Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 91 of 99
Hawaye ya cika idanun Nana, ta ƙanƙame Muhsin, tana tuna wancan.
Jamila ma cikin kuka ta ce "Na yi dana sanin Hajiya Sa'a, da tuni wannan ma ta bayar da shi kamar yadda ta bayar da wancan"
A razane Fadila ta kalle ta ta ce "Me ki ke nufi?"
Nana ta ce "Babu abin da take nufi"
Fadila ta ce "A'a ga abu nan tana faÉ—a, kenan da gaske Hajiya Sa'a ita ta bayar mini da Muhsin É—ina? Ya aka yi ki ka sani"
"Fadila na gaya miki wannan zancen ba haka yake ba, meyasa ki ke da gardama ne? Wannan É—in suwaye su?"
Ya kalli Jamila ya ce "Wannan ba ke ce nake gani a gidan Sa'a ba? Ya aka yi ki ka san wannan zancen?"
Nana ta katse shi, ta hanyar gaishe shi, ya amsa sai dai tana magana ya gane ta.
Ya ce "Nana ke ce?"
Nana ta jinjina masa kai tana murmushi.
"Baiwar Allah kin san tsawon lokacin da na É—auka ina neman ki? Na din ga mafarkai daban-daban da ke. Jinya na haÉ—u da ita bayan kin yi aure"
Fadila kasancewar ba wannan maganar take buƙata ba, cikin ɗimuwa ta ce wa Jamila ta gaya mata abin da Hajiya Sa'a ta yi wa ɗanta.
Alhaji Fatuhu ya fara ƙoƙarin karewa ya hana, amma Jamila ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri, na haddass muku fitina, amma gara na faɗa dan abu ne da yake ta damuna." Nan ta kwashe komai ta faɗa, har abin da Alhaji Fatuhu bai sani ba, da yadda ta shiga ƙungiyar asiri duk sai da ta faɗa, da yadda Abba ya mutu maimakon Muhsin.
Cikin kiɗimewa Fadila ta riƙe Alhaji Fatuhu tana faɗin "Amma ka zalunce ni, saboda ka kare 'yar uwakka, ka din ga yi mini wasa da hankali ka ƙi yarda da abubuwan da take faɗa. Ɗana gudan jinina aka ba wa matsafa. Ɗana fa ɗan da na sha wahala na haifa."
Nana ce ta sauke Muhsin, ta je ta kamo Fadila ta rungume ta cikin rarrashi ta ce "Yanzu wannan da ki ka haifa kin san Allah zai baki shi? Dan haka ko da ita ko babu ita, Allah ya ƙaddara ba rayayye bane ba. Kuma da na san Jamila zata faɗa ba zan yadda mu zo tare ba. Ki yi haƙuri ba zan ce sai kin yafe ba, amma kar ki ɗaga masa hankali, tashin hankalinki yake gudu ya sanya ya ɓoye miki. Kina kallo ya rasa ɗansa dalilin yar uwassa, abokinsa ya cutar da shi da mugun baƙin sihiri, kar ki ce za ki huce a kansa dan Allah"
Ayshercool
08081012143
Littafin kuÉ—i ne, a biya 1k via 0069685771 Aisha Adam stanbic
103
Fadila ta saki rigar Alhaji Fatuhu, ta koma da baya tana zubar da hawaye cikin matsanancin tashin hankali da damuwa.
Nana ta din ga yi mata nasiha mai shiga jiki tare da ba ta misali da kan kanta, irin faÉ—i tashin da ta din ga yi bayan auren ta.
A hankali kuma sai Fadila ta din ga samun nutsuwa, tana jin damuwar ta ta, ta ragu ta kaÉ—u sosai da sosai da jin irin iftila'i da Nana ta din ga faÉ—awa ita ma.
Alhaji Fatuhu ya ce "Sannu Nana"
Nana ta yi murmushi ta ce "Yanzu ga shi komai ya wuce, amma soyayyar da nake yi wa marigayi Muhsin, ta sanya bayan na haihu na sanya wa yarona Muhammad Muhsin, shi ma sunan shi Muhsin, zai yi sa'an wannan Muhsin É—in" Ta yi maganar tana kallon Muhsin da ya kwanta a jikin Alhaji Fatuhu.
Fadila ta ce "Yanzu har sunan Muhsin ki ka saka wa yaronki?"
Nana ta ce "Ƙwarai kuwa, Allah shaida ne na so Muhsin yaron nan ya shiga raina nesa ba kusa ba. Bayan shi sai Haidar ɗin Shukura jikan Alhaji Zailani, gaba ɗaya zuciyata ta tsinke ina tsoron a ce shi ma wani abin ya faru da shi"
Alhaji Fatuhu ya ce "A'a yana nan cikin ƙoshin lafiya shi"
Nana ta sake cewa "Dan Allah Maman Muhsin ina sake baki haƙuri, kar ki ga laifin 'yar uwata tun da har ta nemi yafiyarki ta bayyana duk abin da ya faru ba tare da tsoron abin da zai biyo baya. Yadda aka bi aka saka ta a ƙungiyar asiri ba da saninta ba, kuma a garin ta ceci wannan Muhsin ɗin, ɗan Hajiya Sa'a ya rasa ransa kuma ita ma haryanzu fama take yi da rashin lafiya"
Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, dukkaninmu nan bamu wuce jarrabawa ba. Sai dai mun gode Allah, muna fatan ya zama kaffara a gare mu, domin ni jinya na sha, da sai da na din ga wari da raina, na yanke tsammani da rayuwa na rasa komai. Na ƙi yarda a yi mini maganin addini, ina tunanin ko na Asibiti ne. Wataƙila ma da Muhsin na amince an yi masa na addini da ko zai mutu zai samu afuwa.
Ni kaina mafarki na din ga yi da ke kina ce mini sihiri aka yi mini, na nemi magani na yi mafarkin nan ya fi a ƙirga sannan na yarda na fara neman maganin addini. Wallahi rasa ɗana Muhsin bai yi mini zafin yadda nake tausaya wa Shukura da Zailani ya salwantar da rayuwarsa domin wai ya ga bayana ba. Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Yayi maganar yana fashewa da kuka, saboda dauriya kawai yake yi, amma abin yana mugun cin sa. Ya kasa sakin jiki ko Allah ya isa ya yi wa Zailani da 'yar uwassa gani yake iya bala'i da masifar da suka jefa kansi ma, ta ishe su a wajen Allah ba sai ya ƙara musu da Allah ya isa ba.
Sai azahar su Nana suka bar gidan, sun yi hira sosai da Alhaji Fatuhu jin sa take yi kamar uba. Yake tsokanarta da zai din ga aika mata da kaya Niger tana sayarwa.
Daga gidan Alhaji Fatuhu gidan Ummi suka wuce, jikin Nana duk a matuƙar sanyaye, sai abu ya faru ta yi ta tunanin a ina ta san abin, a ina ta taɓa gani, sai ta nutsu sai ta tuna Ƙaisar ne ya nuna mata.
Ummi ta din ga yi wa su Nana masifar dan me za su zo da rana haka, bayan tun safe take saka ran ganinsu. Cikin jimami da damuwa, Nana ta kwashe komai ta gaya wa Ummi.
Ummi ta kaɗu ta tsure da jin labarin da Nana ta bata, sai dai sam bata bayyana mata, wai Jamila har ƙungiyar asiri ta shiga ba, ita ma Ummin bata nuna mata Baba ya gaya mata ba.
Ummi ta ce 'Ina ta saka ran ki zo mu sha hira, amma kin zo mini da abin tashin hankali.
Suka watsar da wannan hirar, suka shiga wata. Hira tayi hira har take ba wa Nana labarin Saleh yana gidan yari, saboda sayen kayan sata da suka yi na gwangwan an kulle shi a Lagos.
Ta tambaye ta su Barira, ta gaya mata auren Barira ya mutu, Sajida kuma tashi suka yi daga unguwar gaba É—aya.
Ta gaya wa Nana cewar sau biyu Hammad yana aiko mata da kuÉ—i masu tsoka, ya ce ta É—auki nata ta tura wa Uwani sauran.
Nana ta ce "Ni bai taɓa gaya mini ba ma, ha tsaraba kuma ya sake bani na kawo miki"
Ummi ta ce "Allah sarki, Nana kin sha wahala ashe dai Allah ya yi kina da rabon jin daÉ—i a duniya"
Nana ta ce "Ke dai bari, irin wanda ban taɓa tsammani ba. Amma wahalar da na sha sai da na yanke tsammani da samun afuwa. Sai kuma a hankali na lura da wani tsananin da na din ga shiga, shi ya din ga sadani da hanyoyin warwarewar matsalolin nawa. Na koma na din ga istigfari saboda na yi wa Ubangiji halin namu ɗan Adam, raki da kuma gaggawa Allah dai ya ƙara datar da mu" Jamila sai koma wa tayi gefe ta yi shiru, ba ta iya cewa komai.
Da suka koma gida bayan magariba, Baba ya yi ta faÉ—an Nana ga ga da aure, amma taje ta yi dare a waje.
Ta idar da sallar isha'i, tana ƙare wa ɗakinsu kallo, ɗakin da ta din ga shan azabar a Ƙaisar a cikin sa. Kawai ta tuna lokacin da ta ga bararoji na shan jinin Suwaiba. Ta kalli inda Suwaiban take, ta koma kamar wata mai shan inna, duk ta bushe ko abincin kirki ba ta ci, ƙwaƙwalwarta ta taɓu sosai da sosai.
Ba shiri ta tashi ta aika Nasiru, ya nemo mata tazargade.
Da kanta ta É—auki Alqur'ani ta din ga karantawa tana busa wa a ruwa.
Ta idar ta ba wa Suwaiba, ta shashashfa mata ruwan a jikinta, ta rungume ta tana ci gaba da yi mata karatun Alqur'ani ƙasan zuciyarta ta din ga yi mata addu'a da fatan Allah ya yaye mata wannan ciwon.
Kullum sai Sayyid sun yi waya da Nana, aka fara processing yi mata passport, da kuma visa a Nigeria.
Kwanan Nana uku, sai ga Suwaiba na iya cin abinci, Jamila ma tana cewa yanzu tana iya bacci sosai, ba tare da ana tsorata ta ba. Nana ta yi mata nasiha sosai da sosai a kan kula da ibada da kuma yin addu'a.
Yaya Atine da kanta ta wanko ƙafa ta zo gidan, tana bala'in Nana ba ta je ta gidanta ba.
Da ta ga Nana ba ta kula ta ba, sai kuma ta hau kame-kame tana faÉ—in "Haba ta gidana, a ce kin zo takanas bayan tsawon shekaru ba kya nan a ce, kuma ba ki taka kin je inda nake ba? Babu faÉ—a me ya kawo gaba Nana?"
"To Yaya Atine kwata-kwata yaushe na zo garin, sai a hankali ai nake zagayawa amma kin zo kina ta faÉ—a"
Nasiru ya ce "Ke ma dai Yaya Atine da fitina ki ke, ya za a yi ki zo ki rufe basarakiya da faÉ—a haka, kin ma ci sa'a da ta kula ki. Nanan yanzu fa ba wadda ki ka sani da ba ce"
"Aikuwa na ga alama, maganar ma da kyar take yi, aishikenan"
Nana duk gidansu ta rasa wanda ya ke da lambar Sarkin baka, kowa sai ya ce mata ba shi da ita.
Nana ta kira lambar Sagir, kamar yadda ta karɓa a gurin Alhaji Fatuhu.
Bayan sun gaisa ta ce masa kwatancen gidansa take nema, za ta zo gurin Shukura. Ya kwatanta mata ta yi masa godiya ta kashe wayar.
Tana katse kiran, kiran Sayyid ya shigo wayarta.
Ta yi murmushi ta É—aga ta ce "Masoyi"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.