Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 29 of 99

*****
Alhaji Fatuhu ne ya kira wani abokinsa, ya ce ya zo ya kai shi gidan Yayarsa Hajiya Sa'a a motarsa, saboda yadda baya samun ta kwana biyu a waya.

Ko da yaje gidan, mai aikinta ta sanar da shi cewa ta ce ko waye ya zo, kar a sake a dame ta.

Ya kalli mai aikin ya ce "Ko wannan dokar za ta yi aiki a kan kowa, ba za ta yi a kaina ba, dan haka yi mini magana da ita"

Mai aikin ta shiga ta fito, ta ce "Na yi mata magana ba ta kula ni ba"

Ba shi da zaɓin da ya wuce ya shiga ɗakin nata da kansa. Ya tarar da ita a zaune, daga mutuwar Abba zuwa yanzu ta yi wani irin tsufa, jikinta duk ya saki. Fuskarta duk ta yi wani iri kamar ba ita ba.

A hankali ya taka da sandarsa, sai ta ƙura masa ido tama fara tunanin a ina ma ta san shi? Gaba ɗaya sai kanta ya toshe ta kasa tuna waye shi.

Sai da ya ce "Yaya Sa'a, lafiya kuwa?" Yana yin maganar, sai kuma ta tuna shi. Ta yi zuru tana tunanin ya aka yi ya samu lafiya haka har yake iya takawa?

"Yaya Sa'a me yake damunki?" Ya yi maganar cikin damuwar halin da ya tarar da ita. Kawai ta fashe da kuka.

Cikin damuwa ya ce "Haba ke kuwa, kamar ba musulma ba, yanzu da ke Allah ya jarabta da halin da nake ciki yaya za ki yi? Dan Allah ki yi haƙuri mu ci gaba da yi wa Abba addu'a, amma wannan hanyar da ki ka ɗaukko, ba mai ɓullewa ba ce ba" Ya yi ta rarrashinta da lafuzzan ƙwarin gwiwa. Ya sanya mai aikinta ta kawo Abinci, ya tabbatar ta ci sannan ya yi mata sallama ya tafi. Sai dai bayan tafiyarsa sai ta hau tunanin abin da ya faru gaske ne ya faru, ko kuwa dai mafarki ne. Gaba ɗaya. Haka ta zauna tana ta lissafin yanayin.

*****

Bayan majalisar Sultan ta cika, domin ci gaba da gudanar da sha'anin mulki na Agadez. Akwai takardu da a kan turo domin gabatar da su a tattauna.

Mai karanto takardun ya warwareta, ya zuba wa takardar ido sannan ya numfasa ya ce "Zuwa ga Sultan da 'yan Majalisar sa baki ɗaya. Sanin duk wanda ya kwana ya tashi a Agadez ne, babu wani abu da muke martabawa, bayan addininmu kamar al'adarmu. Mu na kira ga Sultan da 'yan majalissar sa, su gaggauta duba ga al'amarin Imam Hammad. Babu yadda za a yi ya ci gaba da jagorantar majalissar Imam, ba tare da zoben tambari ba, wanda kawo yanzu babu wani cikakken bayani a kan inda zoben nasa yake. Sannan ya yi iƙirarin yana da ɗa, wanda haryanzu ba mu ji matsayar binciken da aka ce za a gudanar ba. A dan haka muke kira ga sauran 'yan uwanmu na majalissar Sultan, a gaggauta sanar da mutane sakamakon binciken da aka gudanar, sannan Imam Hammad ya fito gaban majalisar sarki, ya kare kansa, ko kuma ya sauka daga kan muƙaminsa na shugaban majalisar Imam, har zuwa lokacin da sakamakon binciken iƙirarin da ya yi na yana da ɗa zai fito. Idan kuma shaci faɗi ne abin da ya faɗa ta tabatta yana da matsalar ƙwaƙwalwa, kamar yadda jita-jita ta yi yawa.

86
A SAUKE HAKKI, A BIYA KUÆŠIN KARATU 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 08081012143
Gaba ɗaya tsit majalissar ta yi, aka rasa wanda zai sake cewa wani abu. Wani abu mai ɗaci ya tsirga wa Sultan a zuciyarsa, yana takaicin kasancewar Tafawa ɗan uwansa, yadda yake nuna son ganin bayan jininsa wato Hammad duk saboda mulki. Ya san ko ba a gaya masa ba, da saninsa aka rubuta wannan takardar aka kawo. Surutu 'yan majalissar suka fara yi ƙasa-ƙasa. Sardauna ya numfasa ya yi gyaran murya, duk aka yi shiru Sannan ya ce "Ina ga wannan maganar mun riga mun yi ta a baya. Ban ga amfanin sake dawo da ita ba, mu na nan ana kan bincike a kan al'amuran kuma za a zo da sakamakon binciken, sake dawo da maganar ba abu ne da zai taimake mu ba, duba da yadda muke da tarin abubu a gabamu, da yakamata a ce an mayar da hankali a kai"
Ɗaya daga cikin mutanen majalisar ya ce "A'a Sardauna, ba na tunanin wannan ba maganar da za a tattauna ba ce ba. Kar ka manta goben Agadez ta ta'alaƙƙa da waɗannan Imam da aka naɗa, su ma suke jagorantar wasu al'amuran na sha'anin sarauta, muddin aka ce da tangarɗa kuma ba a ɗauki wani mataki ba, to yana nufin goben ƙasar nan yana cikin hakin da ba a sani ba"

Matawalle ya ce "Turaki ai dama sanin gobe sai Allah. Mu muna bulayinmu ne kawai. Amma kamar yadda mai girma Sardauna ya ce, a jira sakamakon binciken ya fito tukuna. Sannan wani batun taɓin hankali da ake danganta Imam Hammad da shi, batu ne mara tushe balle makama, sannan duk wanda muka samu da yaɗa wannan zancen, za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kansa."
Haka aka so tayar da hatsaniya, sai da Sultan ya tsawatar, haka aka watse daga zaman babu wata ƙwaƙwƙwarar magana. Sultan ya san tabbas tun da  Tafawa ya samu magoya baya a Majalisa, al'amura za su sake dagulewa ne, kuma za su ci gaba da bibiya su ji ƙwal uwar daka.

*****

Shukura ce a kwance a ƙasa, sai burgima take yi, wani irin matsanancin ciwo yana ratsa ta. Sai jujjuya kanta take yi a galabaice. Kamar kullum mai ba ta abinci ya buɗe ƙofar ya ziro abincin ya ajiye mata ya tafi. Sai dai a duk lokacin da aka kawo mata abincin, idan aka rufe ɗakin duhu ne yake gauraye ko ina, amma sai ga yau da sauran haske. Ta ɗaga kanta a mugun galabaice ta kalli ƙofar ta ga kamar ƙofar ce ba ta rufu ba. Ta lumshe idanunta cike da azabar ciwo, wata zuciyar na azalzalarta ta je ta buɗe ƙofar ko a buɗe take, wata zuciyar kuma ta ce mata wahalar ciwo ne kawai amma ƙofar a rufe take. Ta ji ciwon na ƙara tsananta, yayin da wani abu mai ɗumi da ba za ta iya tantance ko na mene ne ba, yake bin ƙafarta.
Ta din ga jan jikinta a hankali, ta lalubi bango ta dafa, a durƙushe ta ƙarasa gaban ƙofar ta saka hannu ta ja, kawai ta ga ƙofar ta buɗe. Ta zura kanta ta lelleƙa ta ga babu kowa a harabar gurin, daji ne sosai aka yi ɗakin a cikinsa.
Tana faɗin "La'ila ha illa Anta Subhanaka Inni Kuntu mina Zalumin" Ta ci gaba da jan ƙafafuwanta tana takawa a hankali.
Ko da ta duba jikinta sai ta ga alamun faya ce ta fashe, ga ruwanan mai haɗe da jini a jikin ƙafafuwanta da rigarta. Ba ta damu da yadda take gani dishi-dishi ba, saboda azabar galabaitar da ta yi, da kuma haske da ya cika mata ido, kawai ta saɓi hanyar da ba ta san ina ne ba, ta hau tafiya. Duk da duk taku ji take yi tamkar ɗan cikinta zai faɗo saboda nauyin cikin da azabar ciwo. Tafe take tana addu'a Allah ya kuɓutar da ita.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.