Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 1 of 99
78
78
Gaban Nana ya faÉ—i, cikin tsoro da razani ta ce "Waye? Waye a nan?" Sai dai shiru ba a yi mata magana ba.
Ta kunna fitilar kawai ta ga Imam Hammad a tsaye a cikin É—akin. Ja da baya ta yi a razane tana toshe bakinta saboda ihun da take shirin kurmawa saboda razani da tsoro.
"Idan ki ka yi ihun da Asal ta ji ki, za ki yi mata bayanin abin da ya kawo ni É—akin nan, kuma duk hukuncin da ta zartar a kan ki sai an yi miki shi, komai tsaurin sa."
Ta marairaice ido tana kallon sa cike da tsoro.
Ya tako a hankali ya ƙaraso gabanta, ya zuba mata idanunsa da suka ƙara rikita ta, jikinta har tsuma yake yi.
"Wace ce ke?" Ya yi maganar yana kafe ta da idanunsa.
"Ni ba kowa ba ce" Ta furta jikinta na tsuma cike da tsoron ko yana hayyacinsa jiya da ta je turakarsa.
"Ki gaya mini wace ce ke? Kuma da wace manufar ki ka zo gidan nan?"
Ta rintse idanunta tana girgiza masa kai ta ce "Wallahi ni ba kowa ba ce ba, Matarka ce ma ta kawo ni nan"
"Kin sanni a wani gurin kafin nan?" Ta É—ago kai ta kalle shi, ta girgiza masa kai a hankali, idanunta na cika da hawaye.
"Kin hana ni cin ayaba, kin ci kin yi rashin lafiya, kin hana ni hawa kan taguwa, na hau na faɗo. Idan na ganki ina jin wasu abubuwa da ba na ganewa a jikina, tamkar ke ba ɗan Adam ba ce. Ɗanɗanon Abincinki na yi mini kama da wani Abinci da nake ci a wani guri da ba zan iya tunawa ba, idan ba Abincin da ki ka dafa ba, ba ya yi mini ɗanɗano a bakina. Ki na shafa irin turarena kin ba ni madara da habbatussauda, wani abu da ba kowa ya san ina sha ba. Ki gaya mini wace ce ke, kuma a ina ki ka sanni?" Ya yi maganar yana ƙara matsawa daf da ita yana ƙara ɗaga mata murya.
"Ni ban sanka ba, ban taɓa zuwa Agadez ba sai a wannan karon, ni babu abin da na sani game da kai" Ta yi maganar hawaye na ta sintiri a kan fuskarta.
Ya numfasa ya ce "Idan wani ne ma ya turo ki, ki ke yi mini wasa da hankali, ki ji tsoron Allah, jarrabawoyin da suka yi wa rayuwata ma ƙawaanya sun ishe ni. Kar ki bari na kama ki da kowane irin nau'i na rashin gaskiya"
Ta yi shiru tana sunkuyar da kanta ƙasa.
"Nana ko?" Ta jinjina masa kai cikin tsoro.
"Ki yi haƙuri na tsorata ki, ba na son Asal ta gane wani abu, za ta ƙara tsanar ki ne." Daga haka ya juya ya bar ɗakin nata.
Neman guri ta yi ta zauna tana mayar da numfashi, saboda yadda ta tsorata.
*****
Sagir ne ya ɗauki Yusra suka tafi gidan su Shukura, domin ƙara jajantawa juna tare da su Hajiya Amina, ta kuma tabattar da iyayen Shukura ba sa zarginta da ɓatan Yusra kamar yadda take faɗa.
A babban falon gidan suka zauna, Hajiya Amina duk ta rame saboda tashin hankali da kuma damuwa.
Gefe ga Yusuf yayan Shukura, da shi ma fuskarsa take É—auke da damuwa.
Bayan sun gaisa Hajiya Amina ta ce "Sagir har yanzu babu wani labari game da ɓatan Shukura ko?"
"Wallahi Mami babu, na yi sintirin gurin jami'an tsaro amma babu wani labari, kullum sai dai su ce mini a kan bincike. An kasa tracking É—in in da wayarta take, abin dai sha'anin binciken na rasa gane wane iri ake yi"
Hajiya Amina ta ce "Babu komai, akwai Allah mu ci gaba da gaya masa, in sha Allah za ta kuɓuta"
Alhaji Zailani ne ya fito da shirin fita, Cikin girmamawa.
Bai amsa ba ya ce "Yaya ake ciki da batun Shukura haryanzu babu wani labari?"
"Eh Daddy, amma mu na ta addu'a in sha Allah za a gan ta"
"Ka ga ni fa na gaji da wannan kwana-kwanar, ta ɓangarena zan ƙara saka wa a tsananta bincike, dan kai kan ka ban yarda da kai ba. Ta yaya za a ce rana tsaka a nemi yarinya a rasa ga tsohon ciki, kai me yasa ba a neme ka an rasa ba ko matarka sai ita?"
Hajiya Amina ta ce "Haba Alhaji, ya za a yi Sagir ya sanya a sace Shukura a sace ya kai ta ina?"
"Ni ki yi mini shiru, babu abin da ba zai iya faruwa ba" ya gama bambaminsa ya fita.
Hajiya Amina ta ce "Ka yi haƙuri Sagir, kawai yana cikin tashin hankali da damuwar ɓatan Shukura ne. Dan Allah kar ka damu za a gan ta da yardar Allah"
Yusra ta ce "Da ƙawata tana nan wataƙila da tuni ta gaya muku inda Shukura take".
Gaba É—aya suka kalli Yusra, ta ce "Eh Nana mana, ai kin tuna ta ko?" Ta yi maganar tana kallon Hajiya Amina.
Ta jinjina kai. Amma Sagir ya ce "Mami bari mu tafi, kin san ba ta da cikakkiyar lafiya ne"
Mami ta ce "Allah sarki, amma ta yi gaskiya na san Nana, a ina ki ka santa?"
Yusra sai ta yi shiru, saboda ba ta son ta ji an ce ba ta da cikakkiyar lafiya, amma tun da suka shigo gidan, ta ji ƙamshin Nana.
*****
Nana kuwa bayan sallar asuba, ta kashingiɗa tana ta zancen zuci, tana tunanin mece ce mafitarta ta ƙarshe, ta fuskanci kullum al'amuran cikin ƙara rikice mata suke.
Wayarta ta É—aukko tana kallon hotunan Muhsin, kewarsa take yi sosai da sosai, har sai da hawaye ya cika mata ido. Sai ta yanke shawarar neman izini daga gurin Imam, ta je gida, dan ta ga ya fi Asal kan gado.
Sai dai wani abu mai kama da bacci ya ɗauke ta, sai dai ta iya kiran shi da dannau, wato sleep paralysis, da wasu kan ce aljani ne yake danne mutum, ya yi iya ƙoƙarinsa gurin tashi amma ya kasa.
Iya ƙoƙarinta take son ta yi addu'a, amma ta kasa. Inuwar mutum ta gani ya shigo ɗakin, amma ba ta iya tantance wane jinsin ba ne ba, mace ko namiji.
Inuwar na zuwa aka zare wayar da ke hannunta, aka fice.
Cikin razani da tsoro ta farka a galabaice tana ta haki tana rarraba ido, amma ba ta ga kowa a É—akin ba, ta laluba ta nemi wayarya ta rasa. Hankalinta ya yi mummunan tashi, ta É—aga fulon, ta zazzage inda take zaune, amma babu waya babu dalilinta.
Ta tashi cikin azama ta hau buÉ—e kayanta, ko wayar tana ciki, amma wayam babu waya babu dalilinta.
Ta fita da sauri ko za ta ga alamar wanda ya shigo sashen amma ba ta ga kowa ba.
Hankalinta ya yi mummunan tashi, saboda rashin sanin wanda ya shigo ya É—auke mata waya.
Gudun masifar Asal idan ta makara gurin hattama abinci ya sanya ta shiga É—akin girki.
Ta fito jiki a sanyaye tana gyaran falon Asal ta fito, kamar Nana ta share ta sai kuma ta ce mata "Barka da wannan lokaci"
"Yauwwa. Amm kar ki damu da ajiyewa Imam abinci, tun asuba baya nan, za su yi zaman majalisar Sultan." Nana ta jinjina kai.
Idan haka ne ba shi ne ya sake shigar mata É—aki ba kenan, to ko Asal ce?
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.