Abokin Aikina Complete Hausa Novel
Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 5 of 86
Rashin wayata da rashin jin motsin yarana kusa da ni, ya haifar mini da wata sabuwar damuwar da ta janyo mini Zazzaɓi. Nan take na fara jin sanyi na nemo paracetamol, ƙwara biyu na afa na dunƙule ina rawar sanyi. Cikin ikon Allah mintuna a tsakani na fara jiɓi a daidai lokacin da na fara jin ihun murnar yarana, wanda hakan yake tabbar mini da alamun sun dawo. Farinciki fal raina na fara ƙoƙarin saukowa daga kan gadon da nufin tarbon su. Sai ga su sun shigo da gudu sun rungume ni suna faɗin "Oyoyo Mama" tsananin daɗi ya sa na maƙalƙale su duka su ukun ina faɗin "Sannun ku da zuwa". Ummu Salma babbar 'yata ta taɓa wuyana ta ce "Mama jikinki da zafi har yanzu ciwon kan kike ji?" Hawayen kuka ya zo mini na yi ƙoƙarin mayar da su ina faɗin "Ai na ji sauƙi, amma gobe zan je asibiti a duba ni..." "Mama duk na girma na zama babba, sai na gina miki ƙatuwar asibiti a cire miki ciwon kan nan ki huta" Abin da Haidar ya faɗa kenan yana share mini hawayen da ban san lokacin da suka zubo kan fuskata ba. Iman na kalla wadda ta yi tagumi tun da suka shigo ba ta ce komai ba tana kallona. Sanyin halinta da na sani ya sa na dafa kanta cikin ƙaunar uwa zuwa 'yarta na ce "Ke kuma me za ki yi mini idan kika girma". Sai da ta share hawayenta sannan ta ce "Zan saka ki farinciki ki daina kuka ba na son ganin hawsyenki..." Kukan da ta fashe da shi ya sa ni ma nawa ya ƙara ambaliya. Hannunta na riƙo cike da jarumta na goge hawayen da ke ta sauko mini kan fuska na ce "Ki daina kuka kin manta za ki zamo likitaa!?" Na ja kalmar ƙarshe cike da jan zaren wasa domin na tsayar da kukanta. Kai ta ɗaga mini alamun "e" Ina murmushin ƙarfin hali na ce "To ai da kin yi mini allura cikin baki shi kenan ruwan hawayen zai ɗauke" cikin sauri ta rufe bakinta tana dariya ta ce "A baki kuma..?" Kafin na ba ta amsa Haidar ya ce "Ai Mama har cikin ido ana allura ko?" Tambayar shi ta ba ni dariya na ce "Har cikin kunne ma.." Gabaɗaya daga ni har su muka fashe da dariya. Cikin dariyar na kalli Ummu Salma na ce "Ki je ki dafa muku Indomie.." "Umma fa ta ba da abinci a kawo muku ke da Abbanmu. Mu ma ta ba mu namu ta ce mu zo da shi mu ci a nan" Annurin fuskata ya ɗauke a dalilin Abbansu da na ji ta ambata, saboda har ga Allah ba na son maganar Mukhtar da duk abin da ya shafe shi, har cikin zuciyata.
Haɗe fuska na yi na ce "Oya ku je ku yi shirin sallar magrib ga ta can an fara kira. Kai kuma Haidar ka wuce masallaci kada ka bari a fara sallah ba ka fita gidan nan ba" Suka fice ɗakin cikin sauri na sauke ajiyar zuciya. Raina a jagule na sauko gadon na fito falo, kulolin Ummata da na hango saman table ɗin tsakiyar falona. Hakan ya sa na isa da sassarfa na fara buɗe babbar kulolin da ke gabana. Tuwon masara ne da miyar ganye sai ƙamshin man shanu ke tashi. Sai ɗaya kular da na buɗe na hango ɗanwake maƙil a ciki da man ja a leda tare da yajinsu a leda. Hakan ya tabbatar mini tuwon ne namu su ne da ɗanwake. Wuri na samu na zauna cikin tagumi ina nazarin har yaushe Umma za ta dawo daga rakiyar Mukhtar, duk da abin da yake yi mini ita har kullum girmansa take gani a idonta. 'Shin ta ya ya zan fahimtar da Umma illar ɗaure wa Mukhtar ƙugun da take yi? Kuma har zuwa yaushe zan fita daga wannan ƙangin rayuwar da nake ciki?'
Hmmmm!😰
D. AUTA CEâœðŸ¼
D. AUTA CE🫰ðŸ»
*ABOKIN AIKINA*
*@HADIZA D. AUTA*
*SADAUKARWA: DAUGHTER ANUP*
*LAMBA TA BIYAR.*
Hawayen da suka gangaro mini na share, sannan na miƙe na yi ɗaki domin na yi sallah. Na daɗe kan sallaya ina addu'o'in waraka daga halin da nake ciki. Shigowar yaran ya sa na ɗaga kai ina kallon su, rige-rigen gaishe ni suke yi ina amsawa cikin sakin fuska, Ummu Salma ta ajiye abincin da ta zubo mini shaƙe da plate. Sai da na yi murmushi sannan na ce "Wannan abinci ina zan kai shi ni kaɗai...?"
"Ki ci ki ƙoshi Mama. Umma ta ce mu dinga saka ki kina cin abinci mai yawa, kuma mu dinga ba ki haƙuri kada mu bari ki yi kuka".
Abin da Haidar ya faɗa kenan tare da ɗebo tuwon yana ƙoƙarin kai mini lomar a bakina. Baki na buɗe ya saka mini murmushi ɗauke a kan fuskar shi yana jin daɗi. Ganin hakan ya sa dukansu suka dinga ɗebo tuwon suna ba ni, ban hana su ba kuma ban ƙi karɓa ba. Sai da na fara jin amai sannan na dakatar su. Ruwa Ummu Salma ta kawo mini na Sha, cike da jin daɗi har cikin raina na yi musu godiya kuma na saka musu albarka.
Na ba su umurnin canye sauran tuwon sannan na ce da su mu je falo, a can ma tare muka ci É—an waken kuma sosai na ji daÉ—in shi a bakina.
***
Daren ranar na yi bacci sosai kuma na ji sauƙi dangane da ciwon kan da ya addabe ni. Mukhtar kuma bai dawo gidan ba sai sha biyu da rabi, kamar yadda ya saba yin daren shi a waje koyaushe. Ina jin lokacin da yake rufe gida tare da rufewar ɗakin shi, ajiyar zuciya na sauke a raina na ce,
'Ni kam dai ba ni da bambanci da bazawara. Wai me ya sa wasu mazan suke kasa gane abin da mata suka fi so a wurinsu? Shin ta ya ya mace za ta ji daÉ—in kyautata wa mijinta bayan shi ba ita ce a gaban shi ba..?'
Katsar da marata ta yi na yi hanzarin dafe wurin ina faÉ—in,
"Wash! Allah!"
Gumi ya fara karyo mini saboda kartar da marar take yi mini, bayan ta dunƙule wuri ɗaya tana zugi. Saboda wani feeling da nake ji wanda nake da tabbacin sha'awa ce ta janyo mini ciwon marar. Na jima cikin halin kafin ta lafa bayan na samar wa kaina waraka, ta hanyar da na saba a duk lokacin da na shiga irin wannan halin. Kuka na fashe da shi cike da ƙyamar abin da nake yi, wanda nake jin takaicin abin a raina amma kuma na kasa dainawa.
Saboda ganin ba ni da wata mafita mai sauƙi idan ba ta wannan hanyar ba. Duk da na san hakan laifi ne kuma illa ne gare ni ga lafiyata, amma na zaɓi bai wa kaina natsuwa ta wannan hanyar domin ba zan iya aikata zina ba, haka ma ba zan iya zuwa wurin Mukhtar ba. Sanin ko na je babu abin da zai iya tsinana mini balle ya warkar mini da ciwon, illa ya ƙara mini damuwa da takaicin da zan kwana ina tsaki tare da jin haushin kaina. Ban bari na kwana da najasa ba, na tashi na yi wankan tsarki sannan na dawo na kwanta raina a cunkushe kamar ko yaushe. Amma na yi bacci mai daɗi saboda samun natsuwar da na yi ta hanyar gamsar da kaina.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.