Complete Hausa Novels

Abokin Aikina Complete Hausa Novel

Reading file: Abokin_Aikina_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 85 of 86

"Ranka ya daÉ—e! Don Allah a bar zancen rantsuwar nan! Saboda na yi sau É—aya kuma ba na fatar Allah ya sake kama ni da laifinta."
Mukhtar ya ƙare maganar yana goge gumin fuskarsa da gefen rigarsa. Alƙalin ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce,

"Me kake zance a kansa, na ka yi sau É—aya?"

"Rantsuwar ranka ya daÉ—e!"

"To fa! Kenan dai ka gamsu da dukkan bayanan da ta yi?"

"Na gamsu da wasu, amma wasu ƙarya ce kawai take yi mini ranka ya daɗe kamar yadda na faɗa tun farko."

"Wace magana ce ƙarya? Kuma wace ce gaskiya a cikin abin da ta faɗa yanzu?"

In da-in da ya fara yi sannan ya ce, "Zancen da ta yi a kan na ce dama an cire mini aure ba gaskiya ba ne! Amma abin da ta ce ina yi wannan gaskiya ne tun ina saurayi. Saboda ba na so na faɗa sana'ar zinace-zinace, shi ya sa nake yin hakan musamman a lokutan da ta ƙi ba ni haƙƙina."

"Kenan ka tabbatar da kanka; kana yin hakan ba ƙarya ta yi maka ba?"

"Haka ne ranka ya daÉ—e!"

"To ma Sha Allah! Daman abin da nake so ka amsa kenan da bakinka. Kuma Alhamdulillah! Ka tabbatar da hakan a gaban kowa ya ji."

Shiru ya ratsa tsakani bayan maganar Alƙalin, babu wanda ya yi ko dogon motsi balle wani ya yi yunƙurin cewa wani abu. Sai da ya ja ɗan lokaci sannan ya sake magana cikin wata kalar murya ta daban, ba irin wadda ya yi wa Mukhtar tambayoyin da ita ba. Domin wannan muryar sabuwa a kame take sosai kuma harɗe, saɓanin ta farkon da yake haɗawa da murmushi yayin maganar.

"Istimna'i abu ne mai hatsari ga lafiyar mutum, sannan ƙololuwar zunubi a wurin Allah da addininmu na Musulunci. Saboda ko babu laifi a cikinsa yana haifar da matsalolin da za su zamo barazana ga lafiyar mai yin sa. Bayan ɓangaren wasu cututtukan, da kan iya zama barazanar da za ta shafi lafiyarsa da imaninsa, domin yana rage ƙarfin gani, kuma yana haifar da ƙuncin zuciya da yawan bugun ƙirji da na zuciya. Idan abin ya kama jikin mutum sosai yana haifar masa da taɓin ƙwaƙwalwa. Taɓin ƙwaƙwalwar kuma ba irin ta hauka ko doke-doke ba. A tsaye za a dinga ganin mutum lafiyayyensa amma ba ya aiki irin na masu cikakken hankali. Sannan an yi ittifaƙi a kan duk mai aikata irin wannan ɗabi'ar ta biya wa kai buƙata, musamman namiji; ba zai taɓa zaman aure da matarsa ba. Saboda zai rasa kuzarinsa na mazakutar ɗa namiji gabaɗaya, kuma zai iya komawa tamkar wani mata-maza ba tare da ya sani ba. Domin zai dinga abubuwa irin na mata, wanda idan aka yi rashin sa'a wata macen ma sai ta fi shi kuzari. Saboda ba zai iya ɗaukar lokaci yana saduwa da iyalinsa yadda ake so ba. Dalilin kuwa ya saba wasa da al'aurarsa, mintuna kaɗan ya zubar da ruwansa ya huta. Kuma shi kenan buƙatarsa ta gama biya daga hakan, saɓanin saduwar aure wadda ko ga mai kuzarin gaske sai ya yi da gaske. Domin a lokacin da maniyinsa yake gangar fita, ita kuma macen a lokacin sha'awarta take fara tashi. Shi ya sa masu dabara sai sun tabbatar da gamsuwar matansu; sannan suke zubar da ruwansu saboda gudun cutar da su, ba tare da sun sauke musu nauyin da ke rataye a kawunansu ba."

Shiru na ji Alƙalin ya yi kaina a duƙe, kunya kamar ta kashe ni. Saboda bayanin da yake yi cikin raina; ina jin ina ma ƙasa ta tsage na shige cikinta na ɓoye, saboda muguwar kunyar da ta lulluɓe ni.
Shirun da ya yi, ya bai wa kowa damar tagumi da nazartar maganganunsa. Duba da yanayin fuskokinsu da na saci kallo a fakaice É—aya bayan É—aya.

"Mukhtar ba za ka iya zaman aure da wannan baiwar Allah ba, idan ma kun ci gaba da zama; to kai ma za ka ci gaba da cutar da ita ne kamar yadda ka yi a baya. Don haka kotu za ta sauwaƙe mata, domin gudun ta faɗa halaka ta sanadin wannan ɗabi'ar da ta auri jikinka. Kai ma akwai damar gyara gare ka har yanzu tun da kana da sauran numfashi, saboda duk mai irin wannan halin, daidai yake da masu ɗabi'ar neman jinsi. Ma'ana mace ta nemi 'yar'uwarta mace ko namiji ya nemi ɗan'uwansa namiji, domin su biya wa juna buƙatunsu kuma su kawar wa da juna sha'awa. Kuma Allah da kansa ya tsine wa mai irin wannan halin har sau uku, inda masana sun ce babu wani laifi da bawa yake aikatawa na saɓo a nan doron duniya; wanda Ubangiji ya tsinewa mutum har sau uku jere da juna, sai masu aikata irin wannan ɗabi'ar. Kuma hukuncin neman jinsi ya yi kamanceceniya da biya wa kai buƙata. Wanda ake ɗaukar hannu ko wani abun da za a dinga wasa da azzakari ko farji, domin a biya wa kai buƙata ko kuma a gusar wa da juna sha'awa, ta wannan haramtacciyar hanya abin ƙyama. Saboda ɗabi'a ce irin ta dabbobi, shi kuma ɗan'adam Allah ya bambanta shi da dabba don ya mallaka masa hankalin da bai bai wa dabbobin ba."

Sai da ya numfasa, sannan ya sauke ajiyar zuciya ya sake cewa,
"Abin da kowa ya sani zina saɓon Allah ce, ya saka haramci a cikinta kuma ya ce mu nisance ta. Amma tana da sauƙi a kan wannan mummunar ɗabi'ar ta maɗigo, luwaɗi da biya wa kai buƙata. Kuma duk masu irin wannan halin, suna cikin tsinuwar Allah da mala'ikunsa koyaushe. Sannan muddin suka mutu a cikin wannan halin ba tare da sun tuba ba, to tabbas za su dawwama a cikin wutar jahanna da azaba marar yankewa."

Ƙirjina ya shiga bugawa da sauri da sauri, saboda ni ma wa'azin da tunatarwar da Alƙalin yake yi sun shafe Ni. Domin ɗabi'ar Mukhtar tuni ta yi naso a jikina, duk da ba ta zamar mini jiki kamar shi ba; amma dai Ina aikatawa lokaci bayan lokaci. Idan kuma har haka ne, ni ma ina cikin tsinuwar Allah da mala'ikunsa kamar yadda ya faɗa. Babu shiri hawaye suka dinga fareti a kan fuskata, tare da da-na-sani a kan biye wa ruɗin zuciya da kururuwar shaiɗan. Domin sun saka ni aikata abin da Allah zai yi fushi da ni, bayan kuma ya tsine mini.

Muryar Mukhtar na tsinkayo yana faÉ—in,

"Na gamsu da bayananka duka ranka ya daɗe! Kuma in Sha Allah zan gyara kuskuren da na aikata daga yau. Amma a yi mini haƙuri a yafe mini a janye zancen sakin nan, in Sha Allah daga yanzun nan zan shiga fafutukar neman magani domin na zamo kamar yadda take so!"

Alƙalin ya girgiza kai ya ce,
"Hukuncinku rubuce yake a cikin littafan addinin Musulunci irinsu; Minhajil Muslim, Muwaɗɗa Malik da sauran littafan da suka zo da bayani a kan matsalarku. Saboda Allah ya fi kowa sanin kalolin halittarmu 'yan Adam, dalilin da ya sa kenan aka bai wa mata damar neman wanda ya yi daidai da buƙatarsu. Saboda gudun su faɗa halaka ta sanadin wannan matsala. Saɓanin kai da kake namiji kana da damar auren mace fiye da biyu zuwa uku har huɗu ma. Ita kuma kai kaɗai ne take da shi, idan ba ka cire mata kwaɗayin wasu mazan ba; za ta iya fita waje nemansu ido rufe domin su yi mata abin da take buƙata, Wanda kai ka kasa sauke mata nauyinsa a cikin gidanka. Don haka an bai wa mata damar muddin mijinsu ba ya gamsar da su yadda suke so, ko kuma ba ya iya ɗauke ragamar buƙatuwarsu a duk lokacin da suka nema a wurinsa; su kai kotu a raba auren, domin su je su auri wanda ya yi daidai da halinsu da kuma ra'ayinsu. Saboda tsoron su faɗa halaka a ɓoye ba tare da an sani ba."

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.