Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 19 of 99
82
LITTAFIN KUÆŠI NE, KARKI RAINA GIRMAN HAKKI, 1K NE VIA 0069685771
Aisha Adam stanbic
08081012143
Hankalin Sultan da muƙarrabansa ya dunguzuma nesa ba kusa ba. Suka gaza gane kan Imam Hammad ta ko ina.
Ga Muhsin shi ma yana ta rikici, ba ya cin abinci sam, sai koke-koke ya ƙi saurar kowa saboda rashin sabo.
Cikin tashin hankali Sultan yake kallon Hammad da yake wance kamar itace, ya dubi Matawalle ya ce "Anya Matawalle ba Asibiti zamu kai shi ba. Ina ga wannan ɓoye-ɓoyen da muke yi, lokaci ne ya yi da asirinmu zai tonu. Sai dai ina jin tsoron a san halin da muke ciki".
Matawalle ya ce "Wannan ba abin da ya shafi Asibiti ba ne, ko ka manta haka ya yi ta yi a lokacin da aka dawo da shi daga Nigeria? Sai da muka fita faransa sannan ya daina wannan abin,har tunaninsa ya dawo?"
Sultan ya ce "Haka ne, amma kamar wannan karon, abin ya ninka wancan da ya yi. Ba ya ci ba ya sha fa" Ya yi maganar cikin damuwa.
Matawalle ya ce "Nima abin da ya tsorata ni gaskiya, amma dole mu nemo masu magani da za su duba shi. Amma ya zama dole mu samo waÉ—anda ba za su furta komai ba, idan ba haka ba nan ma akwai matsala"
Sultan ya dafe kansa yana kallon Hammad, tamkar ya fashe da kuka.
Asal ta shigo É—akin da sallama, ta kalle su ta gaishe su cikin girmamawa suka amsa mata baki É—aya.
Cikin damuwa ta ce "Abie yau ma bai farka ba ko?"
Sultan ya jinjina kai ya ce "Bai farka ba Asal"
Daga nesa inda take tsaya take ɗan leƙa shi ta ce "Baccin dai yake yi?"
Matawalle ya ce "Ƙaraso ki gan shi mana"
Ta girgiza kai ta ce "A'a shaƙe ni yake yi ya kusa kashe ni, daga nan ma ina hango shi"
Babu babban abin da yake sake É—aga wa Sultan hankali, sama da wannan azababben zafin da jikinsa yake yi mai ban tsoro, kamar ba jikin É—an Adam ba.
Da yamma Sultan na cikin É—akinsa, yana ta kai komo, ya rasa mene ne mafita, ya san muddin batun ciwon nan na Hammad ya fita, ba su da wata mafita.
Aka sanar masa da isowar Imam Zahradeen. Ya bayar da iznin ya shiga. Bayan shigarsa suka gaisa. Ya dubi Sultan ya ce "Abie, wai ko ka aiki Imam Hammad wani gurin ne? Ya saka ni wani aiki, na je gidansa Gimbiya Asal ta ce "Baya nan, kuma a iya sanina ban san ya yi wata tafiya ba"
Sultan ya ce "Haka ne, yana ƙarƙashin takunkumi na hana shi zuwa ko ina ne".
Ya ce "Na sani, ina son ganinsa ne, a yi mini alfarmar nan, wani saƙo zan isar masa na aikin da ya sanya ni"
Sultan ya dubi Zahradeen ya ce "Aikin me kenan?" Zahradeen ya sunkuyar da kai ya yi shiru. Sultan ya ce "Shikenan na fahimta, amma a yanzu dai ka yi haƙuri ba zaka samu ganinsa ba, yana ƙarƙashin takunkumi "
Imam Zahradeen ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Shikenan, godiya nake ranka ya daɗe" Daga haka ya tashi ya bar sashen. Ya san iya takunkumin hana fita aka ƙaƙaba masa, banda na killace shi a hana ganinsa gaba ɗaya, amma lokaci ɗaya an ce har ganinsa ma ba zai yiwu ba.
*****
Nana ce zaune ta saka kwanon abinci a gaba ta yi shiru, Nene ta taɓa ta ta ce "Ki ci Abincin mana, kin bari yana ta shan iska"
Nana ta numfasa ta ce "Nene wai zuwa yaushe zan je na karɓo ɗa na ne, ci gaba da zama fa bai kamace ni a garin nan ba, ni duk hankalina ya yi gida wallahi"
"Nana na san duk abin da nake yi, ba na son ki faɗa komar mutanen nan, su ci moriyar ganga su yada kwaronta. Mutane ne masu bala'in son kansu fiye da yadda ki ke tunani, dan haka ki ɗan yi haƙuri. Sai dai Nene na rufe baki, wayarta ta fara ringing.
Nene ta É—auki wayar ta saka a kunnenta tare da yin sallama.
"Barka da wannan lokaci Ummana"
Ta amsa da "Barkanmu dai"
"Umma dan Allah Nana tana tare da ke ne? Idan ke ki ka É—auke ta ki taimaka ki sanar mini inda ki ka kaita, kan Imam Hammad ya farga ba ta nan, wallahi ban san me zan ce masa ba"
Nene ta ce "Idan ya fargan me ya yi saura a tsakaninsu? Ba dai ɗanku ba ne kun ƙwace? Takardar sakinta kawai muke jira, zan mayar da ita Nigeria har gidansu"
Mahmoudu ya ce "Ummana, wannan wani abu ne da ya shafi Nana da Imam da iyalinshi. Ni fa kamar ya san za a yi haka ya haÉ—a ni da Imam Zahradeen ya sanya aka killace ku a wannan gidan, kuma lokaci guda sai ki É—auke ta ki tafi na neme ki na rasa. Dan girman Allah da buwayarsa ki taimaka ki gaya mini inda ku ke"
"Kai ka kiyaye ni, ba zan faÉ—a ba É—in, ba ku da wani haÉ—i da Nana, ka gaya wa ubangidanka ya aiko mini da takardar yarinyata, zan mayar da ita gaban iyayenta ta nemi gafararsu" Ta katse wayar.
Nana ta ce "Nene to idan ya sake ni ba su bani Muhsin É—in ba fa?"
"Shi Muhsin É—in da shi aka haife ki ne?"
Idon Nana fal hawaye ta ce "Ni dai a bani É—a na kan ya sake ni"
Nene ta girgiza kai ta ce "Nana kina cikin jarrabawa, wannan ɗan shi zai sanya ki lalata komai ki kasa ƙwatarwa kanki 'yanci, ai sai ki yi"
Nana ta ɗan ɓata fuska ta ce "Amma Nene, ya aka yi aka saki Mahmoudu na ji sun ce wai sai sun hukunta shi, sun ɗora masa laifin aurenmu, sun sake shi kenan sun fasa hukunta shi?"
Nene ta ce "Oho musu, su kashe shi ma kar su bar shi da rai."
Nana ta waro ido ta ce "Nene wai ke ba kya son É—an nan naki ne?"
"To Nana idan ma ina son nasa, zan goya shi ne?"
"To Nene dama mutum yana daina son É—ansa ne?"
Nene kawai ta yi murmushi, ta tashi ta bar Nana da wasi-wasi.
*****
Wasa-wasa aka shafe kwana uku curr ba a ga 'yar gidan Doctor Sharif ba, ga matarsa a Asibiti, hankalinsa ya tashi kamar zai haukace. Ga jikin matarsa kullum babu afuwa ga shi ta fara damuwa da ina Hafsa take. Sai dai ya ce mata tana gida ba ta da lafiya.
Ya din ga yawo gurin 'yan sanda da gidajen radio, yana bayar da cigiya ko za a ganta. Ya din ga jin tamkar ya ɗora hannu a ka ya zunduma ihu. Gefe guda ga mummunan mafarkin da yake yi da Shukura babu ƙaƙƙautawa har fargabar kwanciya bacci yake yi. Saboda munanan mafarkai ne marasa daɗi.
Ya shiga Asibiti ya tarar da wata katoɓara, an yi wa matarsa insulin allurar sauke sugar, fiye da kima suganta ya yi mummunan sauka, har ta shiga shock.
Tare da sauran abokan aikinsa likitoci, suka yi ta fafutuka ƙoƙarin ganin sun ceto ranta. Yana tsaka da wannan tashin hankalin 'yan sanda suka kira shi, ya tafi cike da fatan 'yarsa Hafsa aka gani. Sai dai 'yan sanda suka ce masa Asibiti za su je ya ga wata yarinya da aka tsinta aka kaita domin a duba lafiyarta. Suka ɗauke shi a mota suka tafi. Sai dai suna zuwa aka tafi da shi ɗakin adana gawarwaki. Sam bai kawo komai a ransa ba, idonsa ya rufe kawai Hafsansa za a nuna masa. Sai dai aka fito da gawarwaki biyu. Ɗaya a kango a ka tsince ta, an fafe cikinta an kwashe wasu sassa na jikinta a can wata unguwa. Yarinyar sanye da Uniform ɗin makarantar da ya fasaltawa 'yan sanda.
Tamkar ba Namiji ba, haka ya kurma uban ihu ya faɗi ƙasa sumamme, bayan ganin 'yarsa Hafsa a wannan mumman yanayi.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.