Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 4 of 99
"Na sani, ba na buƙatar ka musanta abin da na zo da shi, ka yi mini biyayya kawai. Kuma majalisa sun zartar da hukunci a kan Tafawa bisa abin da ya aikata"
Hammad ya kalli Sultan ya ce "Ina fatan ba wani abin mai tsauri suka yanke a kansa ba, kar alaƙa tsakanina da shi ta ƙara yin tsami, ga 'yar sa ina aure. Ko ba komai uba ne a gare ni, kuma Asal ƙanwata ce kuma matata"
Sultan ya girgiza kai ya ce "Kar ka damu, hukuncin ba zai shafi nasaba da dangantaka ba, ka je ka samu ka huta" Ya risuna cikin girmamawa ya yi godiya ya fita.
Bayan fitarsa Sultan ya zauna, zuciyarsa cunkushe da damuwa, tunani yake yi yaya aka yi Tafawa ya san batun larurar Hammad.
Ya yi tunanin ko Asal ce ta gaya masa, amma ko Asal ba ta san taɓin hankali Hammad ya yi ba, kawai dai ciwo ne yake kama shi, gangar jikinsa ta sauya, ya din ga wannan jijjigar da kakarin.
*****
Kaiwa da komowa Tafawa yake yi a cikin falonsa, zuciyarsa a cunkushe da baƙin ciki, bayan tuna yadda wasu daga cikin majalisar Sultan suka ƙaryata shi, bayan da ya faɗi cewa Hammad yana da taɓin hankali.
Ya yi ƙwafa ya ce "Da ni ku ke zancen, sai na tabattar wa da Duniya ɗan ka mahaukaci ne, sai ya yi hauka tuburan Duniya ta gani ta shaida, kujerar da ka ke ƙoƙarin cusa shi ya hau, sai ta zama haramiyarsa ta har gaban Abada. Mulkin ai ba da shi aka haifoka ba, da za ka ce lallai ka yi shi ma sai ya yi ba. A wancan karon mu na ji mu na gani, aka ɗora ka aka ce bamu cancanta ba, a wannan karon dole sarauta ta bar gidanka ta dawo gidana, Asadullah sai ya hau kujerar Sultan, ko ka na raye ko ka mutu".
*****
Tun da ya koma gida Asal ta share shi, shi ya manta ma abin da ya yi mata, ya ga tana basar da shi ga damuwa da yake ciki.
"C'heri'"
Ta É—ago ta kalle shi. "Me yake faruwa ne?"
Ta girgiza masa kai alamar babu komai.
"Idan na yi miki laifi ne, ki yi haƙuri, ina cikin damuwa ne kwanakin nan, ki din ga yi mini addu'a" Ya yi maganar yana hargitsa gashin kanta da ta gyara.
Ya nemi guri ya kwanta ya lumshe idanunsa, yana fatan bacci ya ɗauke shi, ko ya samu sauƙin wannan damuwoyin.
Yana jin ta ta kashe fitilar ɗakin, sai hasken fitila na gefen gado wanda ba mai takura ba ne. Ta hau kan gadon ta kwanta a bayansa, ta zura hannunta ƙirjinsa.
A hankali ya juyo, ya rungumeta sosai a jikinsa yana shafa bayanta, duk da ta ji haushin abun da ya yi mata ɗazu, amma da yake ya ƙware a iya mantar da mutum laifin da ya aikata masa, dole ta ba da kai bori ya hau. A hankali ya ji jikinsa ya fara ɗaukar zafi. Ya raba Asal da jikinsa saboda yadda yake jin san tamkar an saka masa fetur an kunna wuta a jikinsa.
Ya miƙe ya din ga kaiwa yana komawa a ɗakin, yana maimaita ya hayyu ya ƙayyum. Ya shiga banɗaki ya haɗa ruwan ɗumi ya yi wanka ya fito.
Kasa jurewa ya yi jin yana neman ya fita daga hayyacinsa, ya fita falo. Yana fita ya ji wannan dadaÉ—an sanyin ya ratsa shi. Kan sa tsaye ya nufi inda yake jin sanyin na fitowa wanda hanyar É—akin Nana ne.
A corridor din gurin ya yada zango, ya samu guri ya zauna, ya jingina da jikin bango yana numfarfashi.
*****
Kwanaki biyu a tsakani, aka kuma zama, sai dai a wannan karon ba da duka Imam É—in aka zauna ba, Hammad ne kawai, sai manyan masu faÉ—a a ji na kusa da Sultan, wanda an yi zaman ne saboda abin ya shafi Hammad É—in.
Sardauna ya yi gyaran murya ya ce "Imam Hammad, kamar yadda Tafawa ya buƙata da shi da wasu daga cikin 'yan majalissar Sultan. Lallai mu na buƙatar jin gamsashshiyar amsar ina zobenka na tambarin Imam yake? Gamsashshiyar amsa mai cike da hujja muke so, na wai-wai ko kame-kame ba, dan ka san muhimmancin zoben idan babu shi dole za ka sauka daga kan muƙamin da ka ke kai.
Abu na gaba, mu na buƙatar sakamakon rahoton lafiyarka, na tsawon lokacin da a ka ce ka shafe a faransa kana jinya.
Kuma hakan baya nufin za a canza umarnin da Sultan ya yi? Zuwanka faransa wakiltar Agadez wajibi ne bisa ga sahalewar Sultan.
Kai kuma Tafawa, duk da uba ne kai ga Imam Hammad, kuma uba a Agadez za a hukuntaka bisa ɗaga murya da yin jayayya da hukuncin da Sultan ya aiwatar, kamar yadda kwamitin ladabtarwa da sulhu ya yanke. Zaka kawo mana cikakkiyar shaida da hujja, ba wai-wai ko kame-kame ba, a kan Imam Hammad yana ɗauke da larurar ƙwaƙwalwa, akasin haka za'a yanka maka tara mai yawan gaske ka biya shi.
Haka zalika an hukuntaka bisa amfani da kausasan laffuza a kan Imam Hammad, wanda yake shugaba ne da yake jagorantar Imam, da ake sanya ran zaman su sarakan gobe. Dan haka an dakatar da kai tsawon watanni shida, har sai ka gabatar da abin da aka nema daga gare ka"
Cikin fusata ya miƙe ya ce "Ai dama na sani, wata maƙarƙashiyar da manaƙisar ake ƙulla mini, saboda ba a ƙaunata. Amma shi Jalaludeen ya musa cewar ɗansa mahaukaci ne mana. Ciwon hauka ya yi suka kai shi suka ɓoye amma aka ce jinya ya yi a ƙasar waje. Ba ku burge ni ba da ba sauke ni kuka yi daga muƙamina ba har abada ai.
Kuma na faɗa na maimaita, Hammad ba zai taɓa zama Sultan a Agadez ba, ba shi da lafiyar zuciya, ba shi da ta ƙwaƙwalwa kuma ba shi da magaji juya ne, dan haka mai baƙin baya ba zai yi mulki a Agadez ba"
Wani irin duka Hammad ya yi wa teburin gabansa da ya bayar da wani irin sauti.
Ya kalli Tafawa ya ce "'yar ka zaka tuhuma ya aka yi ba ta haihuwa? Ni mahaukaci ne ka zagaye Agadez kana maimaita hakan, kuma ba ni da lafiyar zuciya shi ma ban damu ba, na yi sarauta ko kar na yi bai dame ni ba, duk abu dai ka san kujerar Sultan ta fi ƙarfinka. Duk abin da za ka faɗa a kaina ka faɗa amma kar ka sake kira na da Juya mai baƙin baya, Asal ita ce juya ita zaka bincika dan ni ina da ɗa, na haihu ba baƙin baya ne da ni ba! Zobe kuma ya ɓata ban san inda yake ba" Ɗif gurin ya yi, tamkar an yi ruwa an shanye, ko kuma babu mai sauran numfashi a gurin, saboda yadda maganganun nasa suke buƙatar fashin baƙi gwari-gwari.
*****
Hajiya Amina cikin damuwa da nuna rashin jin daÉ—inta take duban Alhaji Zailani ta ce "Alhaji ban ji daÉ—in yadda ka yi wa yaron nan mijin Shukura ba. Tare da mu da shi ake ta faÉ—i tashin neman Shukura, bai kamata a ce gaya masa maganganun da suke nuni da cewar wai zarginsa ka ke yi da sace Shukura ba"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.