Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 10 of 99
Ayshercool
08081012143
80
Gaba É—aya kanta ya kulle, ta zuba masa idanunta da suka yi jawur.
A mugun kasanlance ta ce "Ciki kuma?"
Ya jinjina mata kai, ta rasa abin da za ta yi gaba É—aya. Ciki yaushe? Yaushe wani abu ya shiga tsakaninsu da har za ta É—auki ciki? Ta tambayi kanta, sai dai ta kasa tambayarsa. Sai tsare shi da ta yi da idanunta.
Ya gyara zamansa sosai ya ce "Kina ji na?"
"Babu abin da zan ji? Kar ka gaya mini komai, ba zan ji ba kuma ba na fatan ji. Abin da ka yi mini haka ma ya isa, ka bar ni na ji da kaina". Ta yi maganar a matuƙar zafafe.
Ya ce "Shikenan na ji. Na rabu da ke. Amma ina so ki sani, muddin ba ki saki jikinki ba, ki din ga cin abinci ki rage wa kanki wannan damuwar ba, to fa ba zan ba ki Muhsin ba. Gwargwadon sakin jikinki, da cin abinci da zaki yi, shi zai sanya ki gan shi. Akasin haka kuma zan ci gaba da tsare ki a nan, na kai wa Asal shi ta riƙe shi, tun da dama ita Allah bai ba ta haihuwa ba. Wannan ma idan ki ka haifa ki bani abina tun da ba za ki saurare ni ba" Kallon ba ka da hankali ta yi masa. Ya yinƙura da kyar, jikinsa babu ƙwari, ya ɗauki hiraminsa ya rufe kansa ya fice ya bar ɗakin.
A ɗaya falon ya tarar da Mahmoudu, cikin zaƙuwa ya ce masa "Yaya ta saurare ka kuwa?"
Jiki a sanyaye ya girgiza kai tare da zama ya ce "Fafur ta ƙi saurar ta, duk wani rarrashi da ban baki da zan yi, taƙi saurarta kawai na ba ta ɗan ta na sake ta ta nanata mini, na rasa yadda zan yi ko na minti ɗaya ta saurare ni. Babban abin da yake ɗaga mini hankali gani nake kamar da gaske Husna ta daina so na"
Mahmoudu ya girgiza kai ya ce "Ka yi haƙuri, ɓacin rai ne kawai ya sanya ta faɗar haka, amma a irin so da sadaukarwar da ta yi maka ba zai yiwu a ce ta daina sonka ba"
Ya tashi zaune sosai yana kallon Mahmoudu ya ce "Kana ganin idan ta huce, za ta ci gaba da so na kuwa?"
"Sosai ma, yanzun ma ɓacin rai ne kawai. Amma za ta ci gaba da sonka da zarar ta huce"
Ya koma ya kashingiɗa yana kaɗa ƙafafuwansa.
Mahmoudu ya numfasa ya ce "Yanzu Imam mene ne abin yi, na san fa yanzu ana can ana nemanmu, ta ina zaka fara Fuskantar wannan balahirar? Ta ina za a fahimce mu, akwai gagarumar matsala fa"
Ya ɗan kwaɓe baki ya ce "Wannan balahairar ba ta kai fushin da Asmy take yi da ni ba. Ni duk yadda za su yi da ni sai dai su yi. Ko su bar ni a raye ko ma su yanka ni, burina da fatana na ga ta haƙura ta yafe mini ta saurare ni."
"Yanzu soyayyarka gaba take da gagarumin tashin hankalin da yake gabanmu?"
"Nesa ba kusa ba kuwa, idan aka kamanata shi da zunzurutun soyayya mara algus É—in da na samu. Ko ka manta abu ne da nake nema ido rufe"
Mahmoudu ya ce "Turƙashi, to yaya za ka yi da Gimbiya Asal?"
Kawai ya saki murmushi, ya shafa sajensa.
"Au dariya ma na baka?"
"Eh mana, ni fa duk wannan masu sauƙi ne, ban ɗauke su matsaloli ba, zan gaya wa kowa gaskiya ko me za a yi mini sai dai a yi mini, ni fatana Asma'u ta yafe mini" Ya ƙarasa maganar cikin damuwa.
"Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah za ta saurare ka, ta É—auki zafi ne, amma tana hucewa za ta saurare ka"
*****
Doctor Sharif ne yake kallon matarsa cikin tausayawa, cikinta ya tsufa, amma sai fama take da rashin lafiya, duk da haihuwa ta biyar za ta yi.
A dole ya ba ta gado a Asibitin, cikin wata bakwai da sati É—aya, amma tana ta zubar da ruwa, ga matsalar numfashi da suga da yake hawa yana sauka.
Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Gida zaka tafi ka bar ni?"
Ya ce "Eh mana, ba ga Yaya za ta kwana tare da ke ba? Kin ga yara su na gida, ga shi gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta, dole na koma gida. Da na kai su school zan taho nan, duk wani abu da za a yi miki, na yi shi a rubuce duk za a yi miki"
Ta numfasa ta jinjina kai ta ce "To shikenan, sai da safe"
"Yauwwa Madam, ki samu isasshen bacci dan Allah"
"Idan na kwanta ne, baccin ko na fara sai na ji numfashina yana yi mini sama, kwanciyar babu daÉ—i sam"
"Na sani, ki yi haƙuri sai ki kwanta a side ɗin hannunki na hagu ko na dama"
Ta ce "To, sai da safe" Suka yi sallama ya tafi cike da tausayinta, wannan cikin tun yana ƙarami ya zo da tangarɗa yake wahalar da ita, ga shi ya tsufa ma amma ba ta daina wahala ba.
Hankalin Alhaji Zailani ya yi mummunan tashi, ganin sauƙi sosai da sosai a tattare da Alhaji Fatuhu.
Ga 'yan kasuwa sun yi masa caaa a ka, a kan lallai ba sa son shugabancinsa, sai dai ya sauka a canza wani. Ya tattara nutsuwarsa ya yi burusu da su, domin ba ya son ya rarraba hankalinsa, wani abin ya ƙwace masa.
****
Nana kuwa ji ta yi da gaske yunwa na ƙoƙarin hana ta sukuni.
Tashi ta yi ta fito, ta fara dube-dube. Yana daga inda yake tsaye yana kallon ta.
"Me ki ke nema ne?"
Firgita ta yi ta juyo tana kallon inda yake, ganin yadda yake ƙare mata kallo ne, ya sanya ta haɗe rai.
"Ina fatan ba wani gurin ki ke shirin tafiya ba, babu hanyar da za ki bi ki je ko ina"
"Ni ba guduwa zan yi ba, idan na ci Abincin yau za ka bari na gan shi?"
Ya yi murmushi ya ce "Ki ci É—in tukuna, Bismillah biyo ni" Jiki a sanyaye ta bi bayansa, cikin matsanancin tsoro, dan ganin shi take yi kamar wani mutum na daban.
Haɗaɗen bedroom ya kai ta, ta tsaya saroro tana kallon ɗakin, ta ɗaga kai ta kalli agogon ɗakin, ƙarfe ɗaya da rabi na dare.
"Zauna ki jira ni a nan" Ta tsaya tana kallon sa.
"Ki zauna mana" Ya yi maganar yana nuna mata bakin gado.
Ta yi ƙyam tana kallonsa. Bai sake ce mata komai ba, ya fita ta tsaya tana zazzare ido, tana ƙara ƙarewa ɗakin kallo. Ta gaji da tsayuwa, ta samu guri ta jingina da jikin bango, sanyin AC da yake ɗakin ya fara damunta.
Falon ta koma, tana nan zaune sai ga shi ya shigo da leda a hannunsa.
"Me yasa ki ka fito?"
"Sanyi nake ji" Ta ba shi amsa a taƙaice.
"Ohh yi haƙuri, mu je sai na kashe miki A.C" Ta girgiza masa kai tana sake haɗe rai.
"Shikenan, zauna ga abincin na samo" Ya yi maganar yana riga ta zaman.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.