Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 98 of 99
"Eh na je na É—aukko Abinci ne, mutane na ta son su zo su ga jaririya fa."
"Ki ƙyale su, idan sun koma gida a ganta"
Har ranar suna Nana ba ta san sunanta za a saka wa jaririyar ba, aka shirya gagarumin suna a Agadez. Nana ta yi wa jaririyar nan kaya na alfarma. Kawai ta ji Hammad yana gaya wa Zahradeen wai sunan jaririya Asma'u. Nana ta yi turus ta ce "Sayyid, amma da wasa ka ke yi ko?"
"Kamar yaya wasa? Da gaske nake"
Cikin damuwa ta ce "Dan zatin Allah ka yi haƙuri, wannan ai rigima ce, kawai salon ka ja mini magana a garin nan, shekara da shekaru tana neman abu, ta sha wahala ta haihu kuma a saka sunana?"
"To ai ita ta nemi hakan ba ni ba"
Nana ta girgiza kai ta ce "A'a ka yi mata fin ƙarfi dai, Asal ba za ta yarda a saka wa yarinyarta sunana ba. Ni dai dan Allah ka canza"
Kawai ya hau dariya, ya ce "To ni yaya zan yi muku? Idan kin je gurin sunan, ki tambaye ta"
Nana ta ce "A'a ni dai na yafe, dan Allah ka canza mata suna, ya za a yi ka yi mata haka, salon kawai ka saka a ƙara tsana ta"
"To ai ni ina sonki dan a tsane ki ba komai tun da ina sonki"
Da gaske Nana ta fututtuke ta ce bata yarda ba, sai da ya É—auke ta suka je gidan.
Asal ta ce "Dan na ce a saka wa jaririyar ki sunanki shi ne za ki ce ba kya so? Kina jin haushina kenan tun abubuwan da suka faru tsawon shekaru goma"
Nana ta ce "Wallahi ba haka ba ne ba, ba na son a yi miki fin ƙarfi ne, a takura miki abin da ba kya so"
Asal ta ce "A'a ni na ce a saka mata, babu wanda ya takura mini" Nana ta yi wa Nana bayani kamar yadda ta yi wa Hammad, sannan ta ɗora da cewa "Nana ni da ke mu na da tabon juna, da ba zai taɓa yiwuwa na ce sai mun yi nu'amala da juna ba. Amma ina son yaranmu su tashi da haɗin kai, kamar yadda ki ka kawar da kai ki ka nuna mini yaranki nawa ne. Ba na fatan a sake samun matsala na rabuwar kawuna saboda mulki ko abin Duniya a tsakanin yaranmu. Ina fatan za ki saka mini takwarar ki a cikin su Yarima, ta samu kyakykywar kulawa. Kuma ina godiya da dukkanin wasu abubuwa na alkhairi da ki ka yi mini, da ɗaukar damuwa ta taki, duk da ba jituwa muke yi ba"
Wani irin farinciki ya mamaye ta, ta ce "Tabbas takwarata kin haife ta ne, amma ni ki ka haifawa. Kuma na yi wannan alƙawarin na sanya ta cikin jerin 'ya'yana. Ya hayyu ya ƙayyum Ubangiji Allah ya kawo biyar a bayan ta"
Asal ta ce "Biyar sun yi yawa ai, yadda shekaruna su ka ja É—in nan? Ita É—in ma na gode Allah"
Nana ta ce "Taskar Allah babu abin da babu, ko ba biyar ba Allah ya ƙaro mana wasu, shekara iyanzu a ce an kusa haifo mana wasu. Na gode sosai da sosai da karamcin nan da ki ka yi mini"
Jin sunan da aka saka wa jaririya, ya janyo cecekuce sosai da sosai a garin. Da ganin kamar ba a yi wa Asal adalci.
Kwanan Husna arba'in, Nana ta buÉ—e cibiyar magungunan musulunci.
Manyan mutane duk sun halarta, har da 'yan uwan Nana na Nigeria. A daidai lokacin ta kammala rubutun littafinta, da ta yi bincike tsawon shekaru, a kan aljanu, da ilimin ruƙiyya da ladduban yin ta.
A cikin sunayen mutane masu muhimmanci da ta lissafo a cikin littafin, sai da ta sanya sunan Ƙaisar Giyaz.
Ko da aka nemi Asal ta tofa wani abu a gurin taron, Nana ba ta zaci za ta yi magana ba, amma ta karɓa ta taya ta murna, tare da shaidawa duniya, a kanta Nana ta fara gwajin maganin haihuwa kuma Allah ya amsa.
Nene ta taimakawa Nana sosai a ɓangaren magungunan, haka Sarkin baka ya halarci taron, Hammad ne da kansa ya gayyace shi. Ya din ga yi wa Nana dariyar ba a guje wa ƙaddara.
Nana ta yi murmushi ta ce "Na karɓe ta ta hanyar da ta dace ne" Nana ta yi shiru tana kallon gurin nata. A hankali ta furta "Na cika maka alƙawarinka uban ɗakina"
"Nima na cika wanda na yi miki uwar gijiyata, na rubuta tarihinki da alƙalamin zinare a cikin kundi na mussaman da ba zai ɓace ba" Ta ji tamkar muryar Ƙaisar a gurin. Idonta ya sauka a kan award da ta yi da sunansa ta ajiye a gefe guda.
Shukura wannan rashin lafiya da ta yi ta fama, da damuwar da take ciki ne yayi ajalinta, Yusra ta shiga damuwa da tashin hankali sosai, sai dai ta rungumi yaran Shukura da waÉ—anda ta haifa.
Jamila ta samu wani jami'in ɗan sanda mai mata biyu ta aura, Allah ya taimake ta, ya ware mata gidanta sai dai tana shan azabar kishiyoyin duk da haka. Ta rungumi sana'arta sosai da sosai. Suwaiba kam ƙwaƙwalwa ta riga ta taɓu haka Mama ta ci gaba da wahala da ita.
Allah Al-musawwiru, shekarar Husna É—aya a duniya, ta sake samun juna biyu, a dole Nana ta É—auke ta, ta yaye ta. Ta haifi yara biyu mace da namiji.
Nana kuma sai a haihuwa ta ƙarshe, ta haifi 'ya mace, duk da ba wani shiri suke yi ba, amma kan yaransu a haɗe yake sosai da sosai. Nana tsaye take a kan tarbiyya da kuma ilimin yaran mussaman na addini.
Hatta garin Buda sai da suka amfana da Nana, dan ta sai filin da kukar Lanti take, filin da kukar da aka yi wa Lanti girka, aka buÉ—e islamiyya. Sannan duk shekara suna samun abin alkhairi na kayan masarufi mussaman da azumi.
Ummanta duk ta aurar da ƙannenta mata, Imrana bayan ya kammala karatunsa, ya yi zamansa a faransa, sai da Nana ta matsa masa da batun aure, sannan ya ce ta samo masa duk wadda ta yi mata zai aura.
Suka rayu cikin kwanciyar hankali, da son juna. Ta samu kulawa da tsantsar soyayya daga miji, yaransu gaba ɗaya suna matuƙar sonta da ƙaunarta. Husna kuwa tamkar babbar 'yar Nana. Yayin da Yarima yake ɗan gurin Asal.
Ta shiga cikin mata da aka sanya sunansu a kundin tarihin Agadez.
Ta rayu cikin aminci da nutsuwa, a rayuwar da sai ta so ta yanke tsammani saboda gwagwarmaya. Sai ɗan sauran ƙalubale da faɗi tashin rayuwa da ba a rasa bawa da shi.
A hankali ya yi ajiyar zuciya, ya kalli matashin da yake zaune yana saurarensa, ya ce "Ka ji labarin Gimbiya Asma'u, to kai ma shigen abin da ya faru da su ne yake shirin faruwa da kai"
Ɗaya matashin ya ce "Allah ya yi mini tsari, idan kuma ni ban taki irin wannan sa'ar da Nana ta taka ba fa? Lallaɓawa zan yi na bi dare na gudu na bar garin nan, sai ta koma bin wani. Haka kurum mahaukaciya ta liƙe mini ta din ga bi na"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.