Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 53 of 99
"Cherié, ba zai yiwu ki ɗaukko wadda ba hadima ba a cikin gidan nan, alhalin kin san kin taka dokar gidan mulki ba, sannan ki ce ta din ga saka kayan hadimai a nan ta fiki gaskiya."
Cikin mamaki Asal ta kalle shi za ta yi magana, amma ya ɗora yatsansa a kan laɓɓansa a dole ta yi shiru. Nana kuwa haɗa su ta yi, tai musu kallon banza ta wuce ta bar su a gurin. Sai dai kallon da ta yi musun, sai da ya kusa ɗimaucewa, ji ya yi tamkar ya bi bayanta. Wani murmushi ya saki ya nufi Asal yana lumshe ido ya ce "Ba girmanki ba ne, ki din ga sa'in sa da ma'aikatanki ai kin wuce nan".
"Amma ka na kallo a yadda take yi mini magana, kuma ka hana ni magana?" Ta yi maganar kamar za ta yi kuka.
Ya kamo hannunta ya ce "Yawan musayar yawu da na ƙasa da kai, raini yake janyowa, kuma kar ki yadda ki yi fin ƙarfi a abin da ba ki da gaskiya, nan ma raini zai din ga janyo miki" Ya ƙarasa maganar yana rungume Asal, amma a zahiri hanyar da Nana ta bi, ya bi da kallo ƙamshin turarensa da ta shafa ya ci gaba da karaɗa hancinsa.
Mahmoudu kuwa bai yi bacci ba, so yake ya tabattar da abin da idanunsa suka gane masa, gaskiya ne ba gizo ba.
Ya kira wayar Hammad, amma bai É—auka ba, ga shi tsoron zuwa gidan yake domin kar su haÉ—u da Nana, ya san komai zai rikice ne. Ga yaron da ya gani a gurin Ummansa, ga kashedin su Matawalle, ga kuma wannan abu da ya tarar.
"Anya yaron na ba É—an Hammad ba ne?" Ya tambayi kansa. Wayewar garin Allah ya din ga kiran Hammad a waya amma bai É—aga ba. Takaici ya ishe shi, sai can wajen Azahar sannan ya kira Mahmoudu.
"Tun jiya nake kiran ka ka ƙi ɗaga wayata"
Hammad ya ce "Ban jin daÉ—i ne, sai yanzu na duba wayar, ya ake ciki ne?"
Mahmoudu ya ce "A ina zamu haÉ—u, ina da magana da kai"
Hammad ya ce "Ina gurin Sultan, haryanzu bai sallame ni ba"
"Idan ya sallame ka, mu haÉ—u a saharar gidan tarihi mu sha shayi, zan nuna maka wani abu"
Hammad ya ce "To, saura na ga ba wani abin kirki ba ne, ba za ka yi mini ya jiki ba?"
Mahmoudu ya ce "To ya jiki Allah ya kiyaye gaba sai mun haÉ—u"
Hammad ya yi murmushi ya ajiye wayar.
Da yamma suka haÉ—u a sahara, lokacin rana ta yi sanyi.
Hammad ya ce "Sai wani nema na ka ke yi, me za ka bani?"
Mahmoudu ya ce "Babu komai shayi kawai nake son mu sha tare."
Hammad ya yi shiru yana kallon saharar, daga inda suke su na hango gidan tarihi, kuma suna hango wani sashe na gidan sarauta.
Ya na shan shayin a hankali yana son ya tuna wani abu, amma ya kasa.
Mahmoudu ya ce "Ya na ji ka yi shiru?"
"Ina tunanin yarinyar nan ne"
"Wacce?"
"Wadda Asal ta kawo, a matsayin mai yi mini girki, abubu da dama su na faruwa da na kasa gane kansu" Nan ya sake gaya wa Mahmoudu yadda ta hana shi hawan taguwa, da abubuwan da yake ji game da ita"
Mahmoudu ya ce "Kuma kai ba ka santa ba, baka taɓa ganinta ba ko a wani guri?" Ya ɗan yi shiru Sannan ya girgiza kai ya ce "A nan kawai na taɓa ganinta"
"Baka tuna komai ba, da muka zo gurin nan?" Nan ma ya girgiza kai duk da yadda ya ji kansa ya fara ciwo.
Mahmoudu ya ce "Gaskiya yakamata a ce duk yadda za mu yi, muyi bincike a kanta, mu san daga ina take, kar mu sakankance wani abin ya faru. Ka san ita kanta Gimbiya Asal ba ta yin abu babu dalili, kar mu je shirin Tafawa ne"
Hammad ya ce "Gaskiya ne, amma ta ce mini daga gidan cin abinci na MaraÉ—i ta É—aukko ta a gurin su Al-Husssain"
Mahmoudu ya ciro wayarsa ya daddana, ya miƙa masa ya ce "Ka ga wani ikon Allah"
Hammd ya sanya hannu ya karɓa, ya yi shiru ya zuba wa wayar ido. Jiki a sanyaye ya ɗago ya kalli Mahmoudu ya ce "Ina ka samo wannan hoton?"
"Samo shi na yi kawai na nuna maka"
Ya damƙe wayar da ƙarfi, ƙirjinsa ya yi masa nauyi ya ce "Mahmoudu kuma ka tabatta wannan ba ɗana ba ne ba? Duk wanda ya kalli wannan hoton zai yi zaton ma nine"
"Ka na da wata matar ne da zata haifa maka É—a? Ko kuma Asal ta haihu ne bamu sani ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Ko ɗaya, amma wannan yaron buzu ne, duk inda iyayensa suke ka nemo mini su a faɗin ƙasar nan"
"Me za ka yi musu?"
"Zan yi musu alkhairi ne kawai. Amma Mahmoudu kawai ji nake kamar ina da alaƙa da shi, dan Allah ka tura mini hoton nan"
Mahmoudu ya karɓi wayar ya ce "Zan tura maka" Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, ya kuma kasa shan shayin. Sule ne ya zo gurin a kan babur, ya kafe baburin, ya sauka ya gaida Hammad cikin girmamawa. Hammad dai ya amsa yana bin sa da kallo.
Suka gaisa da Mahmoudu ma, ya ga sun sake sun fara hira. Mahmoudu yana ta satar kallon Hammad, ko zai É—ago ya tuna wani abin, amma ya ga babu alamar hakan. Bayan tafiyar Sule, yake gaya masa ai abokin kasuwancinsa ne na Nigeria. Kawai ya jinjina kai.
Ƙaisar ne ya bayyana a gaban Giyaz, fuskarsa babu annuri ko kaɗan. Giyaz ya ɗaga kai ya kalle shi, ya ce "Ɗan samari ya dai?"
"Zuwa yaushe zaka ci gaba da wannan mugun wasan da ka ke yi?"
Giyaz ya ce "Wanne daga ciki?"
"Kowanne ma? Ka dawowa da mutumin nan tunaninsa ya tuna da yarinyar nan, ga ɗa a tsakaninsu ko iya yanzu ka ɗauki fansar ai, ka ƙyale ta ta huta haka?"
"Yaro yaro ne. Yarinyar da kakaninta suka cutar da mu, ta zo ta ƙona ni ta sanya ni jinya, ita ka ke tunanin na ɗagawa ƙafa ma sassauta mata?"
"Ba na son alaƙata da kai ta ƙara tsami, amma zan yi abin da ba ka zato, ba zan zuba ido ka ci gaba da cutar da ita har haka ba" Ƙaisar ya yi maganar cikin ƙunar rai.
Giyaz ya ce "To babu laifi, ka yi abin da duk za ka yi"
Hammad kuwa da ya koma gida, ya kasa zaune ya kasa tsaye, hoton yaron nan ya din ga kaiwa da komowa a cikin kwanyarsa. Yaya za a yi a ce a samu yaro yana irin wannan kamanin da shi, ba kamanni sama-sama ba, kamanni na zahiri nesa ba kusa ba. Bayan haka yaron ya yi masa kama da wani wanda ya sani ko ya taɓa gani, amma ya manta waye, ya din ga duba wayarsa ko Mahmoudu ya turo masa hoton yaron, amma wayam bai tuta masa ba.
Gefe guda ya so haÉ—uwa da Nana, amma bai ganta ba. Sai washegari da ta kawo masa Abincin safe ta yi masa ya jiki.
Ya ce "Sai yanzu za ki yi mini ya jikin?" Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, saboda wani irin kyau da ta yi masa. Ga ƙamshin da take yi, har wani ƙara nutsuwa ya yi yana kallonta.
"Tuba nake ranka ya daÉ—e" Sayyid É—in da take kiransa da shi, ya din ga kaiwa yana komowa a cikin kwanyarsa.
Haka da rana da ta yi shigar Atamfa, kamar ya sace ta ya gudu. Ta karya É—aurin É—an kwali, ta yi kyau.
Ya ce "Amm Asma'u ko?"
Ta jinjina masa kai duk da yadda ta ji Asma'un banbarakwai a bakinsa.
"Cherié ta ce mini a gidan cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ki ko?"
"Eh Sayyid"
"Me ya kawo ki Niger ne? Ko takanas ki ka nemi aiki da mu, tun daga Nigeria?"
Nana ta girgiza kai ta kalle shi ta ce "Abuna ne ya ɓata na zo Niger neman sa, ina son a yi mini izini, nan kusa na koma Nigeria"
Ya jinjina kai kawai ba tare da ya gama fahimtar abin da take nufi ba.
A daren ne kuma Nana ta jiyo kakarinsa, Asal ta fice ita kuma ta shiga É—akin.
Ƙara lafewa ya yi tamkar ya shige cikin ta, saboda daddaɗan sanyin da ya mamaye jikinsa. A hankali ya buɗe idanunsa, ya ji yadda ta ƙanƙame shi tana kuka. Ya saurara ya yi shiru ya ji ba muryar Asal ba ce. "Allah ka duba mu, ka yaye masa wannan ciwo, Allah ka yi masa maganin abin da yake damunsa. Yana jin yadda take shafa gashinsa tana ci gaba da kuka tana faɗin "Da gaske ba ka gane ni ba Sayyid, ko kuma wasa ka ke yi mini da hankali kawai. Na fara sarewa Sayyid, idan wasa ne ka tausaya mini haka, wahalar da na sha ta isa, ka duba ni ka duba makomar abin da na haifa maka dan Allah" Ta yi maganar tana ƙanƙame shi tana ci gaba da kuka. Gaba ɗaya sai ya rikice, bayan kukanta da maganganun da take yi da suka rikita masa lissafi, gangar jikinsa kuma wani saƙon take aika masa na daban, har wata tsuma ya fara yi. Sai dai Allah ya taimake shi, bai yi wani yinƙuri ba, ya ji tana magana da Ƙaisar, ta kwantar da shi a kan pillow ta koma gefe.
Tunani ya din ga yi ina Asal ta tafi? Ya aka yi Nana ta shigo har turakarsa kai tsaye haka, kuma wasu irin maganganu take yi haka? Ya yi lamo kamar bacci yake yi, amma idonsa biyu.
Sai gefin Asuba da ta bar ɗakin, ya tashi ya zauna, yana jin wani irin raɗaɗi a tsakiyar kansa, zuwa ƙirjinsa gaba ɗaya ji yake kamar zai fita hayyacinsa ƙwaƙwalwarsa na nema ta hargitse.
Garau ya miƙe bayan sallar asuba, ya sake tuna yaron da Mahmoudu ya nuna masa, da maganganun da ya ji Nana tana yi. Ya kira Al Hussain a waya, ya ce masa lallai yana son cikakken bincike a kan Nana.
Ga Sultan ya tura shi wakilicin wani É—aurin aure, amma kusan baya cikin cikakken hayyacinsa, kansa cunkushe da lissafi kala-kala. Maganganun Nana suka din ga karafkiya a cikin kwanyarsa, da rungumar da ta yi masa ba tare da tsoron komai ba.
Ko da ya dawo, har ya wuce É—akinsa, amma kansa ya din ga wani irin ciwo, kawai ya yanke shawarar zuwa ya turke Nana, ta yi masa bayani dalla-dalla.
Sai da ya bari Asal ta yi bacci, sannan ya tashi ya tafi É—akin Nana. Sai dai da ya je É—akin ya tarar ba ta ciki, sai wayarta da take kan katifarta a ajiye.
Har zai juya ya fita, kawai ya nufi kan katifar ya sanya hannu ya ɗauki wayar. Ya jujjuya wayar, yanayin yadda screen ɗin wayar ya dusashe ya sanya ya gane wayar ta kwana biyu. Kawai ya danna madannin gefe a take hoton fuskar Nana da Muhsin ya bayyana a kan screen ɗin wayar. Mutuwar tsaye ya yi zuciyarsa ta yi wani irin mummunan bugawa da ƙarfin gaske. Alamun tahowar Nana ya ji, babu shiri ya jefa wayar kan katifar ya yi sauri ya kashe fitilar ɗakin.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.