Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 27 of 99
****
Mahmoudu ya dawo, ya kai wa Nana shayi da kayan marmarin da ta ce . Sai kuma kayansu da Alƙur'ani. Ya haɗu da Sultan a hanyar da suke bi su shiga gurin. Domin wani sashi ne a can cikin sashensa da ba kowa ma ya san da shi ba. Hatta iyalansa sai da izninsa suke zuwa gurin. Wasu lokutan ya kan sanar da ya yi tafiya, ya tafi cikin gurin ya kulle kansa ya samu hutu da nutsuwa.
Mahmoudu ya ƙarasa gabansa cikin girmamawa.
Ya ce "Abincin ka kawo musu?"
"Eh ranka ya daÉ—e"
Sultan ya numfasa ya ce "Shikenan, amma ina fatan babu wata matsala barinsa tare da yarinyar nan, duk da na fuskanci tana da hankali akwai abubuwan da take ɓoyewa. Ni kaina ba komai nake son kowa ya sani ba"
"In sha Allah Sultan, kare martaba, mutunci da kuma sirrikan Imam Hammad abu ne da ya zama wajibi a gare mu. Kuma tabbaci nake da shi ba yaƙini nake da shi, ba za ta taɓa aikata wani abu da zai cutar da shi ba"
Ya jinjina kai ya ce "Na ga alamun haka, duk da na ga wasu abubuwa na ban mamaki a tattare da ita. Dama Hammad ya gaya mini sai mun neme ta, amma ban ɗauki zancen nasa da wani muhimmanci ba. Akwai wasu abubuwa da ya gaya mini da ban gama gane ma'anarsu ba, amma bari mu jira mu gani ya samu sauƙi"
Mahmoudu ya risuna ya ce "Godiya muke ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon kwana" Ya ɗaga wa Mahmoudu hannu.
Nana na ganin Mahmoudu ta yi ajiyar zuciya, domin shi take ta jira ya kawo abin da za ta ba wa Hammad ya saka a cikinsa. Yana kwance a kan cinyarta tana shafa gashin kansa.
Ya ajijiye mata kayan, Nana ta ce "Sannu da ƙoƙari, Ubangiji Allah ya biya ku da kai da mahaifiyarka, na fuskanci kirki da karamci a jininku yake, gado ka yi Nene akwai kirki"
Ya ce "Allah ya taimake ki, ai kin ƙwace mini ita" Nana ita abin dariya yake bata, idan ta ji su na girmamata.
Ta ce "Sayyid, ga abinci an kawo tashi ka ci" Mahmoudu ya taimaka mata, ta zaunar da shi. Ta zuba shayin a kofi, ta fara ba shi a hankali da cokali.
Duk da wata irin yunwa da yake ji, tamkar ya haɗa da Nanan ya cinye, amma haka ya daure ya din ga karɓa a hankali.
Ta ce wa Mahmoudu "Ka je ka samu ka huta, amma dan Allah ka zo da wuri, ka san ni da kai na saba, kuma kai kaÉ—ai nake jin zan iya sakin jiki da kai. Sannan dan Allah abincinsa kar a bari ya biyo ta hannun kowa, ta gurinka kawai"
Ya ce "In sha Allah, zan yi yadda ki ka ce, sai da safe"
Sosai ya din ga cin kayan marmarin nan, yana sake shan shayin girfae da Habu ya kawo. Sai da Nana ta lura jikinsa ya daina rawa. Ya ɗan huta sannan ta tashi tsaye ta ce masa "Sayyid yinƙura a hankali ka tashi mu gani"
Ya dafa gadon, ya tashi a hankali amma ya ji kamar kayan cikinsa zai zubo. Ta riƙe hannunsa yana durƙushe yana tafiya a hankali.
Ƙofar banɗakin suka je, ta tsaya ta kalle shi ta ce "Mun yi wanka a Nigeria, yau za mu yi a Agadez ko?"
Murmushi ya yi mata sai da haƙoransa suka bayyana. Suka shiga banɗakin. Sai dai wata irin kunyarsa da ba ta san daga ina ba, ta bujiro mata. Za ta iya cewa yau jiƙa-jiƙa kawai ta yi masa, saboda yadda ya ƙara yi mata kwarjini take ganin kamar wani aka canza mata. Babban abin da ya ƙara takura ta, shi ne kallon da yake ta bin ta da shi, kamar zai lashe ta. Da kanta ta yi masa brush, hakan ya din ga tuna mata da rayuwarsu ta Nigeria.
Ta saka ya yi alwala, suka dawo É—akin ta saka masa doguwar rigar jallabiya. Ta ce "To an ce kwananka takwas baka hayyacinka, yanzu zaka lissafa sallolin da suke kanka. Ka yi wanda zaka iya yanzu sauran sai ka ci gaba ko gobe in Allah ya kaimu ne"
Ya jinjina kai, ya kalli gabas daga zauna ya tayar da salla, saboda ba zai iya tsayuwa ba. Nana ta din ga tunani ko ta roƙi alfarmar su nuna mata ɗanta ta gan shi, tun da nasu ɗan ya farfaɗo, amma wata zuciyar ta hana ta hakan, duk da tarin kewar Muhsin da take yi. Ta shiga banɗakin ita ma, ta yi wanka ta gama ta sako hijjabinta ta fito.
Jakar kayanta ta buÉ—e, tana duddubawa, ta ga magungunan da Nene take bata na sha da wanka a ciki.
Kawai ta yi murmushi ta shafa mayukanta, ta duba kaya masu sauƙin nauyi dan ta saka, dan duk da ba shi da lafiya ba za ta kwana shimfiɗa ɗaya da shi ba, da haryanzu ba ta san matsayinta ba, da matsayin kawo ta gurinsa ba, duk da da aka zo ita ta nema. Ga uwa uba rashin tabbacin da gaske tana da juna biyu ko kuwa?.
Ta sakankance da salla yake yi, saboda a bayansa take zaune tana ƙoƙarin canza kaya. Kawai ta ji ya faɗo jikinta, suka faɗi ƙasa a gurin, hasken wutar ɗakin ya ɗauke baki ɗaya duhu ya mamaye ɗakin.
Ayshercool
85
LITTAFIN KUÆŠI NE, KI BIYA KUÆŠIN KARATU KAFIN KI KARANTA. VIA 0069685771
AISHA ADAM STANBIC BANK
08081012143
Nana ta razana ta ce "Sayyid lafiya kuwa?" Ya rirriƙeta jikinsa na rawa.
Nana ta yi shiru cike da damuwa, ga shi yanzu ta fara wahala da riƙon da yake yi mata, dan ya ninka wanda yake yi mata su na Nigeria. Haka ta haƙura ƙyale shi.
Can bayan wani lokaci, hasken ɗakin ya dawo, a lokacin ya samu bacci, Nana ta yi shiru tana tunani daban-daban a kansa. Tabba! Tana da tarin tambayoyi da take buƙatar samun amsarsu, daga gare shi, dan akwai tarin abubuwan da suke faruwa, da suke ɗaure mata kai.
Ta ture shi da kyar, ta tashi ta saka kayanta, ta kwanta a bayansa, tana jin yadda jikinta ya ƙara tsami da ciwo.
Sai dai bayan bacci ya ɗauke ta, ta din ga munanan mafarkai marasa kyau da ban tsoro a cikin baccin. Abubuwan da ta din ga gani a gidan, sun tsorata ta. Har da yaƙe-yaƙen da aka din ga yi, kafin kafuwar masarautar, da irin azabar da bayi suka sha haka ta din ga gani. Ban da miyagun Aljanu masu ɗauke da siffofi daban-daban na ban tsoro a cikin baccin.
Juyi ta din ga yi tana haÉ—a wani irin gumi, tana sauke numfashi saboda tsoro. Ga shi a baccin da fari a gefe take tana kallon abin da yake faruwa, kafin daga bisani ta ganta tsamo-tsamo a cikin rikicin da ake yi, daga bisani ma miyagun abubuwan suka din ga nufo ta. Cike da tashin hankali ta farka tana waige-waige. Amma ta yi ido huÉ—u da Hammad a zaune yana kallon ta, da alama ma sallolinsa ya yi.
Mamaki ya kama ta, yaushe ya tashi har ya yi alawala ya zo yana rama sallolin. "Sannu ya jikin naka?" Ya jinjina kai yana kallonta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.