Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 11 of 99
Ta zuba wa ledar ido, bayan da ya fito da gasassun zabi guda biyu, babu abin da ya faÉ—o ranta, sai zaman su a gidan Hajiya Halima, lokacin da ya saka Habu ya kawo mata zabbi gasassu.
Ya kalle ta ya ce "Ko na dafo miki shayi?"
Ta girgiza kai ta tashi tsaye. "ina za ki je?"
"ÆŠakin da nake zan koma,a can zan ci" Ta ba shi amsa ciki-ciki.
"To mu je can ɗin, nima ban ci komai ba, wataƙila idan muka ci tare, zan iya sakin jiki na ci Abincin"
Nana ta ƙara haɗe rai ta ce "Ni fa ba zan ci wani abinci tare da kai ba, bana buƙatar duk wani abu da zai ƙara kusanta ni da kai. Ni a yanzu neman maraba nake yi da kai".
"Neman maraba ki ke yi da ni?" Ya yi maganar yana murmushi mai ciwo, daga bisani ya ce "Shikenan, É—auki abincin ki je ki ci, sai ki kwanta ki huta" Ya tashi ya bar mata falon.
Ta tattare kan kayan abincin, ta tafi É—akin da aka ajiye ta.
Sosai ta fara ƙoƙarin cin abincin, saboda azabar yunwar da take ji, sai kuma ta tuna da gaske idan ba ta yi girki ba, ba ya cin abincin.
Kenan tun da ta tafi bai ci cikakken abinci ba kenan ko yaya? Wata zuciyar ta tambaye ta.
Har za ta yinƙura ta tashi, sai ta tuno batun cikin da ya ce tana da shi. A take wani malolon takaici ya ƙule ta, ta ƙuduri aniyar sai ta yi dalilin zubewar cikin nan.
To tayaya ma za a yi a ce ina da ciki? Yaushe kuma ta yaya?" Ta tambayi kanta.
Gaba ɗaya ta ji kanta yana juya mata, dan haka ta haƙura da tunanin, ta je ta wanke hannunta ta ta rufe abin da ta rage ta kwanta.
Sai dai ta ƙi yadda ta yi bacci, saboda gudun kar ya biyo dare ya zo ya yi yinƙurin yi mata wani abin.
Sai dai ko mintuna goma ba a yi ba, ta tsinci kanta a cikin Libraryn Ƙaisar.
Ta gan shi a kwance a kan wani gado, ya lulluɓa da wani baƙin mayafi.
Ya kalli fuskarta da ke É—auke da damuwa ya ce "Ya dai?"
Ta Numfasa ta ce "Ya na gan ka a kwance a nan?"
"Eh to zan yi ta zama ba zan kwanta ba ne?"
Ta ce "A'a, amma galibi sai ba ka da lafiya ka ke kwanciya a nan gurin"
"Lafiyata ƙalau. Na ɗauka zan gan ki cikin murna da farin ciki, tun da mijinki ya dawo hayyacinsa ya gane ki, sai kuma na gan ki cikin damuwa?"
Ta nemi guri ta zaune a gefen Ƙaisar ta ce "Ni fa ba na ƙaunar mutumin nan, fatana kawai ya bani ɗa na, na koma Nigeria Ubangiji Allah ya sanya su Baba su yafe mini, ina kyautata zaton alhakinsu ne ya kama ni"
Ƙaisar ya ce "Waye ba kya ƙaunar yanzu?"
"Sayyid"
"Ƙarya ki ke yi" ta ce "Ƙarya kuma?"
"Da dai ban san halinki ba ne"
Cikin sanyin jiki ta ce "Da gaske nake, ba wasa nake yi maka ba. Ba na ko ƙaunar jin sunansa, ya yaudare ni, sun cutar da ni. Gaba ɗaya kimarsa da son da nake yi masa sun zube a idanuna"
Ƙaisar ya yinƙura ya tashi zaune, yana ƙara rufe jikinsa ya ce "Tun da ya ce ki saurare shi, ki tsaya ki ji mai zai ce miki mana. Kar zuciyar da ki ka yi ta sanya ki yanke hukuncin da ba zai ɓulle muku ba"
"Ni fa babu abin da zan ji daga bakinsa, ba na buƙatar sa a rayuwata gaba ɗaya" Ƙaisar ya yi murmushi yana gyara zamansa a hankali. Idon Nana ya sauka a kan Jakar Sarkin baka da ke gefen gadon da yake.
"Ƙaisar, me ka ke yi da jakar Sarkin baka?" Ya yi mata shiru kamar bai ji ta ba.
Miƙewa ta yi da sauri ta ce "Wani abu ya faru tsakaninka da Giyaz ko?"
"A'a aron jakar na yi, wani aiki na yi da ita".
Nana ta saka hannu ta É—an ja mayafin da ya rufe jikinsa da shi, wani irin haske ne ya haske mata ido, daga bisani hasken ya ragu a hankali.
Jikinsa ya yi wani irin kore-kore, wani gurin kuma ya yi baƙi ƙirin tamkar an ƙona shi.
Nana ta ce "Meyafaru? Me ya same ka haka? Giyaz ya yi maka wani abu ne?"
"Babu abin da ya faru, zan dawo miki da jakar ki kuma, ki je sai na sake neman ki" Nana ta farka daga baccin da take yi, fuskarta duk hawaye.
Gaba É—aya jikinta a sanyaye ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili, sannan ta gabatar da sallar asuba.
Har gari ya yi haske, tana zaune a ƙasa. Shiru ta yi tana tuna yadda ta ga jikin Ƙaisar, sai ta ji abin ya dame ta sosai da sosai.
"Mene ne makomar wannan sakankancewar da nake yi da Ƙaisar yanzu? Me yasa kuma yake taimakona a wasu guraren? Anya ba wani tarkon na yaudara ya yi mini ba, yake son na afka ya yi amfani da damar ba? Ko ma dai yaya ne, Ubangiji Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abin ƙi." Sosai take son mantawa da tunanin Ƙaisar, ta koma tunanin Muhsin, da wannan balahirar ta gabanta, amma abu ya ci tura, a jikinta take jin Ƙaisar, take jin ta damu da halin da ta gan shi a ciki.
Sallamarsa ce ta katse mata tunani, ta amsa masa ciki-ciki. Ya je gabanta ya ajiye tray. Ya É—an tsura mata ido ya ce "Barka da safiya Rayuwata" Wani mugun kallo ta yi masa, haÉ—i da uwar harara.
Ya yi murmushi ya ce "Ga abin karyawa nan, kar ki manta sakin jikinki, da cin abincinki ne zai sanya ki ga É—ana"
"Ka daina danganta mini ɗana da kanka, ba shi wata alaƙa da kai" Ta yi maganar cikin tsiwa.
"Ba shi da alaƙa da ni, sai da Ƙaisar?" Ya yi maganar ya kallonta yana murmushi. Bai ba ta damar ba shi amsa ba ya ce "Yau zan koma gida, zan je na ji yadda za mu yi da su Sultan, amma ki nutsu ki kwantar da hankalinki dan Allah"
"Ba ni da wata nutsuwa ko kwanciyar hankali, idan ba É—a na na gani ya zo hannuna ba".
Ya yi shiru yana tsare ta da idanunsa.
Ta É—aga kai ta kalle shi, ta ji gabanta ya faÉ—i, ta rasa gane wane irin kallo ne yake yi mata haka.
Ta sunkuyar da kanta tana haÉ—e rai.
Ta sake ɗaga ido ta suka haɗa ido, ya yi mata murmushi, ya ce "Ma vie, ban san daga ina nake jin ƙaunarki ba a rayuwata, kar ki hukunta ni da abin da ki ka gani kawai a zahiri. Ina sake roƙonki, ki bani dama ki ji ta bakina"
"Ni babu abin da zan ji, na ce maka ɗana kawai nake buƙata"
Ya shafi sajensa ya ce "Muhsin ai nawa ne ni da Asal. Idan ki ka haihu kuma nawa ni da ke, shi ma idan ba kya so sai ki bani abina"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.