Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 57 of 99

A hankali Hammad ya É—ago Nana daga jikinsa ya ce "Asmy bacci ki ka yi?".

"Idona biyu" Ta ba shi amsa.

"Kin yi shiru, Asmy ba da gangan na ganki na ƙi kula ki ba, kin san muddin ina cikin hayyacina babu yadda za a yi na share ki. A lokacin ina ta shirye-shiryen yadda zamu ɓullowa lamarin, Tafawa kuma ya sanya ni a gaba da da haƙilon ba zan yi mulki ba, ni juya ne, ga rashin lafiya ga hauka ga babu zobe. Ya daɗe yana jifana da kalmar juya, abin yana yi mini zafi da ciwo shiyasa na fallasa komai a lokacin da shirin duk abin da zai faru ya faru."

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yakamata mu tashi, an kira sallar Asuba".

Hammad ya ce "Haka ne, amma ba ki ce komai ba" Ta ce "Zan ce ne, ina jin bacci ne sosai ka ga kwana muka yi ba mu yi bacci ba" Ya ce haka ne. Suka tashi suka koma ɗakin nan zai rufe amma ya tsaya ganin Nana na ƙara kallon ɗakin.
Ya ce "Wannan ɗakin tun zamanin Sultan Azhar yake, duk Sultan ɗin da ya zo a nan ɗakin ne turakarsa. Kowane zamani akwai canji da kuma yadda ake ƙawata ɗakin. Kafin daga bisani a daina amfani da gidan gaba ɗaya."

Nana ta jinjina kai ta ce "Ni yanzu abu ɗaya nake son ka gaya mini, ina da ciki ko ba ni da shi?" Ta yi maganar a ɗan shagwaɓa tana marairaice fuska. Ya yi murmushi ya ce "A cikin labarin kin ji inda wani abu ya faru ne?"

"Eh mana, tun da kana zuwar mini É—aki ba tare da sanina ba"

Ya jinjina kai ya ce "Sosai kuwa, dan tun da na gano ke matata ce, kusan kullum tare muke kwana, ya yi maganar yana rufe ɗakin. Ya damƙi hannunta suka yi gaba, ja ta yi ta tsaya tayi shiru sannan ta ce "Sayyid ba ka nuna mini mene ne a cikin ɗakin can ba" Ya kalli ɗakin ya ce "Hanyar tsohuwar prison ce, inda daga baya ake aikin sarrafa gold a ciki, amma yanzu babu abin da ake yi da gurin"

"Ina son ganin mene ne a ciki" Ya ce "To shikenan" Ya ja hannunta zuwa ƙofar gurin, amma suka tarar da ƙaton kwaɗo a jikin ƙofar. Ya ce "To ai gurin a rufe yake ma"

"Ya aka yi sauran ƙofofin ba a saka mukulli ba sai wannan? A tambayi mai tsaron gidan ya buɗe mini zan gani"

Hammad ya ce "To ai lokacin salla ya yi"

Ta ce "Na sani gani kawai zan yi mu tafi"

Ya tsaya yana kallon Nana da rikicin tsiya, ya ce "Zo mu je sai mu yi wa mai gadin magana, ya zo ya buÉ—e mana" ta bi shi a hankali jikinta cike da kasala ga kuma bacci da take ji.

Ko da Hammad ya tambayi tsohon nan mai tsaron ƙofar, sai cewa ya yi "Allah ya taimake ka, ban san wanda ya rufe ɗakin nan ba, ya kwana biyu a rufe"

Hammad ya ce "Wataƙila ko masu yawon buɗe ido su na ɓarna a gurin, shiyasa aka rufe"

Nana ta ce "Waye yake da alhakin rufewar?".

"Ma vie, wai lafiya kuwa?"

"Hammd sai an buÉ—e gurin nan kafin na bar Agadez"

"Shikenan na ji, za a buɗe amma muje mu yi salla tukuna" Da kyar ya lallaɓa ta suka bar gurin, saboda yadda take nema ta burkice masa gaba ɗaya.

*****
Shukura na zaune a kan gadon Asibiti,  ta zuba ido tana kallon ɗan jaririnta, ƙato da shi mai matuƙar kama da Sagir, ta din ga tuno da jaririnta da aka ce ya mutu da haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da hakan. Ji ta yi an turo ƙofar ɗakin ta ɗago da sauri, gabanta ne ya faɗi ta yi turus tana kallon mai shigowar.

Ayshercool
08081012143

94
LITTAFIN KUÆŠI NE, KI BIYA KAFIN KI KARANTA.
0069685771
AISHA ADAM STANBIC

Yusra ce ta shigo É—akin, Shukura ta yi tsuru da ido tana kallonta.
Yusra ta ƙarasa gaban gadon Shukura cikin damuwa ta ce "Meyasa ki ka taho nan, ki ka saka ake ta neman ki, duk hankalin mutane ya tashi?"
Maimakon Shukura ta bata amsa sai cewa ta yi "Ke kaÉ—ai, ki ka yi driving ki ka zo nan? Ina Baban Haidar É—in?"

"Wayarsa ce lalace, ya saka layin a wayata, yana can gurin meeting, kafin ya dawo kawai na ce bari na zo na ɗauke ki. Wannan ɗan da ki ka haifa ne?" Ta yi maganar tana karɓar jaririn hannun Shukura. Shukura ta jinjina kai jiki a sanyaye.
Yausra ta ƙura wa jaririn ido tana kallonsa, tana ɗan murmushi ta mayar da hankali kan Shukura ta ce "Wai meyasa ki ka zo nan gurin ki ka zauna?"
"Ba komai"
"A'a da komai, kowa kin saka hankalinsa ya tashi sosai, ga ki da tsohon ciki, ki tashi mu tafi gida idan ya dawo kawai sai dai ya ganki. Abbanki har yana cewa zai ɗaure shi, shi ne ya saka ki ka ɓata, ai ba dan ya dawo da ni ki ka tafi ba ko?" Ta yi maganar jikinta a sanyaye tana kallon Shukura.
Da mamaki Shukura ta ce "Daddyn ne ya ce zai ɗaure Sagir saboda ɓata na?"
Yusra ta jinjina kai ta ce "Wallahi haka ya ce"
Ta yi shiru tana zunzurutun ɓarna da zaluncin da ya gaya mata ya aikata. Ta numfasa ta ce "Amma ina fatan ba ki gaya wa kowa ina nan ba?"
"Babu wanda na gayawa, ai kin ce kar na faÉ—a, ga abinci can ma na É—aukko a mota, da 'yansanda zan gayawa amma na fasa"
Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yauwwa gara da ba ki faÉ—a ba"
Yusra ta ce "To ki taso mu tafi"
"A'a ai sai an sallame ni tukuna, kuma yakamata ki koma gida saboda ki sanar masa inda nake"
"Babu inda zan koma, salon in tafi ki sake guduwa" Ta yi maganar tana ƙara lulluɓe jaririn Shukura da yake hannunta.

*****
Cikin damuwa Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, yadda take zubar da yawu tana wani irin ihu, da gurnani duk ta yi najasa a jikinta.
Ga ƙafafuwanta sun shanye, ba ta gane kowa sai wannan gurnanin da take yi. Likitoci sai dai su ta mata allurar bacci. Ranar da Fadila ta je duba ta, duk da ba ta magana amma tana ganinta tare da Muhsin ta din ga ihu tana tsine masa tana faɗin "Da tuni wannan shegen ɗan ne zai mutu ba Abbana ba, Allah ya isa ba zan yafe ba" Alhaji Fatuhu yana gurin, ya yi mamakin jin irin wannan maganganun da take yi, amma sai ya bar hakan a sakamakon taɓuwa da aka ce ƙwaƙwalwarta ta yi.
Likitan da ya kammala rubutu a kan takarda, ya miƙa wa Alhaji Fatuhu. Alhaji Fatuhu ya karɓa tare da kallon Likitan ya ce "Doctor haryanzu ba a gano takamaiman abin da yake damunta ba?"
"To, duk wani abu da yakamata mu duba mun duba, jininta lafiya kalau ba ta da hawan jini. Babu alamar strock a tare da ita. Sai dai idan sakamakon gwaje-gwajenta ya kammala bamu ga komai ba, zamu tura ku ɓangaren ƙwaƙwalwa dama mu nan mun riƙe ta ne domin mu gano maƙasudin shanyewar limbs ɗinta, to haryanzu ba a gano komai ba, zuwa ranar Litinin zamu fara tura ku physiotherapy ko Allah zai sanya a dace"
Alhaji Fatuhu ya jinjina kai cike da karaya, tabbas da lokacin da yake da kuÉ—insa ne, da kansa zai fitar da ita waje a duba ta. Ko a yanzu ba ya jin daÉ—in yadda da kuÉ—inta ake nema mata magani.
Haka ya tafi gida jikina a sanyaye. Alhamdillah jikinsa ya yi kyau sosai, duk da haryanzu da sanda yake yawo bai gama warewa ba, amma yana iya fita shikaÉ—ai.
'yarsa Rauda ya samu a gida yake ta yi wa faɗan rashin zuwa duba Hajiya Sa'a da ba son yi. "A ƙa'ida kamata ya yi a ce ke ce a gurinta Raudah, kina kallo lokacin da nake kwance kullum tana tafe"
Rauda ta ce "Daddy ni wallahi tsoron ganinta nake yi, kuma duk lokacin da muka je da Maman Muhsin, sai ta yi ta ihu tana tsine masa tana da tuni shi ya mutu ba É—anta ba, ta yi ta ihu tsoro take bani"
"To Raudah ai larura ce, ni da Allah ya jarabbe ni, ba har wari na din ga yi lokacin da nake kan fama da larura ba. Jarrabwa ce Allah ya jarabce mu, kuma ku da ku ke kusa da mu, ku ne zaku ƙarfafa mana gwiwa. Ku din ga haƙuri". Ta jinjina masa kai kawai ta ce "To"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.