Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 12 of 99

Wata irin É—agowa ta yi, cike da takaici, ya shammace ta ya rungume ta ya haÉ—e bakinsu.
Nana ta tattara nutsuwarta, da duk wata jarumta dan ganin ba ta biye wa Sayyid. Ta din ga ture shi iya ƙarfinta tana kai masa duka, amma tamkar dutse ba jikin ɗan Adam take duka ba. Sai da ta gaji ta ƙyale shi. A hankali ya zare bakinsa daga nata ya ɗago fuskarta yana kallonta.

Hawaye sharkaf a kan fuskarta, ya ce "Kar ki wahal da rayukanmu, ni da ke abu guda ne Asmy, ko kin tafi kin bar ni, ba za ki taɓa samun nutuswa da kwanciyar hankali ba. Kamar yadda tun da muka rabu nawa ruhin ma bai samu nutsuwa ba. Ina ƙaunarki rayuwata" Duk yadda Nana ta so yi masa rashin kunya, ta gaggaya masa maganganu masu zafin gaske, amma ta kasa tamkar ya saka wani abu a cikin idanunsa da ya yi tasirin da ya hana ta maganar.
"Ki yi mana addu'a rayuwata, akwai kaya a É—akin da muka je jiya, idan kin yi wanka akwai kayan sakawa. Sai akwai kitchen shi ma, duk za ki iya shiga ki dafa mana duk abin da ki ke so. Sai na dawo" Ko tari Nana ba ta kuma yi ba, har ya tashi ya bar É—akin, ta bi bayansa da harara.

Nene ce rungume da Muhsin, ya sha ado cikin kayan buzaye, kayansa iri ɗaya da na jikin babansa, sai ƙoƙarin cire mayafin da aka rufe masa gashinsa da shi yake yi, sai ƙamshin turare yake yi.
Hammad ya saka hannu ya karɓe shi fuskarsa ɗauke da murmushi har da wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.

Hammad ya ce "Mu je ko?"

Nene jiki a sanyaye ta ce "Ina mai neman afuwarka, ni tsoron zuwa gidan nan nake yi. Kuma a wane hali Nana take ciki yanzu, na kasa nutsuwa gaba É—aya, ina jin ban kyauta ba gaba É—aya"

"Ki kwantar da hankalinki, Nana tana tare da ni, kuma babu wanda zai yi miki komai a cikin gidan, ki taimaka mini dan Allah"

AREWABOOKS

Nene ta numfasa ta ce "Alfamarka ce kawai za ta sanya na yi maka abin da ka nema, dan na yi alƙawarin babu abin da zai sake haɗa ni da wannan gidan naku, saboda mummunan tabon da yake binne a zuciyata. Kuma da ko me za ka yi mini ba zan ba da ɗan nan ba, saboda ya saɓa alƙawarin da muka yi da Nana, ban kyauta mata ba za ta yi mini kallon mutuniyar banza mara alƙawari. Amma kai ma ɗa ne a gurina, ban da dalilin haka gaskiya ba zan iya ba"

"Na sani, kuma na gode sosai da sosai, da wannan alfarma da ki ka yi mini"

Ta risunar da kanta cikin girmamawa. Ya miƙa mata Muhsin ta karɓe shi, suka shiga mota.

*****
A tsanake Tafawa ya kalli Asad ya ce "Asad, wai waye ka ce ya karɓi ayabar nan ya ci?"

"Wata yarinya ce, ni ban santa ma a gidan nan ba gaba É—aya"

"Dole a nemo ko wacece, saboda an tabattar mini, da cin ayabar da ta yi, da gayya ta karɓa ta ci, dan aikin da aka yi ya ɓaci ya lalace."

Asad ya yi shiru, ya ce "Gaskiya ban san ko wace ce ba, sai dai ko a tambayi Asal, ko ta santa abinci dai ya kawo mana. Ina kyautata zaton ko kuku ce ko dai makamancin hakan. Ban ma san yadda aka yi ta zo inda muke ba, dan kamar ba buzuwa ba ce gaskiya"

Tafawa ya yi shiru yana nazari, ya ce "Babu yadda za a yi wadda ba buzuwa ba, ta tsallako ta shigo gidan sarautar Agadez, ta yi wannan abin, lallai zuwanta na manufa ne, dole a binciko wace ce."
Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa.

Asal duk ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankali, mussaman da Imam ya kwana uku ba ta san inda ya shiga ba, hakan ya sanya ta fara jin kamar akwai ƙamshin gaskiya a maganar da Tafawa ya gaya mata. Ta kasa jurewa ta je ta samu Sultan, tana yi masa kuka.

Cikin damuwa ya ce "Yarinyar kirki lafiya kuwa?"

"Sultan ji na yi an ce wai Imam yana da É—a, dama aure ya yi ban sani ba? Kuma tun shekaranjiya ban sake ganinsa ba, kuma ba na samun sa a waya"

Sultan ya ce "Waye ya gaya miki?"

Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. Ya numfasa ya ce "Shikenan na fahimta, amma ki kwantar da hankalinki, na tabattar da Hammad ba zai aikata abin da zai zubar da kima da mutuncin gidan nan ba, dan haka ki yi haƙuri ki bani lokaci, ina kan bincike ne"

"Amma Abie, to ina ya tafi, haryanzu ban san inda yake ba, kuma wayarsa ba ta shiga"

Sultan ya ce "Na sani, ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki. Zai dawo in sha Allah" Asal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi, sai dai zuciyarta ta gaza haƙuri da samun nutsuwa.

Washegari, Sultan na tare da Sardauna da kuma Matawalle su na tattaunawa, aka zo neman iso cewar Imam Hammad yana neman izinin shigowa.
Cikin takunsa mai burgewa, ya shiga. Gaba É—aya suka zuba masa ido suna kallonsa.
Hammad ya nemi guri ya zauna a ƙasa tare da gaishe su. Matawalle ya amasa masa. Sultan kuwa rasa abin cewa ma ya yi sai daga bisani ya numfasa ya ce "Ina ka tafi tsawon kwanaki uku haka, ka kashe wayoyinka ka tayar mana da hankali?"

Hammad ya numfasa ya ce "Ina mai bayar da haƙuri, na laifin da na aikata, na yi hakan ne, domin tabattar muku da abin da na faɗa. Ina cikin hayyacina na faɗi abin da na faɗa, kuma da shaida a kan abin da na faɗa".
Sardauna ya ce "Ka na da hankali kuwa? Ka na nufin da gaske ka haihu da matar da ba mu sani ba?" Ya jinjina kai daidai lokacin da Mahmoudu ya shigo É—akin shima."

Matawalle ya ce "Ga munafukin nan, ya san komai"

Sardauna ya ce "Ni kun sani a duhu, shi kuma wannan waye ya kawo shi cikin wannan mas'alar?"

Sultan ya ce "Bari mu ji ta bakinsa"

Mahmoudu ya zauna ya gaishe su. Sannan ya numfasa ya ce "Da fari ina neman afuwar mai girma Sultan, da ahalinsa da 'yan majalissar sa, da ma duk wani wanda abin ya shafa. Na san na aikata laifin da na cancanci hukunci, kuma a shirye nake na karɓi hukuncin laifina, na aikata abin da ya saɓa wa dokar masarauta duk da girman matsayin Imam Hammad a ƙasar nan"

Sardauna ya ce "Mu na jin ka, ka yi mana bayani, me ka aikata, kuma me a sani a kan lamarin?"

Sultan ya numfasa ya ce "Wato Sardauna mun ɓoye wa mutane abubuwa da dama da suka faru. Magana ta gaskiya Imam Hammad ya samu matsala ya bar ƙasar nan bamu sani ba. Mun yi ta bibiyar inda zamu samo shi. Muka rufe muka ce yana faransa babu lafiya. Da muka rasa shi, aka rasa hadiminsa Mahmoudu, shi ne muka koma binciken Mahmoudu ta ƙarƙashin ƙasa, aka yi nasarar gano su a Nigeria. Sai dai da aka dawo da shi Agadez tamkar ya manta da mu baki ɗaya, baya cikin hayyacinsa. Bamu san haƙiƙanin abin da ya faru a Nigeria ba, sai dai idan sun yi mana bayani yanzu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.