Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 2 of 99
Da sauri ta ce "Amm ranki ya daÉ—e, na ce dan Allah.. sai kuma ta yi shiru kar ta tambaye ta, ta canza mata fassara.
Asal ta ce "Ina sauraren ki"
"Amm shikenan ba komai" Asal ta yi gaba ta yi waje abin ta.
Gaba ɗaya hankalin Nana ya ƙi kwanciya, ba ta san a hannun wa wayar take ba, ba ta san ta ina balli zai tashi ba, tun da wayar babu security a kai.
Ba kuma ta tunanin ma'aikatan gidan, saboda ba su da ikon shiga wannan sashen.
*****
Gaba ɗaya su ke zaune cikin shiga ta alfarma ana tattaunawa, Sultan ya ce "Ina mai farincikin sanar da ku cewa kamfanin masarauta na zinari, zai shiga wata yarjejeniya da ƙasar faransa a kan zinari da kuma sindarin uranium da muke haƙowa. Dan haka ina ganin sai mu tura Imam Hammad da Omar, su je su karanta tsarin yarjejeniyar.
Sai kuma a nan gida mu na da taro shi ma, a kan yadda zamu bunƙasa harkar safarar raƙuma da muke yi zuwa ƙasashen ƙetare. Akwai buƙatar fito da sabbin hanyoyi na ƙara faɗaɗa kiwon su da kuma shige da ficen su. Ina ga wannan da kaina zan je taron tare Imam Asad, Zahradeen"
Tafawa Maleek ya ce "Wai dan Allah Jalaludeen ba ka jin nauyinmu da ka ke fito da son zuciyarka da son kan ka ƙarara a gaban jama'a?"
Gaba É—aya suka É—aga kai su na kallon Tafawa.
"Za ka tura ɗanka yarjejeniyar Zinari da sinadarin uranium, mu kuma ka haɗa ka 'ya'yanmu da harkar raƙuma"
Abduou matawalle ya ce "Tafawa, yakamata ka san abin da ka ke faÉ—a fa, Sultan ka ke yi wa magana"
"Ban saka da kai ba, da É—an uwana nake magana" Tafawa ya yi maganar yana dakatar da Matawalle.
Sultan ya yi murmushi ya ce "Ba abin da ka ke zargi ba ne Tafawa. Hammad ai É—anka ne, kuma ni duk matsayinsu É—aya a gurina."
"Ba matsayinsu É—aya ba, me yasa ba ka tura Zahradeen ba sai shi, mutumin da ko cikakkiyar lafiya ba shi da ita?"
Imam Zahradeen ya ce "Mai girma Tafawa, da ni da Imam Hammad ai duk É—aya ne, ni dan ya je masarautar Agadez ya wakilta babu wani abu a ciki"
"Yi mini shiru, kai har ka na da zarafin da ina magana da babanka ka din ga sanya baki? Ni na gaji da wannan bambanci da ka ke nunawa, sai ƙoƙari ka ke lallai sai ka tura ɗanka kan kujerar Sultan ta ƙarfin tsiya, bayan bai cancanta ba. Shi ba cikakkiyar lafiyar zuciya ba, ga rashin lafiyar ƙwaƙwalwa, kalli yatsunsa babu zobensa na tambari, ga shi tsawon shekaru da aure ba shi da magaji, ta yaya ka ke tunanin makaho ya jagoranci mai idanu? Ta yaya mutumi da shi kansa ba zai iya tsayuwa da ƙafarsa ya yi rayuwa ba za a ce ya wakilci masarauta kamar Agadez a harkar kasuwanci"
Cikin tsawa Sardaunan Agadez ya ce "Wane irin lafazi ne wannan ka ke yi Tafawa? Kar ka manta da wanda ka ke magana, babu ruwan masarauta da gaba ka ke da Sultan, zamu iya sanyawa a warware rawaninka a hukunta ka. Hammad ba É—anka ba ne kai ma? 'yar ka fa yake aure, kuma É—an É—an uwanka ne, kai ba mai rufa masa asiri ba ne idan ma hakan ne? Batun zoben sa zamu yi bincike a kai, haihuwa kuma Allah ne yake bayar da ita, bai zama hujjar da za a ce an hana shi wata dama ba. Ko yana da É—a ko babu idan Allah ya nufi ya yi mulkin Agadez wallahi sai ya yi" Gaba É—aya gurin suka yi tsit.
Ya mayar da idonsa ga Sultan cikin girmamawa ya ce "Ina neman afuwa ya shugabana bisa É—aga murya da na yi a gaban sarki"
Hammad ya dubi Sultan a tsanake ya ce "Ina neman a yi mini izini, zan ɗan fita" Da ka Sultan ya yi masa alama, ya yinƙura ya tashi ya fita.
Zuciyar Sultan tamkar ta kama da wuta saboda damuwa da jin zafin kalaman É—an uwansa ga É—an nasa.
Kai tsaye Imam Hammad ya koma gida, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi na maganganun da Tafawa ya faÉ—a a kansa.
Ɗakin saukar baƙinsa ya wuce, da nufin ya zauna ya kaɗaice a ciki. Kawai ya tarar da Mahmoudu a ɗakin.
Bai kula shi ba kawai ya nemi guri ya zauna idanun nan jawur.
Mahmoudu ya tashi ya koma kusa da shi, ya kalli yadda idanunsa suka yi jawur ya ce "Imam, lafiya kuwa?"
Yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Mahmoudu, ina son na roƙi Sultan ya cire ni daga duk wani abu da ya shafi harkar mulkin nan ba na so"
Mahmoudu ya waro ido ya ce "Saboda me? Kai ma ka san abin da ba zai yiwu ba ne ai. Ka riga ka kai matsayin Imam kuma ka san me hakan yake nufi"
"A cire ni a maye gurbina da wani, tun da akwa masu so. So nake na yi nesa da gidan nan, na samu nutsuwa na yi rayuwata cike da 'yanci yadda babu wanda zai dame ni ya takura mini. Gidan nan ji nake yi tamkar a kan wuta nake. A kan abin da bai taka kara ya karya ba an ci mini mutunci ana ce mini juya. Ni Tafawa yake ci wa mutunci saboda kawai Sultan ya ce na je faransa na wakilci masarauta? Wallahi wataran za su neme ni su rasa"
"Mahmoudu a ransa ya ce wancan karon ma da ka gudu ni ka saka a bala'i'
A zahiri ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri, duk inda ka je ma ba zaka iya zama ba sai ka dawo, dan Allah ka yi haƙuri"
Ya yi wa Mahmoudu shiru, ya lumshe idanunsa.
Yana kwance a kan cinyarta, ya zuba mata idanu yana kallonta. Sai shafa gashin kansa take yi tana yi masa murmushi mai ƙayatarwa. Bai yi mata magana ba, ita ma ba ta yi masa ba, amma yanayin ya yi masa daɗi sosai da sosai.
Wata babbar mace ce a zaune, tana ta huci tamkar za ta fashe, cikin takaici da ƙunar rai take kallon matashin saurayin da yake gabanta.
"Zahradeen wai kai wane irin mutum ne mara kishin zuci da bai san ciwon kansa ba? Ina nan na samu labarin ka na cewa Sultan wai a tura Hammad wakilci kai da shi duk abu ɗaya ne, a gidan uban wa ku ke abu ɗaya, ana ƙoƙarin nemo muku 'yanci, amma kai kana shirme da shiririta?. Ƙarara Sultan yake nuna bambanci a tsakaninku ammma kamar ya yi maka asiri ka zama nusari. To wallahi ni ba nusara ba ce, ban tsaya tsayin daka ka zama Imam ba, sai dan ka zama Sultan ɗin Agadez. Dan haka ba zan zuba ido shashancinka ya ɓata mini wahalata ba na gaya maka".
Zahradeen ya yi shiru bai ce komai ba, shi sam bai ga wani abu da Sultan yake yi na nuna fifiko a kan Hammad ba, kawai yana ba shi kulawa ta musamman ne, saboda yanayin matsalar hawan jini da yake da ita, da kuma rashin mahaifiya.
Aka ci gaba da dambarwa, a kan tafiyar sa Faransa.
Ko da aka koma zaman tattaunawa, Mayan 'yan majalisar Sultan ra'ayinsu ya kasu biyu, wasu su na goyon bayan a tura Hammad, saboda nagartarsa da jajircewa ya cancanta mussaman da duk ya fi sauran Imam Imam ɗin ilmi da mu'amala, ga yarurruka da yake ji. Ya yinda wasu suka goyi bayan Tafawa a kan Hammad ba zai ce wakilci Agadez ba, sai sun ji ba'asin zobensa, sai kuma sun ji matakin lafiyar ƙwaƙwalwarsa. Da rahoton lafiyarsa na tsawon shekarun da ya yi a faransa.
Wannan ƙa'idoji da suka shimfiɗa ƙa'idoji ne da sai an kwashe lokaci kafin cika su, wanda har lokacin taron ya zo ya wuce, ba a kammala cika su ba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.