Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 54 of 99
AREWABOOKS
Ko da Nana ta shigo É—akin, jikinta ya bata akwai mutum a ciki.
Da ta kunna fitilar ta yi arba da shi, ta rikice ta kusa kurma ihu, sai dai duk da a tsorace yake shi ma, amma kasancewar sa Namiji ɗan gwagwarmaya ya sanya ya danne tsoronsa da tashin hankalin da yake ciki, ya yi mata duk tambayoyin da ya yi mata, sai dai bai tambaye ta haƙiƙanin abubuwan da yake son tambayarta ba. Duk amsoshin da ta ba shi, ba su gamshe shi ba, haka ya fice ya bar ta.
Tun da ya bar ɗakin kusan kwanan tsaye ya yi, ya din ga kaiwa yana komowa a ɗakinsa ya dafe kansa, ya zauna ya tashi. Duk wani lissafi da ya yi sai ya ji babu mafita. Shi dai bai taɓa ganin Nana ba, amma meye haɗinta da yaron da Mahmoudu ya nuna masa? Sannan mene ne alaƙarta da shi da ta iya shiga turakarsa ta rungume shi take faɗar wannan maganganun da suke nuna da alaƙa a tsakaninsu.
Har aka yi kiran sallar Asuba ko gyangyaÉ—i bai yi ba.
Da Asuba da ya dawo daga masallaci, har zai wuce hanyar ɗakinta, ya koma ya nufi ɗakin nata. Ya jima a gurin yana kallon ƙofar. Ya buɗe ƙofar ɗakin a hankali. Ya tarar da ita tana bacci. Sai dai abin da bai sani ba, Ƙaisar ne ya ƙara wa Nana nauyin bacci, amma duk abin da yake faruwa tana gani, sai dai ba za ta iya motsi ba. Cikin sanɗa Hammad ya ɗauki wayar ya yi waje.
Bai ko sake nufar É—akinsa ba, ya fice. Gidan Mahmoudu ya tafi, ya je ya tarar da shi a zaune yana lazumi.
Sai da Mahmoud ya tsorata ya ce "Lafiya na ganka da duku-dukun nan?"
"Mahmoudu wane ne yaron nan da ka nuna mini? Kuma wace ce yarinyar da Asal ta kawo a matsayin mai yi mini girki?"
Mahmoudu ya kalle shi ya kalli screen É—in da yake nuna masa, tabbas Nana ce ba wata ba, amma zai so ya yi magana da Nana kafin gaya wa Hammad wani abu.
"Ka yi magana ka tsaya ka na kallo na" Ya yi maganar cikin hasala.
Mahmoudu ya ce "To ai Asal yakamata ka tambaya ba ni ba, ni fa cin karo kawai na yi da hoton na nuna maka"
Zai yi magana kansa ya sara, ya saki wayar ya fara ja da baya yana dafe kansa, ya tafi zai faÉ—i Mahmoudu ya yi saurin tare shi, ya kwantar da shi a hankali.
Ya É—auki wayarsa ya kira Al-Husssain. Bayan sun gaisa Mahmoudu ya ce "Imam Hammad ya yi maka magana a kan yi masa bincike a kan yarinyar da Asal ta kawo Agadez ta din ga yi masa girki ko?"
"Eh ya kira ni, ya yi mini maganar"
"To yaya ake ciki, me aka gano a kanta?"
Al Hussain ya ce "Eh ina kan yin binciken ne, amma dai wani kamfani ne, da suke samar wa mata, guraren aiki suka kawo ta. To na saka Hasna ta tuntuɓe su, dan ni gaskiya ban wani tantance ta ba, na ɗauke ta aiki, saboda ta ce daga Nigeria take. To gidan aikin sun ce, su ma wata mata ce jami'arsu ta kawo musu ita. Amma za a nemo matar yanzu haka su muke saurare"
Mahmoudu ya ce "To shikenan, amma duk abin da aka ƙarasa bincikowa, ni zaka sanar, ka gaya masa tukuna"
Sanin alaƙar da take tsakanin Hammad da Mahmoudu ya sanya kai tsaye ya ce masa to.
Hammad kuwa yana kwnace, sai jujjuya kansa yake yi yana wani irin gumi. Giyaz yake gani yana yi masa wata irin dariya, da ƙara wadda ta cika masa kunne. Ya lallaɓa ya tashi zaune ya toshe kunnunwansa yana faɗin "Hasbunallahu wa ni'imal wakil"
Mahmoudu ya durƙusa a gabansa yana kiran sunansa, amma bai amsa ba ya rintse idanunsa.
"Sayyid, Sayyid dan Allah da gaske ba ka tuna ni ba?" Maganganun da Nana ta din ga yi masa ya din ga ji a cikin kunnensa.
"Mahmoudu" ya kira sunansa a hankali.
"Na'am Imam"
"Mene ne alaƙata da yarinyar nan?"
"Amm ban sani ba tukuna, ina jiran abin da Al Hussain zai ce ne tukuna"
"Ka kirawo ta ka tambaye ta, wane ne yaron nan? Me yasa kuma yake kama da ni?"
"Za a yi, amma ka yi shiru da bakin ka mu gano komai tukuna"
Sai zuwa yamma Hammad ya É—an samu nutsuwa, sai dai bai sake ganin Nana ba, abincinsa ma ajiye masa ta yi.
Da daddare Asal ta ɗauki hankalinsa sosai, saboda yadda ta sha kwalliya cikin jajayen kayan bacci sai ɗaukar ido take yi. Yana ta ƙoƙarin kar ya shiga hakkinta, saboda damuwoyin da suka yi masa yawa.
Sai dai bai iya taɓuka komai ba, hankalinsa ya fara gushewa.
Wani irin haske ya din ga gani a cikin baccin nasa yana ɓullowa ta cikin wani mudubi, sama-sama ya din ga hango shi tare da Nana a ciki, cikin yanayin wata rayuwa da take nuna tsananin kusanci da kyakykywar alaƙa a tsakaninsu.
Sai dai bai gama fahimtar abin cikin mudubin ba, Giyaz ya bayyana ya huro wata irin wuta a take mudubin ya tarwatse, ya ja da baya yana kare kansa. Giyaz ya gani tare da Ƙaisar, tsananin kamaninsu tsufan Giyaz ne kawai ya sanya shi ya banbance su. Farkawa ya yi jikinsa ya ɗauki wani irin zafi. Tashi ya yi yana zagaye ɗakin, amma ya ci gaba da jin zafin ya tsananta kawai ya fita ya je hanyar ɗakin Nana ya zauna. Zuciyarsa kuma sai azalzalarsa take yi a kan ya je ya samu Nana ya yi magana da ita, amma wata zuciyar ta hana shi hakan.
Giyaz kuwa faɗa ne ya kacame tsakaninsa da Ƙaisar.
"Ƙaisar muddin ka yi ƙoƙarin saka mutumin nan ya tuna yarinyar nan, zan iya hallakaka, ko kuma na saka shi ya haukace gaba ɗaya"
Ƙaisar ya ce "Kafin ka halaka ni, ni zan halakka ka muddin za ka ci gaba da shiga abin da bai shafe ka ba"
"Ni zaka hallaka, Giyaz bin Jaddul Jinn?"
Ƙaisar ya ce "Ƙwarai kuwa, a kowane lokaci zan iya baka mamaki"
Hammad kuwa da duku-duku ya sake tafiya gurin Mahmoudu. Yana ganinsa gabansa ya faÉ—i.
Ya ce "Mahmoudu ka zauna mu yi magana"
Mahmoudu ya zauna yana rarraba ido"
"Ko dai ka gaya mini abin da ka ke ɓoye mini, ko kuma zan tari duk wanda nake ganin zan samu abin da nake nema, komai zai faru sai dai ya faru. Ka yi mini bayanin waye yaron nan, kuma wacece yarinyar nan"
"Matarka ce" Ya ba shi amsa kai tsaye. Zabura ya yi ya ja da baya yana kallon Mahmoudu "Yaushe kuma ta yaya?"
"An yi mini gargaɗi sosai da sosai, a kan kar na kuskura na gaya maka, duk da babu wanda ya san da wannan zancen ma. Amma ko zan rasa rayuwata na yi alƙawarin zan gaya maka iya gaskiyata. Nana matarka ce da ka aura a Nigeria. Bisa ga binciken da nake yi ta ƙarƙashin ƙasa kuma, kai ta fito nema ta zo Agadez"
Jiki a sanyaye Ya ce " Mahmoudu ban fa gane me ka ke nufi ba, yaushe na je Nigeriar har na aure ta?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.