Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 58 of 99

****
Nana bayan sun idar da sallar asuba, ta ɓungire ta hau bacci, saboda yadda suka kwana jiya babu bacci. Ya zauna a gabanta ya zuba mata idanunsa, yana jin tamkar ya haɗiyeta ya din ga jinta a cikin jikinsa. Me zai yi wa wannan halitta domin nuna mata ɗumbin godiyarsa da farincikin kasancewa da ita. Ƙarshe ya ɓuge da sumbatarta yana shafa fuskarta, daga bisani ya tashi ya fita.
Sashen Gimbiya Bilkisu ya wuce, ya tarar ba ta fito ba, ya wuce ɗakin da yake kyautata zaton Asal tana ciki. Aikuwa tana ciki ɗin fuskarta ta kumbura suntum ta yi jawur, idanunta sun yi wani irin kumburi mai ban tsoro. Jikinsa a sanyaye ya ƙarasa gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ta kawar da kanta gefe ta yi shiru, ji take kamar ta shaƙe shi ya mutu ta huta.
"Asal" Ya kira sunanta. Ta ɗago ta kalle shi a ƙule.
"Ina roƙon ki da kar ki ɗauki damuwa da tashin hankalin lamarin nan ki saka a cikin ranki. Duk abin da ya faru a cikin rayuwarmu abu ne da Allah ya riga ya ƙaddara"

"Hammad ba na son jin komai daga gare ka, ka tashi ka tafi ka bani guri. Macuci ma ci amana, ba ka ji daÉ—in halinka ba"

Ya ce "Na ji na kuma yadda, duk abin da za ki kira ni da shi na karɓa, na san kina cikin fushi ne, amma ina mai roƙonki kar wani ya ziga ki ko ya tayar miki da hankali aurenmu ya samu matsala"

"Ka riga ka haifar da matsala a cikin aurenmu da kanka, matsalar da ba ta da magani. Har ka yi aure ka haihu ko Hammad, ba ruwanka da matsala ta kanka kawai ka sani. Ka tashi ta fita ka bani guri. Kuma wallahi ina mai yi mka rantsuwa da Allah, sai na yi mata mummunar illar da ba zata moru ba, sannan in saka a hallakata sai ta san ta jangwalo rigima mafi girman da ba zata iya tare ta ba a rayuwarta. Wallahi Hammad kai nawa ne nikaɗai ni Asal ba zan yi tarayya da ƙasƙantaciyar mace a koma mene ne ba"
Ya yi murmushi ya ce "Ni dai ina roƙonki ki kwantar da hankalinki, kar ki biye wa zuciyarki dan kaf cika da batsewar Agadez ke Niger gaba ɗaya babu mahalukin da zai raba ni da matata da ɗana. Dan gara na bar muku Agadez ɗin da mulkinku na bi farin ciki da kwanciyar hankalina. Ba zan taɓa wulaƙantaki ko na yarda a wulaƙantaki ba, saboda matata ce ke kuma 'yar uwata. Amma wallahil azim duk abin da ya samu Asma'u ba zan ɗaga wa kowane mahaluki ƙafa ba, a kanta komai kusancina da shi kuwa, dan Asma'u rayuwata ce, dole kuwa na bawa rayuwata dukkan wata kariya dan babu gangar jikin da take fatan rabuwa da ruhi"
Wani irin kukan kura ta yi, ta din ga kai masa duka ko ta ina, tana gaya masa maganganu masu zafi, amma ko gezau kawai ya tsaya yana kallonta. Gimbiya Bilkisu ce ta shigo da gudu tana tambayar ko lafiya saboda jin ihun Asal da ta yi.
Ta ƙaraso ta rirriƙe Asal ta ce "Imam me ka yi mata?"

Ya ce "Babu abin da na yi mata"

Asal cikin gunjin kuka ta ce "Ammi ya cuce ni, ya bar gida tsawon lokaci ya je ya yi aurensa a ɓoye ya haihu ban sani ba, sai dai na ji zance sama taka, kuma yarinyar da na kawo a matsayin kukunsa. Wataƙila ma shirya komai suka yi, an cuce ni am zalunce ni, wallahi Ammi ba zan zauna da wata ba. Ya aka yi na fara son shi na bari son Hammad ya yi mini illa. Ni yake gaya wa kaf Agadez babu mai raba shi da waccan ƙasƙantaciyar halittar wallahi sai na kashe ta"
Gimbiya Bilkisu ta rungume Asal ta ce "Yi shiru ki daina magana, ki daina faÉ—ar wannan maganar. Ki kwantar da hankalinki"
"Ammi zuciyata ciwo take yi mini, ko ganinsa ba na son yi, ya tashi ya tafi ya bani guri"

Gimbiya Bilkisu ta numfasa ta ce "Imam, ina ga kamar yadda ta buƙata ka tashi ka tafi kawai, ka bata lokaci ta samu nutsuwa. Domin magna ta domin Allah ba ka kyautawa Asal ba, dole ta shiga damuwa da tashin hankali"

Hammad ya ce "Allah ya taimake ki, kar ki zaɓi Asal saboda 'ya take a gurinki, a zamana da ita har zuwa abin da ya faru ban zalunce ta ba.
Cikin ƙaraji Asal ta ce "Ammi kin ji ko? Kina jin abin da yake faɗa"
"Imam ka tashi ka je kawai" Ya miƙe tsam ya fice daga ɗakin, Asal kuma ta ci gaba da kuka.

Fita ya yi, ya nufi wani sashi na gidan, ya yi umarnin a je a zo masa da Sarkin baka.
Yana nan zaune hadimai biyu suka shigo, tare da Sarkin baka, ya tarar da Hammad fuskar nan a É—aure tamau babu annuri.
Sarki ya ce "Barka da wannan lokaci"

Hammad ya amsa da yauwwa barka.

Ya ɗora da cewa "Ammm duk da zan iya cewa baƙon Sultan ne kai, amma saboda ni aka kawo ka gurin nan, kuma ina tunanin ina da damar yin magana da yanke wa kaina hukunci"
Sarkin baka ya ce "Wannan gaskiya ne"

"Ina ganin tun da babu wani abu da ya yi saura, ka ce ba zaka iya yi mini magani ba, yakamata ka yi magana da Sultan a sallame ka ka tafi"

"Saboda ba ka son na kula matarka ko?" Hammad ya yi shiru yana kallon Sarkin baka.
Sarki ya yi murmushi ya ce "Ai duk taka tsantsan ɗinka ina da yaƙinin Nana ta fika, kuma ko da take yi mini kallon ba a kan daidai nake ba, ta san ni ba mutumin banza ba ne. Wannan gidan naku ba zan taɓa tafiya na bar Nana a cikinsa ba saboda balahirar da na gani a gidan"

Ya kalli Sarkin baka ya ce "A matsayinka na wa?"

"A matsayina na ɗan uwanta, ba ka san ina da alaƙa da ita ba? Duk da na san zaka kalli alaƙar ba wata ta kusa ba, amma a yadda ba ta da kowa a cikinku daga ahalinta ina ga zan wakilci ahalinta a nan. Ina da dangantaka ta kakannin kakannin da ita. Ka kwantar da hankalinka ni ba zan cutar da kowa ba, ko na shiga tsakaninku ba amma dole zata buƙace ni, idan kuma ka bari na tafi wallahi ba zan dawo ba bar abada kuma hakan ka iya zame muku matsala. Kuma ya zama dole ka bata duk wata dama ta ganawa da ni a duk lokacin da ta buƙaci hakan, ta nan ne za a iya samun warwarar abubuwan da suka baibaye ka. Ba na son a ji daga bakina ne, kuma ina son ta fahimci akwai abin da idan yana cikin ƙaddararka ba ya nufin ka saɓa wa Allah, amma Allah na iya amfani da kai ya kawo wa wani bawan nasa mafita" Hammad ya yi shiru yana jujjuya maganganun Sarkin baka, duk da ba komai ya gane ba. Amma ya numfasa ya ce a mayar da Sarkin baka masaukinsa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.