fito fili na sanar da shi ya nemi magani. Saboda na fara gundura da halinsa kuma shi ya ƙi ya gano matsalar domin ya gyara. Idan na yi masa zancen neman magani sai ya ce da ni, ai duk namijin da ya saba da amfani da maganin maza; to kullum ba ya iya komai sai ya yi aiki da shi zai moru. Zancen da yake yi mini kenan koyaushe, da ya ga na matsa masa, a kan dole ya nemo magani islamic center don na gaji; Sai ya je ya nemo maganin amma ko ya yi amfani da shi babu wani canjin da ake samu. A ƙarshe ma sai ya bijiro mini da zancen an ce asiri ne wani mai sona ya yi masa. Saboda ya hana mu zaman lafiyar aure, a cewarsa. Bayan kuma ya sha sanar da ni abin da yake yi yana gusar da sha'awarsa ba tare da ya neme ni ba. A ƙoƙarin shi na kare kansa daga neman matan da nake zarginsa da shi, saboda ganin rashin kulawar da yake yi wa haƙƙin auratayy..ar..mu."
Numfasawa na yi, saboda muryata da ta fara rawa alamun damuwa ƙarara a cikinta. Ɗakin ya yi tsit ban da ƙarar fankokin da ke kaɗawa a cikin ɗakin babu mai motsin kirki. Kallona na kai gefen da Mukhtar yake tare da su Yaya Maimuna, na hango shi yana goge gumi da gefen rigarsa. Da abin da ya kai masa maƙura ya cire hular kansa yana fifita.
"Me ya sanar da ke yana yi? Wanda ke gusar masa da sha'awarsa ba ya neman haƙƙinki da ke wurinsa?"
Ajiyar zuciya na sauke, sannan na furzar da iska mai sauti a bakina na ce,
"Amfani yake yi da hannunsa domin ya gamsar da kansa, a taƙaice dai Istimna'i a Musulunce. Dalilin da ya sa ba ya nema na kenan duk tsawon watannin da za mu ja ba ma tare, tun abin yana damuna na shige toilet na yi kuka a ɓoye, na dawo yi a gabansa ba ya bi ta kai, har ya ƙone mini zuciya na tattara shi duka na watsar. Saboda ganin kukana ba ya damunsa, na fara neman saki a wurinsa ba tare da kowa ya sani ba. Saboda wata magana da ya taɓa faɗa mini muna tsaka da hira watarana, inda ya sanar da ni shi da za a zare masa aure a rayuwarsa, da ya ji daɗi. Saboda zai iya tsare kansa ba tare da ya zauna da mace ba. Hakan ya tunzura ni na ga ni zaman me nake yi da shi. Na fitittike masa sosai a kan dole sai ya sake ni, amma ya rufe idonsa ruf! A kan shi ba zai iya sakina ba sai dai na yi haƙuri. Na rufe maganar ban taɓa faɗa wa kowa ba, saboda ba na so na zubar masa da mutunci a idon mutane. Duk da ni kullum burinsa kenan ya yi mini ƙazafi da sharri, saboda ganin ina raba dare ina chartting da mutane kafin na fara zuwa aiki. Allah ya sani ban da saurayi ko wata macen banza da nake hira da ita a waya. Amma akwai wasu groups da ake hira har biyun dare ba a yi bacci ba. A can nake biye matan group ɗin ana hira har dare ya raba, wadda duk rabin hirar a kan topic ne idan admins ɗin group sun turo a bai wa juna shawara. Sosai group ɗin yake ɗauke mini kewar rashin Mukhtar, sannan na yi sabo da mutanen sosai. Idan ba a gan ni ba har nema na ake yi a waya. To ire-iren hakan ne idan sun kira ni a waya cikin daren, ko kuma ya gan ni ina chatt ɗin ya ce da maza nake yi. Na sha faɗa masa, da a ce yana ba ni lokacinsa ya sauke haƙƙina da ke wuyansa, da na daina chatt ɗin dare gabaɗaya na ba shi lokacina, domin mu faranta wa juna. Amma shi zai kwashe lokaci mai tsawo a waje bai dawo gidan ba, wani lokaci har sha biyu da rabi na dare, ko ɗaya saura duka yana kaiwa waje bai dawo ba. Amma yanzu Alhmdulillah! Tun da na fara zuwa aiki na daina hira group ɗin, asali ma ba na samun damar chatt kamar yadda nake yi a can baya. Saboda haka don Allah ina so ya sauwaƙe mini, domin ina jin tsoron na faɗa muguwar rayuwa a sanadin aurensa!"
"Bayan ƙaton da kike tare da shi kuna sheƙe ayarku a wurin aikin, har wata muguwar rayuwa kike gudun faɗawa cikinta saboda aurena? Wallahi Allah sai ya saka mini a kan duk ƙazafin da kika yi mini don kawai kina so na sake ki!"
"Dakata Malam Mukhtar!"
Zancen Alƙalin kenan bayan maganarsa. Ya yi shiru yana aika mini harara tamkar idonsa su faɗo, bayan ya yi ƙwafa mai ƙara wadda ke nuna zallar ɓacin ran da yake ciki.
"Shin ka yarda da zancen da ta yi a kan Istimna'in da ta ce kana yi?"
Alƙalin ya jefo masa tambayar da ta so gigice shi, domin kuwa miƙewa ya yi taku ɗaya biyu kamar zai bar wurin, sannan ya koma kujerar da yake kai ya zauna yana zarar ido.
"Ƙarya take yi mini ranka ya daɗe!"
"To idan haka ne! Za mu ba ku ƙur'ani dukanku ku yi rantsuwa da shi, saboda ka ce tana zina, ita kuma ta ce ba taɓa yi ba. Shin ka yarda ka amince za ka rantse da alƙur'ani, domin ka kare kanka da duk abin da ta faɗa a kanka, wanda ba ka gamsu da su ba duka?"
Turka-turka! Ku hasko mana idon MukhtarðŸ¤
D. AUTA CEâœðŸ¼
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*ARBA'IN DA BAKWAI.*
*Book 1 ending.*
"Rantsuwa da Al'ƙur'ani kuma!?"
Tambayar da ya yi wa Alƙalin kenan yana zarar ido, tare da miƙewa tsaye dafe da ƙirjinsa. Alƙalin bai yi magana ba illa ɗaga masa kan da ya yi alamun tabbatarwa. Sannan ya gyara zamansa ya ce da shi,
"Kwantar da hankalinka ka zauna!"
Mukhtar ya koma kan kujerar da yake kai ya zauna. Alƙalin ya ɗan muskuta bayan ya yi gyaran murya ya ce,
"Abin da ya sa ka ji an sako zancen rantsuwar! Saboda ka ce ƙarya ce take faɗa a kanka ba gaskiya ba. Amma idan ka gamsu da bayananta dole a jingine rantsuwar gefe. Daman ita ana yin ta ne kawai saboda a kore shakku, ko kuma kokwanton da ake yi a kan wani abu a yayin Shari'a. Don haka idan ka yi rantsuwar shi kenan za mu gamsu da zancenka. Ita kuma za mu ƙaryata zancen da ta yi a matsayin sharri ko ƙazafi, matuƙar ita ma ba ta karɓi rantsuwar ba."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.