Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 5 of 99

Ya dube ta ya ce "To dan yana mijinta kar na zarge shi? Duniyar nan fa babu abin da ba zai iya faruwa ba, ni bincikena ba zai bar kowa ba, ya zama dole a binciki kowa, kuma ki rabu da ni da abin da yake damuna, ki ƙyale ni da maganar sani mijin Shukura"

Ta ce "Shikenan, ni ina gudun kar daga baya a zo a ji kunya ne"
Ya É—an É—ago da sauri ya ce "Me ki ke nufi?"

"Ahh a zo a ganta a gano ba shi da hannu a ciki, su ci gaba da zama da matarsa kai ka zo ka na jin kunya"

Ya yi guntun tsaki, yana sake miƙe ƙafafuwansa a kan gadon.

*****
Jamila ce a kwance dare ya tsala, amma ta yi ƙurii tana kallon roofing ɗakin.
Tun da Abba ya koma ga Allah, bacci ya ƙaurace wa idanunta. Idan kuwa bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, to tabbas mafarkin Abba za ta yi ta yi, tana ganin sun yi aure ga yara ta haifa masa.
Sannu a hankali ta tafi tunanin abin da ya faru. Bayan da Hajiya Sa'a ta yi mata bayanin yadda za ta sadaukar da ɗan gidan Alhaji Fatuhu ƙaninta.
Abin ya dame ta, ga shi ta san idan ta je ta sanar wa su Alhaji Fatuhu, asiri ne zai tonu har ita, kuma ma mene ne shaidarta, dan ta san tsaf Hajiya Sa'a za ta zame ta bar ta a ciki.
Ta yi tunanin ko ta sace 'yar tsanar, amma ta fasa, saboda yadda ta rabu da ta ta da ƙyar.
Bayan fitar Hajiya Sa'a, Jamila na kwance a falo bacci ya ɗauke ta, ta yi mafarkin 'yar tsanar nan a ƙone ta yi baƙi ta biyo ta tana ƙoƙari shige mata cikin riga tana wani irin kuka tsiii-tsiii. Cikin ihu ta tashi a razane. Lokacin Abba ya shigo ɗakin, kawai ta cakume shi tana ihu.

"Ƙanwata lafiya kuwa?"
Ya yi maganar yana kallonta, a hankali ta cika shi, ta nemi guri ta zauna ta ce masa tsorata ta yi a bacci. Ya zauna yana yi mata nasihar mafarki ba gaskiya ba ne, kuma ta din ga addu'a, idan ba haka shaiÉ—anu za su iya shiga jikinta saboda wannan tsoron da take ji.
Sai dai har ta tafi gida, a tsorace take kuma tunani take yi, yaya za ta yi ta tseratar da É—an Alhaji Fatuhu.
Ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga 'yar tsana ta sako ta a gaba a mafarki, yanzu bin ta take yi da sata sharɓeɓiyar wuƙa a mafarkin za ta kashe ta.
Kawai ta yanke wata shawara a ranta, wajen ƙarfe sha ɗaya ta je gidan Hajiya Sa'a, lokacin bata nan ta fita gantalinta, cikin sa'a ta duba inda ta ajiye 'yar tsanar da tarkacen kayan tsafin ta ga su na nan.
Ta kira Abba a waya, bayan sun gaisa ta tambaye shi yana ina, ya ce mata ya tafi kasuwa ta ce masa ya zo tana gidansu tana son ganinsa.
Ba a yi awa ɗaya ba sai ga shi ya dawo, har da tsaraba ya sayo mata, cike da murnar ganinta, dan kwana biyu ta ɗauke ƙafa da zuwa gidan.
Yanayin walwalar da ta gani a fuskarsa sai ta ji dana sanin kiransa da ta yi.
Sai dai ya takura mata a kan lallai sai ta gaya masa abin da ya sanya ta kirawo shi.
Ta É—ebo tarkacen nan na kayan tsafin Hajiya Sa'a, ta Zazzage masa a gabansa.

Cikin mamaki ya dube ta ya ce "Mene ne wannan haka?"

Ayshercool
08081012143

79
Tabbas ba ka san ko mene ne ba, kuma na san za ka yi mamakin mene ne wannan ɗin, amma ina mai baka haƙurin abin da zai fito daga bakina, ba ni da wani zaɓi ne nima, ina son yin ceton rai, na rasa wanda zan gayawa ya fahimce ni ya sama mini mafita ya rufa mini Asiri sai kai" Ta yi maganar cikin kuka.

Cikin damuwa da ƙaguwa ya ce "Babu komai, ko mene ne gaya mini. Wallahi Jamila ina jin ki a raina fiye da yadda ki ke zato, ki gaya mini dan Allah"
Ba ta tsallake masa komai ba, tun daga tariyar Maman Khairat a unguwar su, da fara zuwa gidanta zuwa haɗuwa da Hajiya Sa'a, ta gangaro har kan neman jinin Nana yadda suka saka ta a ƙungiyar asiri abin da aka yi mata, hatta labaran da Hajiya Sa'a ta ba ta na yadda ta shiga ƙungiyar sai da ta gaya masa.

Jamila za ta iya cewa tun da take, ba ta taɓa ganin idanun ɗan Adam sun yi jan da na Abba suka yi ba.
Ya ƙame a guri ɗaya tamkar babu rai a jikinsa.

Cikin rikicewa ta ce "Dan Allah Yaya Abba ka yi haƙuri ka yafe mini, ban gaya maka dan na haɗa ka da mahaifiyarka ba ko makamancin haka, ceton rai nake fatan mu yi, bawan Allah nan da yake rashin lafiya kar ya kuma rasa ɗan sa. Kuma dama ni na san mutuwa zan yi, dan ba zan iya bayar da kowa ba ga barazana kuma da ake ta yi mini a mafarki. Dan Allah ka yafe mini ban faɗa dan na haɗa ka da mahaifiyarka ba.

Idanunsa suka fara tsiyayar da hawaye, yayi kuka, ya yi kuka, Jamila kuma ta kasa rarrashinsa, can ya ce "Tabbas! Biri ya yi kama da mutum, yanayin facakar da Mummy take yi da kuÉ—i tamkar ba ta san zafin neman su ba abin yana É—aure mini kai. Ina kula da harkokin kasuwancinta, amma na san abin da take kashewa ya ninka abin da muke samu. Kuma duk yadda zan bi na gano wani abu sai ta toshe.
Jamila na ji daɗi sosai da sosai, da ba ki gaya wa wani abin da take aikatawa ba, kuma na ji daɗin ƙoƙarin kare kisan ɗan ɗan uwanta. Amma na yi mamakin yadda ta iya bayar da mahaifinmu saboda abin Duniya.
Ita ma idan ba ta sadaukar da kowa ba mutuwa za ta yi ko?"

Jamila ta jinjina masa kai tana kuka.
Ya ce "Shikenan, babu komai, ki daina kuka, daga ke har ita ba zaku mutu ba, zan zama abin sadaukarwar ku, sai dai daga ni ina fatan duk yadda za ki yi ki fita daga cikin kungiyar nan. A razane Jamila ta ce "A'a ba zai yiwu ba, ban gaya maka dan ka É—au wannan É—anyen hukuncin ba, mafita zaka nemo"

Abba ya ce "Wace mafitar Jamila? Na nuna wa Mummy na san abin da take yi? Ko na bari ke ko ita wani ya rasa ransa? Ko kuma É—an Kawu Fatuhu da bai ji ba bai gani ba? Dan Allah Jamila duk yadda za ki yi kar ki yadda ki bayar da jinin wani, ki kuma bar kungiyar nan. Wallahi Jamila kuÉ—i ba su ne kwanciyar hankali da nutsuwar É—an Adam ba."
"Yaya Abba to me zaka yi?"

"Ni zan zama abin sadaukarwar taku?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba zai yiwu ba gaskiya, na bayar da jininka kenan, ai gara ni na bayar da jinina ba zai yiwu ba"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.