Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 18 of 99
Imam da kansa ya saka Nana a cikin mota, ya babbake ya hana kowa ya taɓa ta. Ya rufe motar ya zagaya zai buɗe ɗaya ɓangaren ya shiga, amma wasu manyan hadimai suka tsare ƙofar.
Ya kalle su ba tare da ya yi magana ba.
ÆŠayan ya ce "Tuba muke yi, umarni ne daga sama, cewar kar a kuskura a bari ka bar gidan nan"
Cikin mamaki ya ce "Daga sama gurin wa?"
"Daga sama gurina, kar wanda ya bar shi ya fita ko ina daga gidan nan, har sai mun bayar da umarnin hakan, ku kaita inda muka yi umarni, za mu sanya a mayar da ita Nigeria. Ina sake jaddada muku, kar wanda ya kuskura ya bar Imam Hammad ya fita daga gidan nan sai mun ba da damar hakan" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni, aka ji motar da Nana take ciki aka fita da ita daga gidan.
Da ya san haka abubuwan nan za su kasance, da babu abin da zai hana ya ɗauki Nana da ɗansa ya bar musu ƙasar gaba ɗaya. Sai dai halin da Sultan zai shiga kawai yake tunani.
Cike da baƙin ciki da takaici, ya koma ya iske Sultan, gabansa ya je ya tsaya cikin tashin hankali ya ce "Me yasa za ka yi haka? Idan ni ne a matsayin da take za ka so a yi mini haka? Ka kalli lamarin nan a matsayinka na uba, ba Sultan ba. Dokar masarauta ba dokar addini ba ce ba. Me yasa 'yan majalissarka za su ziga ka ka yi haka? Babu wata hujja da ake buƙata domin tabattar da Asma'u matata ce, Mahmoudu su suka ɗaura mini aure. Shi ma kun ce a kulle shi ya yi laifi. Aure muka yi da Nana ga yarona ku na gani me yasa za a raba ta da ɗanta kuma a mayar da ita Nigeria haba Abie"
"Hammad, ni ka zo gabana ka tsaya ka na gaya mini magana a haka saboda mace? Dole ne mu girmama tare da martaba al'adun masarautar nan, mu samu mu binne babban kuskuren da ku ka aikata ko dan tsira da mutuncinka.
Hammad ya girgiza kai ya ce "Sultan, Asma'u ba mace ba ce kawai, ba zan binne laifukana saboda al'ada na je lahira ba ni da abin da zan gaya wa Allah ba. Zan ɗauki matata na bar ƙasar nan gaba ɗaya. Na bar muku sarautar da al'adar. Da na rayu babu su ma babu abin da ya same ni, ka gafarce ni"
Mari Sultan ya kifa masa, ya janyo rigarsa yana kallon sa ya ce "Ko ka fara shan wani abu ne Hammad? Ni ka ke gaya wa ka bar mana sarautar za ka ɗauki wata bare ka bar ƙasar nan?"
Jiki a sanyaye ya ce "Ba bare ba ce ba, matata ce kuma akwai ɗa a tsakaninmu. A halin yanzu a Duniya bayan kai ba na tunanin akwai wani wanda zai iya yi mini abun da ta yi mini. Gaskiyar da ba ka sona faɗa Abie ina tare da baƙin aljani, da yake burkita ni. Nana na iya ganinsa kuma itakaɗai take iya fahimtar halin da nake ci. Abie Nana ba mace ba ce kawai, waliyya ce a cikin mata, har shanyewar ɓarin jiki na yi, lokacin da ku ka gano su Mahmoudu aka ɗauke su, ba ta da wani mataimaki sai Allah kuma ba ta taɓa gajiya da ni ba. Asma'u har najasata ta wanke da hannunta. Da jikinta da lafiyarta da lokacikta da zuciyarta ta rayu da ni cikin kulawa da tausayawa. Idan na bari aka yi amfani da rashin gatanta saboda ni shafaffe da mai ne aka cutar da ita ban yi wa kaina adalci ba. Tsakanina da ita ba alaƙa ce gangar jiki ba kawai, akwai tasirin ruhika, da kuma tasirin alaƙar uba da ɗa. Wannan wani abu ne da ni da ita ne kawai muka sani. Abie ba za ku iya raba ni da Asma'u ba, idan ma ku ka raba mu, sai kun nemo ta da kanku" Ya ƙarasa maganar yana ja da baya ya fice ya bar ɗakin.
Sultan ya dafe gaban goshinsa da yake yi masa wani irin raÉ—aÉ—i, ya nemi guri ya zauna. Duk yana jin maganganun Hammad a matsayin soki burutsun neman mafitar yadda zai samu ya zauna da Nana.
Shi ma yana ganin ba a kyauta ba, a ƙwace mata yaro kuma a kore ta.
Asal kuwa tana can ta gigice, bayan da ta samu labari cewar, an ga Hammad da wata mata ya riƙe hannunta sun shiga sashen Sultan. Ta rasa wa zata dosa domin ta ji gaskiyar lamarin.
Tana cikin wannan gigitar, Tafawa ya kira ta, ta É—aga jikinta yana ta tsuma.
Ya ce "Asal, wace hadima ce a gidanki, ta kai abinci lokacin da su Asad suka zo?" Sai ta manta me ma ake nufi da hadima, sai da ya yi mata tsawa sannan ta farga ta ce "Wata hadima ce a gidan nan. Ce mini a ka yi an ga Imam Hammad da wata ya riƙo hannunta sun shiga sashen Sultan, ko ka na da labarin wace ce?"
Ya ja tsaki ya ce "Sai me kuma? Ina tambayarki ki na tambayata wani abu daban."
"Abbu dan Allah ka gaya mini idan ka san wani abu, ka ga ka ce mini ya ce yana da É—a, a tsorace nake"
Tafawa ya ce "Asal, kina nufin kina son Hammad ne?"
Cikin kuka ta ce "Abbu mijina ne fa, ko ba na son sa ina duba makomata nima" Sai dai tana rufe bakinta, Hammad ya banko ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske.
A razane ta saki wayar hannunta, ta waiwaya tana kallon sa.
Da sauri ta tunkare shi tana faɗin "Hammad wace mata a ce an ganku kun shigo tare yau, har kana riƙe da hannunta kun shiga sashen Sultan? Kar dai maganar da aka gaya mini gaskiya ce?" Ko kallon inda take bai yi ba ya nufi kan gadonsa ya faɗa kai.
Ta nufe shi a hasale ta ce "Ka tashi ka yi mini bayani, wace matar a ganku tare? Kuma da gaske ka na da ɗa ko ba ka da shi? Yanzu da mutuncinka da kimarka ka zaɓi ka tozarta kanka ka kwanta da wata mace a waje dan ta haifa maka ɗa. Wallahi Hammad baka isa ba, ina yi maka rantsuwa da zatin Allah kowace matar ce sai na sanya an kashe ta, kuma an kashe mini banza dan duk cikin Agadez da kewayenta na san duk wata 'yar gata a bayana take. Ka tashi ka yi mini bayani"
Wuyanta ya damƙa, jikinsa na wata irin tsuma, gani ta yi gaba ɗaya ya canza ya koma kamar wani horo, jikinsa ya koma jajawurr tamkar tumatir. Babu baƙar ƙwayar idanunsa sai farar nan tas, duk wata jijiya da taje jikinsa duk sun kumbura. ya faɗo daga kan gadon yana burgima, saboda yadda yake jin tamkar wuta na ci a ƙasan fatarsa.
Tofa!
Ayshercool
08081012143.
Kar dai ku gaji da ni, ina yi muku tuni da cewar labarin Buzu ya shiga gasa a YouTube channel ɗin limamin tsakar gida, wanda da yawan likes na kashi goman farko za a yi amfani gurin alƙalanci. Ku taimaka ku je ku danna like a kashi goman farko na labarin BUZU na gode.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.