Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 33 of 99
Tafawa mutuwar zaune ya yi, tare da bin Hammad da ido, jin sun Sardauna yi shiru kuma babu wanda ya musa, ko ƙaryata abin da Hammad ya faɗa ya sanya shi tabattar da abubuwan da Hammad ya faɗa gaskiya ne.
Sultan da tuni gumi ya jiƙe shi ya ce "Ina fatan ka ji daɗi, da ka kai shi bangon da ka sanya ya fito ya tabattar maka da abin da ka ke son tabattarwa? Ina ga shikenan za ka iya tafiya."
Tafawa bai iya furta uffan ba, jikinsa a matuƙar sanyaye, ya tashi yana jan ƙafarsa, da yake jin kamar ba a jikinsa take ba, da kyar ya fice.
Gaba ɗaya suka yo kan Imam Hammad da faɗa kamar za su dake shi. Hammad ya ce "Ina neman afuwarku, a kan abin da na aikata ba tare da izninku ba. Amma har abada ƙarya fure take yi, ba ta 'ya'ya, ba zamu dauwwama ɓoye wa duniya abin da komai daren daɗewa sai ya bayyana ba. Ba zan iya ci gaba da jure kullum lokacinku ya tafi a kan bani kariya ba, duk na san na aikata laifi, zan tsaya a kan laifina na karɓi duk hukuncin da ya dace".
Sardauna ya ce "Kuma saboda shirme sai ka ce ka sauka daga kan kujerar Imam? Dama kai ka É—ora kanka?"
Suka din ga yi masa faɗa, shi kuwa ko a jikinsa, dan gara ya ɓallo duk abin da zai ɓallo a san abin yi, duk abin da za a yi masa a yi masa, ya san yadda zai da matarsa da ɗansa.
*****
Kamar yadda Alhaji Fatuhu ya umarci Fadila,ta shirya tare da babbar 'yarsaJannat, suka tafi duba Hajiya Sa'a. Sai dai Hajiya Suwaiba ba ta je ba, saboda ba ta jin daÉ—i.
Ko da suka je, ƙin fitowa falo ta yi, sai su ne suka shiga cikin bedroom ɗin ta, suka same ta. Sai dai kamar yadda Alhaji Fatuhu ya ba ta labari, haka ta ga tsufan Hajiya Sa'a ya fito. Kamar ba ita ce 'yar ƙwalisar nan mai ado da kwalliya ba.
Suka gaishe ta, amma sai dai ta sake shiga halin É—imuwa ta kasa gane su, kawai dai ta amsa musu.
Fadila ta sauke Muhsin da yake bayanta, tana ba shi ruwa saboda daga bacci ya tashi. Hajiya Sa'a ta ƙura masa ido, har sai da ya lafe a jikin mahaifiyarsa yana kawar da kansa daga kallon Hajiya Sa'a.
Hajiya Sa'a ta ce "Da tuni wannan tsinannen É—an ne zai mutu, amma nawa É—an ya mutu, Allah ya isa ban yafe ba, kuma shi ma in Allah ya yarda sai ya mutu"
Cikin mamaki da rashin fahimta Fadila da Jannat suke kallonta.
Fadila ta ce "Tsinanne kuma Yaya Sa'a, me ya yi miki? Ba ki gane shi ba ne? Muhsin ne ɗan gurin ƙaninki Alhaji Fatuhu"
A fusace ta ce "Shi É—in fa, Allah ya tsine masa Albarka, shi ma Fatuhun Allah ya tsine masa Allah ya sa ya mutu. Da tuni Abba yana raye, amma bai sha alawar ba sai Abba ya sha ya mutu. Ke ma Allah ya tsine miki shashasha"
Waro ido suka yi gaba É—aya, cike da tsoro.
Jannah ta ce "Kin ga Anty, tashi mu tafi na fara jin tsoro, kar ta fara kai mana duka"
Babu shiri suka miƙe, Fadila ta goya ɗanta suka bar gidan, sai tsine musu take yi, tana faɗar wasu abubuwa da ba su gane kan abin da take nufi ba.
*****
Asal ta sha mamaki, ganin mahaifinta a gidanta wanda idan ba da wani dalili ba baya zuwa, sai dai yanayin fuskarsa ya sanya gabanta faÉ—uwa.
Kan ta yi magana ya ce "Hammad da gaske yake yana da É—a, domin na ga É—an nasa yau ido da ido, aurenki da shi bai amfana mini komai ba gurin cikar muradina ba, kaiconki da gaza cika wa mahaifinki burinsa"
A burkice ta ce "Wane Hammad É—in, yana tsare babu lafiya bai san waye a kansa ba ma?"
Cikin tsawa ya ce "Zan yi miki ƙarya ne? Daga cikin gidan Sultan nake, lafiyarsa ƙalau sai dai idan raina miki hankali suke yi, na yi magana da shi, kuma har ɗan nasa na gani da idanuna"
Hannu Asal ta É—ora a ka, tana lissafa maganganun da mahaifinta yake gaya mata. Da ta rasa mene ne gaskiyarsu.
Imam Hammad kuwa, tun da ya shiga ɗakin, ya hango Nana ta yi ruf da ciki a kan gadon, ga sautin sheshsheƙar kukanta na tashi. Ya rufe ƙofar ya ƙarasa gaban gadon da hanzari.
Ya É—ora hannunsa a bayanta ya ce "Ma vie" Tashi ta yi zaune idanunta jawur, ta ce "Ina Muhsin É—in?"
"Na mayar da shi inda yake. Ya na ji kamar jikinki da zafi ne? Meyafaru ma ki ke kuka? Wani ya shigo ne, ko an yi miki wani abu ban sani ba?"
"Ni ka mayar da ni gurin Nene, tun da ka samu lafiya"
"Yaushe na samu lafiyar? Ni ban samu lafiya ba tukuna, ba ki san me nake ji a jikin nan nawa ba" Yayi maganar yana ci gaba da shafa ta a hankali.
Cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya rayuwata, jikinki da zafi. Ga shi haushina ki ke ji kin ƙi yadda da ni, balle na ce ko Muhsin ne zai samu ƙani"
Nana ta ci gaba da kuka, da ita kanta ta kasa tantance kukan me take yi. Ya yi murmushi ya ce "Yanzu kishin ne ya saka miki zazzaɓi ma viee?" Ture hannunsa ta yi tana kuka. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "Da wasa nake miki, ban je ko ina ba fa da na bar ɗakin nan, a ƙofar ɗakin nan nake kwana, saboda idan mu na tare guri ɗaya akwai matsala ne. Ba kuma na son ɓata miki rai"
Kwanciya ta yi sosai a jikinsa, ta saka hannu ta zagaye bayansa ita ma, ta yi shiru tana mayar da numfashi. Ya din ga murmushi yana shafa bayanta ya ce "Ki yi haƙuri, ba na ƙaunar na din ga aikata duk wani abu da zai sanya mini ke fushi da damuwa. Je vous aime ina son ki rayuwata".
Nana ta ɗago tana kallon ƙwayar idonsa, idanunta fal hawaye.
Ya jinjina kai ya ce "Da gaske nake Asmy, ina yi miki so mai tsananin gaske. A jinina nake jinki ba iya zuciyata ba"
"Sayyid"
"Na'am rayuwata"
"Kar na sakankance da kai, 'yan uwanka su ce ba zaka zauna da ni ba, ban san ya zan yi ba Sayyid. Ba gudunka nake dan na daina sonka ba, tsoro nake ji. Na azabtu ko a iya haka a tsaya, ina son na samu nutsuwar ƙwaƙwawa da zuciya. Na kasance da abubuwan da za su sanya ni farinciki" Ta yi maganar a raunane.
"Ke jaruma ce Asmy, kar wani abu ya baki tsoro, kai da fata komai zai faru ina tare da ke, zan zaɓe ki da ɗana a kan komai, babu butulci tsakanina da ke, ai na san babu wani abu da zan yi miki da zai sanya na biya ki ko na kamanta abin da ki ka yi wa rayuwata ba. Kuma ina fatan a wannan karon za ki ba ni dama ki saurari uzurina, inda na yi miki kuskure kuma ki yafe mini. Ki bani dama mu ɗora ginin rayuwarmu rayuwa mai kyau da aminci"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.