Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 42 of 99

Hammad ya numfasa ya fara nuna mata hotunan nan da bayaninsu ya ce "Kamar yadda yake a babban kundin adana tarihin masarautar Agadez, wannan shi ne Kakan Sarki Azhar, ga mahaifinsa, shi ma ga hotonsa, ga 'ya'yansa ga waÉ—anda suka yi sarauta a cikin 'ya'yansa.
Wannan ita ce Gimbiya Saira, ita ce matar Sultan Azhar, da tun da ya mutu zuriyarsa ce kawai suke Mulkin Agadez ba a sake samun wanda ya ƙwaci mulki daga hannun zuriyarsa ba.

Nana ta tsare shi da ido, har sai da ya tsargu ya ce "Lafiya kuwa?"

"Sayyid, kana nufin ka na ta'amalli da Aljanu kenan, ta hanyar yin amfani da wannan zoben?"

"Meyasa za ki yi tsalle ki tafi ƙarshen labarin? Ki jira na kai da kaina mana"

AREWABOOKS

Ta É—an nutsu tana sunkuyar da kai.
Sai dai ya yi shiru bai ci gaba ba. "Yaya ka yi shiru kuma?"

"Ba na son na ci gaba ki yanke mini hukunci ne haka sama ta ka"

"Ka yi haƙuri ba zan yi haka ba, in sha Allah na yi shiru har ka kammala"

Ya kamo hannunta, suka fito daga cikin wannan É—akin, ya nuna mata wani É—akin ya ce "Wannan É—akin, shi ne inda gawarwakin galibin tsofaffin sarakunan Agadez suke, na kusa da shi kuma É—akin da a kan binne manyan masu faÉ—a a ji. Ba zan buÉ—e miki ba dan za ki iya tsorata.
Ya buÉ—e wani É—akin ya ce "Nan É—akin kuma, shi ne É—akin da ake sarrafa zinari, a cikin fadar Sultan yake. Duk nacin mutum bai isa ya saci zinare ya fita da shi ba, idan kuwa aka kama mutum a kurkukun nan zai mutu.
Wannan ɗakin kuma, a ciki duk wani tarihin yaƙe-yaƙen da Agadez ta yi yake. A nan ake adana duk wani kayan Sultan muhimmai, irin su takalmi, kayan yaƙi takobi da sauransu. Shi kuma wancan ɗakin, wasu daga cikin sassan ƙashi. jikin manyan masu laifukan da aka kashe ne, da Sarakunan da aka yi wa juyin mulki aka kashe su.

Zamani ya ci gaba da jujjuya, hasken addinin Musulunci ya fara bayyana, duk da nisan da Sarakunan ƙasar suka yi ba sa jin kira, dan hatta turawan mulkin mallaka ba su yadda sun kassara musu sarauta da tattalin arziki ba.
Tasirin addinin musulunci ya sanya aka fara rage aikata wasu abubuwan, amma ba a daina wasu ba. Tsaface-tsaface da ta'amalli da Aljanu ba a daina su ba, ga su mutane masu tsatstsauran ra'ayi a kan al'adunsu, da tsafi. Domin ma'abota sarauta sun yarda da cewa, duk wanda ya zauna zai ga zama, mussaman yadda zuriya daban-daban suke farautar kujerar ko ta halin ƙaƙa duk da tushen ɗaya ne, amma kowa burinsa ya zamana Mulkin a gidansu yake.
Sai dai dokar Sultan Sadam tana nan, ta sai wanda bai kai shekaru talatin da biyar ba ne zai yi mulki, sannan sai wanda yake da zoben nan shi ne zai yi mulki.
Sai dai a baya-baya, aka samu ɓarkewar faɗa a tsakanin zuriyar Azhar, har aka yi ƙaramin yaƙi, suka zubar wa da juna jini, abin da ba a taɓa yi ba a tarihin masarautar. Abin a ya girgiza al'ummar ƙasar mussaman ma'abota sarauta, har suka fara tsoron ko ƙarshen masarautar ne ya zo, aka samu rikicin da ta kai ga 'yan uwan junan da tun zamanin iyaye da kakanni ba su taɓa samun rabuwar kai da ta kai ga amfani da makami ba sai a wannan karon.
A lokacin zuwan ilimin addini da na zamani, da kuma wannan hatsaniya da ta faru, sai aka yi wa dokokin masarautar Agadez kwaskwarima. Domin samar da zaman lafiya da ƙara ƙarfafa masarautar sai aka ce sai wanda yake da wasu nagarta da wasu abubuwa masu muhimmanci shi ne zai zamana yana riƙe da zoben a kowanne gida da suka gaji zobunan. Sannan aka ƙara yawan zobunan suka zama uku, kowane gida su na da anihin zoben tambari wanda shi ne mai ɗauke da sihiri da aljanu sai kuma sauran biyu, sannan da abin hannun na tagulla. A zamanin Sultan Ansar, aka yi duk wannan sauye-sauyen, ya ƙirƙiro ƙaramar majalisar masu ɗauke da wannan zobunan, yadda za a din ga shigar da su cikin sha'anin mulki, da koya musu yadda mulki yake. Aka yi yarjejeniya a kan iya wannan masu zoben ne za su iya zama Sultan, sannan a cikin su duk wanda ya haura shekara talatin da biyar za a karɓi zoben daga hannunsa a nemi wanda ya cancanta a ba shi.
A lokacin aka ce duk wanda zai mallaki zoben, domin zama ɗaya daga Imam, kamar yadda Sultan Ansar ya yi musu laƙabi da shi, dole ya zamana yana da ilimin addini, ya haddace kaso saba'in na tarihin Agadez, yana jin wasu yarurrukan bayan yaren su na uwa, da kuma hausa. Domin ya zamana mutanen Agadez su na jin Hausa sosai, saboda yanayin cinikayya da ke tsakaninsu.
Sai dai har a lokacin akwai baƙaƙen al'adunsu da ba su canza ba, kuma ba a yi wa kwaskwarima ba, ba a daina azabtar da mutane a kurkukun nan ba. Sannan su na ƙyamar ɓakar fata, ta kowace fuska sun daƙile baƙaƙen buzaye, sun bautar da su, sun hana su motsi, dan kar su yi wani yinƙuri su yi musu juyin mulki. Ko a cikin kuyangi, ba a yarda basarake ya yi amfani da baƙar buzuwa ba, saboda kar su haɗa zuriya da su, su sanya ran za su samu 'yanci wataran. Kuma baƙaƙen bayi sun taka muhimmiyar rawa gurin gina daular Agadez, da haɓaka tattalin arzikinta, saboda juriyarsu da aiki tuƙuru. Sun daga lokacin da suka yi 'yanci, za su iya ajiue aikace-aikacen, kuma su na tsoron su ce za su rama bautar da su da aka yi tun zamanin iyaye da kakanni alhalin kakannin kakanninsu, da su aka kafa Daular kuma sun taɓa mulki.
Hukunci na iya zama na kora, zaman kurkuku koma kisa, ga duk basaraken da aka kama, da aure ko mu'amala da baƙar buzuwa. Haka duk cinikayyar da suke yi da sauran ƙabilu, ba su yadda auratayya ta haɗa su mussaman da baƙar fata, nasu ma ba su aura ba balle na waje. Sannan yana daga sharuɗɗan da bokaye suka kafa musu, muddin suka yi auratayya da baƙaƙe, ana iya kawo ƙarshen mulkinsu, kuma baƙaƙe ka iya yin galaba a kansu, su ƙwace sarautar baki ɗaya.
Zamanin Sultan Ansar bayan tabattar da waÉ—anann dokoki, shi ma yana da zobuna da abin hannun tagulla na waÉ—anda za su zama Imam.
Lokacin da aka tabbatar da waɗannan dokokin, aka yi musu kwaskwarima, Sultan Ansar yana da tarin 'ya'ya, yana daga cikin dalilan da ya sanya shi ƙara inganta tare da gyara wasu dokokin saboda yana kwaɗayin ɗansa Jalaludeen ya zama Sultan a bayansa, saboda kusan duk abin da aka lissafo yana da su. Kuma ya lura akwai zalamar son Mulkin sosai a wasu daga cikin 'ya'yansa, mussaman babban ɗansa Saifuddeen.
'Ya'yan suka yi ta zuba ido, domin su ga wa zai ba wa zobunan nan, amma ya ƙi bawa kowa, sai daga bisani ya damƙa wa Jalaludeen, ya nemi sauran gidajen da suke da zobunan, su ba wa waɗanda suka zaɓa, a kafa majalisar Imam. Hankalin Saifuddeen da mahaifiyarsa da sauran 'yan uwansa ya yi mummunan tashi, ganin ya ɗauki zobunan tambari ya ba wa Jalaludeen, duk da ga yayyensa.
Sai dai maimakon a samu Imam shida, sai aka samu biyar aka rasa inda sauran zobunan suke.
Hankalin Saifudeen ya ƙi kwanciya, ya tashi hankalinsa da shi da mahaifiyarsa da wanda suke ɗaki ɗaya, a kan lallai su san yadda za su yi, ko dai a karɓe zoben nan daga hannun Jalaludeen, ko kuma a kashe shi. Sai dai suka fahimci karɓe zoben nan, ba abu ne da zai yiwu ba, saboda ya riga ya mallaki Aljanun da aka wakilta tasrifi da zoben.
Duk wani Imam da yake Agadez, askin gashin kai ya haramta a gare shi, haka zalika barin gashin kansa ya haramta. Sannan babu su babu baƙaƙen bayi, a matsayin kuyangi. Sannan akwai nau'in abincin da ba za su ci ba.
Bayan majalisar Imam ta kafu, da yawa sauran zuriyar, sun shiga taradaddin ina É—aya zoben ya shiga?.
A dole Saifudeen ya ɓoye hassadar da yake yi wa ɗan uwan nasa, ya ci gaba da ƙoƙarin ganin bayansa ta ƙarƙashin ƙasa. Ya din ga bin bokaye, har da na wata ƙasar a kan a haukata ɗan uwan nasa, ko ma a kashe shi, saboda shi ne ya fi dacewa da matsayin da yake kai, amma abu ya ci tura.
Wataran Sultan Ansar ya kira Imam Jalaludeen ya ce masa "Ka Imam Jalaludeen, kana daga cikin manyan dilalan da ya sanya, na dage a kan canza wasu daga cikin dokokin Agadez, wanda za su iya taɓuwa. Iyaye da kakanninmu sun tafka kura-kurai, kura-kuran da yakamata a ce mun yi wasu sauye-sauyen da yakamata al'umma su samu sassauci. Sai dai kai nake ganin zaka iya kamantawa wataƙila ko bayan raina. Ragowar zoben da ake nema, yana gurina, idan Allah ya yi ka zama Sultan a Agadez kar ka  danƙa shi ga kowa, sai mafi cancanta. Na san da duk farmakin da ake kawo maka saboda damar da ka samu, amma ka yi haƙuri ka daure. Sannan zan ci gaba da sanya wa a yi maka duk wani abu na kariya da yakamata. Zan sanya a ƙara sadaukar maka da wasu daga cikin manyan hadiman aljanuna, domin ka samu cikakkiyar kariya. A lokacin an yi ginin zamani, na gidan Sultan, an baro tsohuwar fada ta cikin dutse da ake gudanar da mulki a cikinta.
A zamanin Sultan Ansar, ya samu zaɓaɓɓu, aka gina ɗakuna-ɗakuna, a cikin sabuwar masarautar, da hanyoyin tserewa daga cikin gidan, idan an samu farmaki.
Saifuddeen dai bai haƙura ba, ya haɗa kai da matarsa, ya aura wa ƙanin nasa ɗaya daga cikin ƙannen matarsa Gimbiya Bilkisu.  Saifuddeen ya din ga shiga yana fita, dan kar Jalaludeen ya zama Sultan, ya haɗa kai da wasu daga cikin Imam na majalisar lokacin, da ziga su kan cewar lallai su dage, su yi ƙoƙari su karɓi sauratarsu, mulki ya dawo hannunsu. Masu kwaɗayin mulki suka din ga yadda da zigarsa, wasu kuma suka din ga yi masa kallon ya za a yi ya nemi sarauta ta bar gidansu. Ya din ga ziga su ɗaya bayan ɗaya, ba tare da wani ya san yana ziga wani ba.
Sannan ya koma ya din ga ziga sauran 'yan uwansa, a kan kar su kuskura su yarda su bari, Jalaludeen ya zama Sultan, alhalin duk ga su suna gaba da shi.
A kwana a tashi, Sultan Ansar ya koma ga mahaliccinsa, babu ciwo ba komai, ya yi sallar magariba, ya yanke jiki ya faÉ—i sai gawa.
An shiga cikin matsanancin damuwa da tashin hankali, aka yi masa sutura, sai dai manyan 'yan majalisar Sultan na lokacin, ba su bari an wayi gari ba, suka damƙawa Imam Jalaludeen tagullar da kambun Sarautar Agadez, kamar yadda ya bar wasiyya. Sai dai a tsakaninsu ma 'yan majalissar sai da aka so a samu rarrabuwar kai, aka nemi a yi ƙaramin yaƙi a cikin daren.
Babban na kusa da Sultan, ya sanya aka je aka É—aukko masa Imam Jalaludeen, wanda ya san tun da Sultan ya mutu a kowane lokaci za a iya kashe shi. Abin da ba su sani ba shi ne, tun Sultan Ansar yana kan karagar mulki, suke tsara komai da shi da babban amininsa Matawallen Agadez, wanda shi ma duk zuriyar Azhar ne, sun haÉ—a kakanni.
Aka yi ginin ta ƙarƙashin ƙasa, daga sabon gidan Saruta, zuwa tsohon gidan Sarauta, da aka mayar da shi gurin adana kayan tarihi na Agadez. An narka dukiya mai yawan gaske, gurin gina sabon gidan nan, saboda yanayin ƙasar sahara. Da haka ya saka aka ɗaukko masa Imam Jalaludeen, aka biyo da shi ta ƙarƙashin ƙasa, zuwa gidan tarihi, a gidan tarihin ma, cikin kurkukun ƙarƙashin ƙasa, a nan aka ba shi wannan kambun.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.