Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 20 of 99

Bangaren Sagir ma bai fitar da rai ba, yana ta addu'a, da ji a jikinsa Yusransa za ta dawo. Ga shi satin haihuwarta ya kama. Ya daure ya lallaɓa ya je duba Yusra. Wadda ita ma jiki yake a rikice.
Sai dai da yaje ya tarar da jikinta da ɗan sauƙi, dan har suka ɗan fara hirar hankali.
Ta ce "Haryanzu ba a ga matarka ba ko?"

"Haryanzu Yusra, amma kina yi mata addu'a Allah ya bayyanata?"

Ta ce "Ina yi mana, ina so Allah ya sanya a ganta, kuma fa a satin nan za ta haihu, dan ta ma fara naƙuda kaɗan-kaɗan"

Ya ce "Yaya aka yi ki ka sani?"

Ta ce "Mafarkinta na yi mana, tana kulle a wani ɗaki mai duhu, ta ce mini ba ta jin daɗin  zaman gurin, baka gani ba abin tausayi"

Idonsa fal ƙwalla ya ce "Duk a mafarkin ki ka ga haka?"

"Eh mana, tana ta kuka ma"

Ya ce "Shikenan, ya isa haka. Ki ci gaba da yi mata addu'a bari na je gida. Amma yaushe za ki zo mu koma gida, ina fama da kaÉ—aici"

Ta ce "Ko yau ka yi wa Anty magana sai na bika mu tafi"

Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, babu laifi"

Shukura kuwa tana kwance a ƙasa, zama babu daɗi, kwanciya babu daɗi duk inda ta motsa cikin nan sai ya tokare ta. Ga ciwon baya da na ƙafafuwa da take yi da take kyautata zaton naƙuda ta fara a tsaitsaye.
Sai dai tana yawan ganin Nana cikin mafarki, tana nanata mata ta yawaita addua babu ƙaƙƙautawa babu ji babu gani. Duk da tana yi ɗin amma ta ƙara ƙaimi gurin yi.

*****
Ko da aka shiga kwana na biyar da shigar Hammad halin da yake ciki, Sultan ya gama tsurewa babban tashin hankalinsa rashin cin komai da ba ya yi ga abin kullum gaba yake yi.
Tafawa ya samu Sultan a kan lallai a sake zaman majalissa, a ji bayanin Hammad a gaban kowa da kowa a kan yadda aka yi yake da É—a kamar yadda ya faÉ—a."

Matawalle ne ya amsa masa da cewar "A tunanina wannan maganar ai ta wuce ko?"

"Ta wuce ta je ina? Kun san zata wuce ku ka dakatar da ni daga majalissa. Ya faɗi abin da dole sai ya fito ya kare maganar da ya yi. Ya ce yana da ɗa, ina ɗan yake? Kuma wacece uwar yaron? Idan kuma shaci faɗi ne to ta tabatta ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa da na faɗa ku ke ɓoyewa"

Matawalle ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ka san abin da zaka din ga furtawa a kansa, ko babu alaƙar jini a tsakaninku shi shugaba ne."

"Eh Hammad ɗa na ne, kuma shugaba ne, amma ba zai yiwu na zuba ido ina ganin ba daidai ba, a ce yana shugaba babu cikakkiyar lafiya ba kuma ku na dannewa ku ɓoyewa ba. Ita larura ai ba abin kunya ba ce, kuma abu ne da yakamata a sani domin a nemi lafiya"

Cikin nutsuwa Sultan ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ban sna meyasa ka ke aibata shi da da wannan larurar ba"

"Allah ya taimake ka, idan ba haka ba ne, mene ne gaskiyar batun É—an da ya ce yana da shi?" Tafawa ya yi maganar yana tsare Sultan da ido.

"Abu ne da muke kan bincike a kai, koma mene ne zaka ji daga baya"

Ya ce "Shikenan na ji wannan, ina son zan yi magana da shi, magana ce a kan É—iyata Asal"

Sultan ya kalli Tafawa cike da takaici, ya san yana sane yake wannan bin ƙwaƙƙwafin da bin diddigin a kan lallai sai ya ga Hammad."

Sultan ya ce "Za ka gan shi, amma nan da wani É—an lokaci" Hakan ya sanya Tafawa sake tabattar da maganganun Asal.
A ransa ya ce "Idan ka san wata baka san wata ba Jalaludeen"

*****
Tun washegarin dawowar Nana daga gidan su Hammad, yanayin jikinta take jin babu daɗi, kamar akwai wani abu mara daɗi da yake faruwa. Sai dai ta danganta hakan da kewa da kuma tashin hankali da take ciki a kan Muhsin. Amma idan ta nutsu sai ta ji wannan damuwar daban ce, wannan a cikin jikinta da ruhinta take jin damuwar, sai dai ta yi iya ƙoƙarinta gurin danne damuwar, da duƙufa da addu'a Allah ya dawo mata da ɗanta.
Yau da safe Nana ta fito ta tarar da Nana, ta ɗora tukkwane daban-daban har uku a kan murhu, tana ta harhaɗa wasu irin saiwoyi da sassaƙe-sassaƙe tana ta zubawa tana dafawa.
Nana ta ce "Umman Muhsin, yau kuma baya aka tuna wa ake dafa wa magani"
Nene ta yi murmushi ta ce "Ba kula ki zan yi ba ai ki ƙarata, daɗin abin ƙwaryar sama ce ke dukan ta ƙasa daga ni har ke"
Nana ta yi dariya ta ce "Yasin ni ban bayar da magani ba"
"A'a tuna dai, tuna dai yarinya"
"To ai Sayyid kawai na yi wa"
Nene ta ce "Kash, an zo gurin dan haka ki yi mini shiru" Ta ƙarasa maganar tana janyo wayarta da ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta tsuke fuska ta kira Mahmoudu a waya. Ya amsa tare da gaishe ta.
Bayan ta amsa ta ce "Wannan uban kuÉ—in fa da ka sako mini?"

"A'a ki yi haƙuri ai ba naki ba ne, na kula da Gimbiyar Imam ne"

"Da can ku kuke bani abin kula da ita? Lokacin da take gararambar neman taimakon ba ku neme ta ba ba barin ta ku ka yi tana gantali a titi ba?"

Ya ce "Dan Allah ki yi haƙuri, ba zan iya gaya masa haka ba. Haryanzu fa ma ni ban sake ganinsa ba tun ranar da ya je tare da ita. Ba ya gidansa baya fitowa zaman majillisa, ko hawa ba ya fitowa. Duk da na san an saka masa takunkumi shige da fice amma an tsaurara masa sosai. Ki yi haƙuri har gida za mu zo ban haƙuri. Dan Allah ki taya mu rarrashinta dan ta ƙi saurararsa gaba ɗaya, kuma wallahi hankalinsa a tashe yake nesa ba kusa ba. Ga tarin magauta da yake da su a cikin gidan su ma da ba barinsa suka yi ba. Dan Allah ku yi haƙuri Umma ke kin san sha'anin gidan sarauta kin san komai"
"Ni rabu da ni sai daÉ—in bakin tsiya, ai ko mutum zai danne ya yanka sai ka kare shi"
Yayi dariya ya ce "Ai ɗanki ne, kin san ba zai aikata haka ba, tuba muke ranki ya daɗe. Wallahi ina ta faɗi tashin na gan shi ne ma, na san halin da yake ciki. Amma a ƙara ba wa Gimbiyar Imam haƙuri"

"A'a babu ruwana, idan ku ka zo kwa bata da kanku" Suka yi sallama ta kashe wayar.

Ta kalli Nana ta ce "Kafin ki yi wanka, fara É—ibar ruwan maganin nan, ki je ki yi wanka ki gama, sai ki yi wanka da shi. Ki fito ki sha wannan maganin sai ki karya.
Nana ta ce "Shi kuma Nene na mene ne?"
"Na tsarin jiki da kariya ne, saboda kariya ne" Ta yi maganar tana basarwa, tare da tsuke fuska dan kar Nana ta addabe ta da tambayoyi.
Ganin hakan ya sanya Nana amsawa Nene, ba dan tana so ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.