Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 68 of 99

Sultan ya sassauta murya ya ce "Ki na ji na? Ba haÉ—a husuma ba ne ba, mijinki za ki taimaka tun da ke Allah ya yarje miki gano wasu abubuwan da mu ba mu gano ba"

Bakinta na rawa ta ce "Wannan mai kama shi ɗin, da ku ke yawan zama ku uku, mai saka shuɗin rawani, bayan ƙamshin turaren Gimbiya Bilkisu, ranar da muka zo nan, ƙamshin turarensa ne yake tashi, alamar bai daɗe da tafiya ba"
A rikice Imam Zahradeen ya ce "Sardaunan Agadez, ƙamshin turarensa ne"
Buɗe baki Sultan ya yi, ya fara numfarfashi yana kallon Nana, ya ce "Me hakan yake nufi? Ina fatan ba dai wani abin ya yi ba?" Nana ta girgiza kai cikin tsoro ta ce "Ba ni da tabbas, tun da kowa yana da damae zuwa gurin nan, mussaman a cikin manyan Agadez kamar yadda Imam Hammad ya gaya mini. Amma me zai kawo shi nan cikin dare wajen ƙarfe sha biyu na dare. Kuma a mudubin Ƙaisar na ga wani abu da ya sanya ban ji na yarda da ɗakin can ba, amma ba ni da tabbas tun da maganar aljani ba abar yadda ba ce ba wasu lokutan"
Sarkin baka kawai ya nufi ƙofar ɗakin, da Nana ta yi ta nacin a buɗe ta, yana zuwa ya jijjiga ƙofar, amma ya ga ƙaton mukulli a jiki.
A nutse ya ƙare wa sauran ƙofofin kallo, ya saki mukullin ya nufi hanyar fita, yana zuwa ya janyo mai gadin nan har zuwa inda su Sultan suke.
Ya kalle shi ido cikin ido Sarkin baka ya ce "Waye kai?"

"Mai gadin gidan tarihin Agadez" Ya ba shi amsa.

Sarkin baka ya ce "Kai, mugu shi ya san makwantar mugu. Kai da gani idanun nan nawa ka san babu abin da ban gani ba. Waye da waye suke zuwa gurin nan?"

Mai gadin ya yi wa Sarkin baka wani irin kallo, ya ce "Kowa ma yana iya zuwa"

"Ba kowan ba, muhimman mutanen da ka ke yi wa aiki"

"Ni ba ni da wani aiki bayan buÉ—ewa da rufewa, da kula da ababen tarihi"

"Ka tabattar?"

Ya ce "Eh"

Sarkin baka ya numfasa ya fito da jakar nan tasa, ya nuna wa mai gadin nan,ya ce "Idan hatsabibancinka ya kai ya kawo, na san ka san wannan jakar, ko kuma ka ji labarinta, mussaman da Jaddul Jinn ya yi rayuwa a cikin Masarautar nan. Wannan jaka ce da uwar gijiyar Ƙaisar ta farko, Lanti ta haɗa, da gudunmawar uban duƙusa, ta hanyar yin amfani da wani sashi na gashin Jaddul Jinn. Da abubuwa daban-daban da baƙaƙen aljanu ba sa so. Ana iya yi wa aljani tarko da ita, ko ma halaka su baki ɗaya. Yanzu za ka yi mana bayani ne, ko kuma na gwada maka aikin jakar nan, na hallaka baƙin aljanin kanka, na haɗa ka faɗa da Giyaz, sannan na kashe ka?"
Ya din ga kallon Sarkin baka, yaƙi magana. Nana ta ji sanyi ya fara ratsata.
Mai gadin ya ɗan ja da baya yana kallonta. Ta waiwaya ta ga me yake kallo, kawai ta ga Ƙaisar a gurin.
Jikinsa na rawa ya nufi ƙofar ɗakin, ya ciro wani mukulli ya buɗe, yana buɗewa wani irin wari ya daki hancinsu suka ja da baya.
Jikin Nana ya hau tsuma, Shi kansa Sultan ja ya yi da baya cikin tsoro, yana kallon gurin.
Sarkin baka ya tankaɗa ƙeyar mai gadin nan, suka shiga ɗakin. Ɗakin duhu kafin daga bisani kawai su ga haske ya gauraye ɗakin.
Sarkin baka ya waiwaya ya cewa su Imam Zahradeen su shiga.
Suka bi wata doguwar hanya, su na shiga suka wari yana ƙara cika musu hanci.
Ɗakin tsohuwar kurkuku ce, da daga baya a ka mayar da ita gurin aikin zinaren da ake haƙowa. Wannan kurkukun da aka din ga azabtar da mutane a zamanin sarakunan baya.
Gurin gwanin ban tsoro babu kyawun gani ko kaÉ—an.
Nana ta kurma ihu ta ja ta tsaya jikinta yana tsuma, saboda razana da kuma firgicin abin da ta gani.
Ƙwarangwal ne na cikakken mutum, an soke shi a jikin mashi, an kuma soke wani abu mai kama da takarda a jikin ƙwarangwal ɗin, da hotonsa a jiki yana ci da wuta, sai kuma sunan Imam Hammad Jalaludeen, a jikin abin mai kama da takarda an soke allurai a jiki. Sak abin da ta gani a cikin mudubin Ƙaisar. Jikinta ya din ga wata irin karkarwa, saboda razani da tsoro.
Shi kansa Sultan daskarewa ya yi yana rarraba ido, saboda razani da tsoro.
Sarkin baka ya ƙarasa gaban ramin, ramin ba mai zurfi ba ne ba, sai dai wasu irin manya-manyan itace ne a cikin ramin nan. Ya kalli jikin ƙwarangwal ɗin nan, ya yi baƙiƙirin saboda azabar wuta.
"Ya ka yi wannan sihirin?" Sarkin baka ya yi maganar yana tsare shi da ido.
Ya yi shiru.
"Wallahi idan baka faÉ—a ba, sai na jefa ka a ramin nan na kunna wutar"
Ya tsaya ya kalli ramin, ya rufe idanunsa ya faɗi wasu abubuwa, ya kalli ramin a take wata irin wuta ta tashi a cikin ramin. Wata irin ƙara ta din ga tashi a cikin ɗakin. Nana ta toshe kunnenta, ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta toshe kunnenta, ta fashe da wani irin kuka na tashin hankali da gigicewa.
Sarkin baka ya ce "waye ya saka ka wannan aikin, kuma yaya aka yi kana mai gadi ka ke bokanci?"
Ya numfasa ya ce "Na koyi bokanci ne, domin na rama abubuwan da aka yi wa zuriyarmu. Na bautar da mu tun zamanin kakanni.
Nana ta fara neman ta burkice musu gaba É—aya, saboda sama-sama da numfashinta ya din ga yi.
A rikice Sultan, ya ce Zahradeen ya fitar da Nana, kar wani abin ya same ta.
Su na fita ta nemi guri ta zauna ta sauke numfashi cikin matsanancin tsoro da razani.

*****
Mama ce a gaban Likita kamar ta yi kuka, ta yi ƙasa da murya sai magiya take yi masa.
Ya kalle ta ya ce "Hajiya muddin ba ki gaya mini gaskiyar abin da ya faru ba, babu wani abu da zan iya yi a kan 'yarki"
Cikin damuwa ta ce "Likita ka san ɗan yau ne, ka haife shi amma ba ka haifi halinsa ba, abin kunya ta kwaso mini, na yi na yi da ita a zubar ta ƙi, shi ne aka gaya mini wata ƙwaya na je na karɓo aka ce na saka mata guda goma a cikin kunu zai fita."
Ya yi zuru da ido yana kallonta, ya ce "Amma baiwar Allah ba ki da imani, kin san abin da ki ka aikata kuwa?"
"Dan Allah likita ka yi haƙuri,  ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka" Sai da ya yi mata faɗa kamar zai yi mata duka, sannan ya rubuta abin da za a yi wa Jamila.
Hajiya Sa'a kuwa, ta daina magana gaba ɗaya, komai sai an yi mata. Ƙarshe Asibiti aka sallame ta, ta koma gida, gidan kuma babu mai jinyarta, abin duk ya damu Alhaji Fatuhu amma babu yadda ya iya.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.