Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 55 of 99

"Bayanan da Matawalle ya yi maka ba haka yake ba, ka manta da komai naka, na tafi da kai Nigeria. Yanzu duk bayanin da zan yi maka ba komai zaka fahimta ba, amma Nana Asma'u matarka ce"

Hammad ya ce "Mahmoudu, anya ba haukacewa na yi ba kuwa? Ji nake yi kamar ba mutum ne ni ba. Gaskiya"

Ya dafa kafaÉ—ar Hammad ya ce "Mutum ne kai, wasu abubuwa ne dai kawai suke faruwa amma ka nutsu, ka yi addu'a. Dan muddin ba ka tuna komai ba, ba zamu iya tunkarar kowa da maganar nan ba. Mutumin da ya zo muna tare a sahara, tare aka kamo ni da su, tare muka yi aikin gadi da su a Nigeria. Hammad ban san yaya zan yi maka bayanin jajircewa da sadaukarwar da yarinyar nan ta yi saboda kai ba." Nan Mahmoudu ya din ga yi masa bayanin wasu abubuwan da ya sani.
Ya yi shiru ya rasa gazgatawa zai yi ko ƙaryatawa, idan ya yi duba da wasu abubuwan sai ya ga yakamata ya gazgata batun, dan Mahmoudu ba zai masa ƙarya ba.
Amma ya din ga jin sa kamar ba mutum ba, ko kuma a wata Duniyar yake ta daban.
Da daddare yana tare da Asal, tana danna waya, Nana ta kawo Abincin dare. Kamar ya yi mata magana ya fasa, sai dai ƙasan zuciyarsa ya din ga fatan Allah ya sanya gaske ne, Nana matarsa ce, ta kowacce fuska ta yi masa. Tun kan ya ji kan wannan burkitaccen labarin yake jin wani abu na sukan zuciyarsa a game da ita. Babban abin da yake ƙara burge shi da ita, sanin mutuncin kanta da ba ta yadda Asal ta taka ta ba. Saɓanin waɗanda suke kwantar da kai Asal ɗin ta taka su saboda abin Duniya. Ya gaza manta rungumar da ta yi masa a turakarsa.
Ta ɗago kai suka yi ido huɗu da shi, amma bai sauke idanunsa ba ya ci gaba da kallon ta. A ɗan diririce ta ce "Na gama zan iya tafiya. Bai amsa mata ba ya tuna yadda take ba shi Nonon raƙumi da habbatussauda, ga abinciccikan da yake matuƙar da take gwangwaje shi da su.
Asal ta ce "Za ki iya tafiya" Sai da Nana ta je tsakiyar falon sanan ya ce yana buƙatar lemon kankana da shayin citta da kanumfari kawai, ba zai sha na kimba ba.
Nana ta yi shiru ta ci gaba da tafiya, Asal ta ce "Kin ji ai"

A hankali Nana ta ce "Na ce miki ba ni da kunne ne, da ba zaki iya tsinana wa mijinki uban komai ba"

"Ke ba magana nake yi miki ba" Nana ta waiwaya ta ce "Ai na amsa na ce to"

Shi kuwa ya yi haka ne, dan ta sake dawowa ya ci gaba da kallon ta ko Allah zai sanya ya iya tuna wani abin.
Amma har ta kawo masa shayin tayi tafiyarta bai tuna komai ba.

Sosai faɗa ya ɓarke a tsakanin Giyaz da Ƙaisar a kan Nana, Giyaz ya din ga ɗaga Ƙaisar yana bu ga shi da ƙasa. Karfin Ƙaisar da na Giyaz ba ɗaya ba ne ba, duk da Giyaz ya kwana biyu a duniya amma yana da matuƙar ƙarfi.
Ƙaisar ya baje a gurin, bayan buga shi da jikin dutsen gidan tarihin Agadez,da Giyaz ya yi, ga ƙona shi da ya din ga yi da wuta. Sai dai ganin Ƙaisar ya baje ko motsi ba ya yi, ya sanya ya nufe shi da sauri yana kiran sunansa, ya ɗago Ƙaisar, amma ya shammaci Giyaz, ya fito da jakar gurin Sarkin Baka daga cikin rigarsa, ya naɗe masa wuya da hannun jakar. Wata irin kururuwa Giyaz ya din ga yi, yana tumami a gurin yana burgima. Ihun nasa sai da ya razana da yawa daga cikin halittun da suke cikin gidan tarihin.
Ƙaisar ya miƙe da kyar ya tunkari wani ɗaki, aljanun da suke ƙofar ɗakin su ka dare suka ba shi guri. Ya zura hannunsa a ya ɗaukko kwalbar da Giyaz ya ce tunanin Imam Hammad ne a cikinta. Ya ajiye ta a nesa kaɗan ya ja da baya ya din ga hura iskar bakinsa a jikin kwalbar. A take kwalbar ta yi wata irin ƙara ta tarwatse, a take ɗan hayaƙin da yake cikin kwalbar yana zagayawa a cikin wani ruwa ya bar cikin ta. Ƙaisar ya koma kan Giyaz da ya suma a gurin, ya ɗauke jakar da ya shaƙe shi da hannunta, ya ɓace daga gurin.

A hankali yake juyi, ya buÉ—e bakinsa domin ya jarraba yin magana, ya ji ko maganar ta dawo ya ce "Ma vie" sai dai ya ji shiru. Shi ma shirun ya yi yana ji wani raÉ—aÉ—i tun daga cikin kansa har idanunsa. Ya yi juyi ya ji taushin abin da yake kai ya banbanta da nasu. Ya buÉ—e idanun da suke yi masa raÉ—aÉ—i da kyar yana kallon É—akin. Asal ce ta shigo ya kalle ta, ta ce "Amour ta gama abinci, ka taso ka karya" Ya jinjina mata kansa da ya yi masa wani irin nauyi mara misaltuwa.
Tabbas ya san Asal matarsa ce, amma ina Nana. Sai ya yi shiru sannu a hankali ƙwaƙwalwarsa ta tariyo masa yadda aka fita da shi daga gidansu na Buda yana fizge-fizge yana kiran matarsa Nana. Ya rintse idanunsa tare da damƙar gashin kansa yana girgiza kan, saboda yadda ƙwaƙwalwar tasa ta hargiste, tunanin ma ya rasa wanne zai yi.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya din ga maimaitawa babu ƙaƙƙautawa. Asal ta sake shigowa ta ce "Amour wai yane? Baccin ne bai ishe ka ba? Sha biyu saura fa na rana, ba ka ko karya ba"
Ya yi mata nuni da hannunsa alamun yana zuwa.

"Ok, ni zan je gida, Abbu yana jira na" Ya jinjina mata kai"

Sannu a hankali ya fara samun nutsuwa, ya miƙe tsaye a hankali, ya shiga banɗaki ya watsa ruwa, sai dai jiri ya din ga ɗibarsa.
Ya fito ya zura rigarsa ya fita, ya hau kan doguwar kujera ya kwanta. Ya lumshe idanunsa, abubuwan da suka faru a Nigeria suka din ga dawo masa saɗara-saɗara, zuwa dawo da shi Niger da aka yi. To ya ya aka yi ya manta da ita komai nasa ya shafe da ya baro Nigeria, kuma yaya aka yi ya manta da komai nasa da yaje Nigeria. "Anya babu wata maƙarƙashiya ko wani abu da ban sani ba, game da rayuwata ba?"

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin, hannunta riƙe da kwandon kwanukan Abinci.
Wata irin karaya ta ziyarce shi, zuciyarsa ta din ga azalzalarsa ya tashi ya rungume ta, Asmynsa ce, amma zuciyarsa ta din ga gargaÉ—insa kar a samu matsala, dan ya san dokar Agadez.

"Barka da wannan lokaci Sayyid, ga abincinka, na ga na safe ma baka ci ba, ko ba shi ka ke so ba ne?" Hannu kawai ya É—aga mata, ya lumshe idanunsa, mamaki ya cika ta, ganin ba shi da niyyar magana, ya sanya ta tashi ta fita cike da damuwa.
Tana fita ya haɗe tafukan hannayensa, ya dafe fuskarsa ya fashe da kuka, da wace fuskar zai kalle ta? Me zai ce mata? Ta ina za ta yarda da shi cewar ba yana sane ya ƙi kula ta ba. A hankali ya ci gaba da tuna tsantsar juriya da sadaukarwar da ta yi saboda shi. Ba ta haƙura ba ta taho nemansa, sun haɗu kuma bai gane ta ba.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.