Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 76 of 99
"To bawan Allah, ni wa nake da shi Agadez, kuma ba ɓatan kai ku ka yi ba?"
Mahmoudu ya ce "Ba mu yi ɓatan kai ba, na yi mamaki da ka ce ba ka gane ni ba, amma ai ka tuna buzun da ka aura wa 'yarka shekarun da suka gabata"
A razane Baba ya ɗago ya kalli Mahmoudu, sai kuma ya riƙe rigarsa, ya ce "Dama ku ne? Ba ku yi mini adalci ba, ku ka tattara ku ka gudu, ku ka bar mini 'ya da jinyar ɗan uwanku, shi ma daga ƙarshe ya gudu ya bar ta, saboda wauta da rashin hankali wai ta tafi Niger neman shi, haryanzu shekara ta uku kenan, babu wanda ya san inda take, baku kyauta mini ba" Baba yayi maganar yana kuka kamar ƙaramin yaro.
Imam Zahradeen ya ce "Baba, ka yi haƙuri abubuwan da suka faru ba a kyauta maka ba. Amma mu na da kyakyawan albishir ne"
Baba ya ce "Kai ba kai ne mijin nata ba?" Yayi maganar yana nuna Imam Zahradeen.
Zahradeen ya ce "Baba ai na fi wancan tsufa, shi ya fi ni ƙuruciya, ya kuma fi ni kyau, ni yayansa ne. Zancen da nake yi maka, a kowane lokaci mahaifinmu zai iya aiko da mutanensa daga Agadez da kayan auren Nana za a sake gagarumin bikin aurensu"
Baba ya ce "Ashsha! Yarinyar da nake gaya muku shekara uku babu wanda ya san inda take, kuma babu wanda ya waiwaye ta tunda ku ka gudu kuka bar ta. Kuma ni mene ne haÉ—ina da Sarkin Agadez da zai kawo kayan aure? Ni dai na yi nadamar abin da na aikata na aurar da 'yata ga mutumin da ban san daga inda yake ba"
Imam Zahradeen ya lura ran Baba a ɓace yake.
Ya sassauta murya ya ce "Baba sunana Imam Zahradeen Jalaludeen Agadez, ni Yaya ne ga Imam Hammad Jalaludeen Agadez. Kuma 'ya'ya ga Sultan Jalaludeen Agadez, wato Sarkin Agadez na yanzu. Buzun da ka aura wa 'yarka, ɗan uwana ne, kuma ɗa ne ga Sultan na Agadez."
Baba ya kalli Imam Zahradeen kamar yana raina masa hankali.
Ya ce "Ɗan sarki ne zai zo baro ƙasarsa ya zo Nigeria yana aikin gadi?"
Mahmoudu ya ce "Baba, idan baka manta ba, ko lokacin da aka yi aurensu, a yanayi na rashin lafiya yake, rashin lafiya ce ta kama shi"
"To yaya za a yi a ce É—an sarki ya zo Nigeria gadi, ni abin ya bani mamaki ne. Kuma na kasa yarda, ni kar ku sake dugunzuma mini hankali bayan halin da nake cikix
Zahradeen ya ce "Baba ba dunguzuma maka hankali za mu yi ba. Mun zo mu sanar da kai batun zuwan baƙinka ne daga Agadez, kafin su zo ɗin."
"To wai su zo, su yi mini me?"
" 'yarka Nana, tana gurinmu tare da É—anta Muhsin"
Baba bai san ya aka yi ya tashi tsaye ba, yana zazzaro ido ya ce "Nana Asma'u dai 'ya ta? Yaya aka yi ku ka same ta? Tana ina? Kun taho mini da ita?"
Mahmoudu ya miƙe tsaye ya ce "Baba shi ne bayanin da muke yi maka, Nana tana tare da mu, za a kawo dukiyar aurenta Nigeria za kuma a yi bikin aurensu sosai da sosai. Duk abin da za mu gaya maka yanzu ba za ka fahimce mu ba, saboda a cikin damuwa ka ke, kuma abubuwan da suka faru su na da tsawo da sarƙaƙiya akwai buƙatar a yi maka bayani daki-daki. Ba Nana ba hatta Imrana yana tare da mu a Agadez, akwai tarin bayanai da sai ka nutsu, an yi maka bayani zaka fahimce su"
"Amm bawan Allah, ni ko yanzu a shirye nake, mu tafi Agadez ɗin na karɓi 'ya'yana. Bayan Nana kuma me ya haɗa ku da Imrana"
Imam Zahradeen ya ce "Alkhairi ne, a cikin satin nan, zuwa mai kamawa in sha Allah; za a sake turo maka baƙi daga can. Kuma za a yi bikin su al'ada saɓanin yadda ya gudana, kuma za a yi maka bayani kamar yadda nake nanata maka. Amma kafin nan mu na son za a gyara maka gidan nan, ko kuma a canza maka wani"
Baba ya girgiza kai ya ce "Ba na buƙatar haka, muddin Nana yake so, babu amfani a raina inda ta fito, ni dai fatana na gansu cikin ƙoshin lafiya"
Zahradeen ya ce "Ba raina maka aka yi ba, matsayinka da girmanka ne ya sanya za a yi maka." Fafur Baba ya ƙi yarda da hakan, da kyar suka rarrashe shi suka tafi, dan cewa ya yi ba za su bar ƙofar gidansa ba, ba tare da ya ga yaransa ba.
Kasancewar duniya makarantar da ko babu malami, ta biya maka darasi dole ka É—auka ce, ta karanta wa Baba darasin da duk son abin Duniyarsa, yanzu tsoro yake ji.
Zuwansu Imam Zahradeen babu wanda ya sanarwa, saboda gani yake yi tamkar ƙarya Buzayen nan suka zo suka sharara masa.
Ya kasa gaya wa kowa, sai Uwani ya kira ya sanar mata. Sai dai a ƙarshen maganar Baba ya ce "Amma Uwani ni ban ji na yarda ba, ji nake kamar ƙarya kawai suke yi ban ji na yarda ba"
Uwani ta ce "Alhamdillah, ni dai na ji na yarda har cikin zuciyata. Ko ba hakan ba ne, ina fatan Allah ya tabattar da shi ya zama gaske. Wallahi zuciyata ta daɗe tana bani, mijin Nana ba ƙaramin mutum ba ne, to ita Nanan da gaske tana gurinsu, kuma har da Imrana sun haɗa ku ko a waya ne?"
Ya ce "A'a, shiyasa na kasa yarda ma gaba É—aya"
"Isa, yarda ni dai na gama ta, zamu duƙufa mu ci gaba da addu'a in sha Allah Nana suna cikin kwanciyar hankali tare da ɗan uwanta" Kalaman Uwani suka ɗan ƙwarara wa Baba gwiwa.
Bayan sallar isha'i ya shiga gida, yana zaune yana jin radio, Mama tana cikin É—aki tare da Jamila da ta koma so silent, ko magana ba ta iya yi.
Ihun da Jamila ta yi ne, ya sany Baba jifa da radio ya tashi tsaye yana rarraba ido.
"Mama! Mama!! Dan Allah ki taimake ni, dodon ƙungiya zai shanye mini jini. Hajiya Sa'a kin cuce ni, kin cuci rayuwata, na kasa samun aminci da salama. Na baku Abba me kuma ku ke nama a gurina?"
Cikin rashin fahimta duk suke kallon Jamila, Baba ya ce "Me yarinyar nan take faÉ—a ne haka?"
Mama ta ce "Nima ban sani ba wallahi, ina ga jikin ne ya motsa."
Baba ya ce "Jikinta ya motsa kuma take irin wannan maganganun?"
Ba ta ko saurare su ba, ta ci gaba da surutanta. "Ni ban so shiga kungiyar nan ba, dole ki ka yi mini, ga shi kin sanya ni a bala'i, na rasa mutuncina, kin saka nayi kisan kai, yanzu kuma na kasa samun kwanciyar hankali, sai tsorata ni ake yi, nima ana nema na a kashe ni, kin cuce ni"
Baba ya ce "Jamila, meyafaru ne? Me ki ke faÉ—a wai?"
"Baba riƙe hannuna, Baba ku taimake ni"
Ya ƙarasa ya riƙe hannun Jamila, cikin kuka ta ce "Baba na shiga uku, na aikata mummunar ɓarna, Baba hakki ne zai yi ajalina"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.