Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 89 of 99

*****

Sayyid a gurin Asal yake, amma yaje yana damunta. Sai da ya fara shirin tafiya, ta ce masa ya jira tana da baƙi su gaisa.
"Suwaye baƙin kai a Agadez? Umma ce? (Da yake haka yake kiran Nene, kamar yadda Mahmoudu yake kiran ta)"
"Ba ita ba ce"
"To suwaye?"

"Baƙi masu muhimmancin gaske ne, za ka gani"

Ya ce "To bari na je masallaci, kafin su zo" Ya yi alwala ya fita falo, ya ga Nene tare da wata mata da namiji da alamu suka nuna mata da miji ne. Su na ganinsa suka ƙara nutsuwa, domin sukan ji zancensa a bakin Nene. Cikin girmamawa suka risuna su na gaishe shi. Ya amsa yana mamakin dalilin shigo masa da ƙato haka har cikin falo. Ya dake ya ce "Umma dama ke ce baƙuwar, ta dage kar na fita sai kin zo?"

Ta yi murmushi ta ce "Ba ma nice baƙuwar ba, ga baƙin nata nan" Ta yi maganar tana nuna masa mata da mijin. Ya yi shiru yana kallonsu, ba su yi kama da 'yan Nigeria ba, sun fi kama da hausawan Niger, mussaman daga yanayin hausar su.
Nana ce ta buɗe ƙofa ta fito, da gudu ta nufi Hajara ta rungume ta, Muhsin ya biyo bayanta ya ja ya tsaya a kusa da mahaifinsa.

"Hajara, dama zan sake ganinki?"

"Gani kuwa shugabata" Hajara ta yi maganar cikin girmamawa.

Nana har ƙasa ta durƙusa ta gaida Auwwal, takaici ya kama Hammad, haryanzu Nana ta kasa gane mene ne matsayinta. Banda haka ya za a yi ta durƙusa har ƙasa tana gaida mutumin da shi kansa ya girme shi, da ma dattijo ne da sauƙi.

Nene ta ce "Nana ba girmanki ba ne, ai shi yakamata ya gaishe ki"

Shi ma a tsorace ya ce "Wallahi kuwa"

"Kash, Nene ba ni da wani girma, ni na kasa jin girman nan. Meyasa ba zan girmama mutane mafiya karamci a gare ni ba?" Ta taso tana kallon Sayyid fuskarta sharkaf da hawaye ta ce "Wannan gidan su ne je, lokacin da na baro Agadez na nemi Nene na rasa, a can gidansu aka ɗaukko ni. Sayyid lokacin da na zo Niger na sauka a Maraɗi, ba ni da kowa sai Allah, Allah ya dubi zuciyata ya ji ƙaina ya haɗa ni da mutane masu karamci. Wannan su ne sanadin haɗuwa ta da Nene." Nan ta kwashe komai ta gaya masa. Sannan ta ɗora da cewa "Ina tambayar Nene su, ta ce mini sun tafi ci rani can ƙasar Mali. Sai yau Neme ta kira ni ta ce mini sun zo Niger, su na Agadez za ta kawo su mu gaisa. Ni na so mu je har inda suke amma ta hana" Kukan da Nana take yi kawai ya tabattar masa da ba ƙaramin karamci suka yi mata ba.
Ya taka ya ƙarasa gaban Auwall da kansa yake ƙasa, ya miƙa masa hannu su yi musabaha. Da kyar ya iya miƙo masa hannu.
Suka gaisa Hammad ya dafa kafaÉ—arsa ya ce "Na gode sosai da sosai. Mutane a zamanin nan abin tsoro ne, amma ka zama mutum na farko gurin bawa matar da baka sani ba taimako.
Na gode sosai da sosai, dama Umma uwata ce, kai ne dai ban sani ba, tabbas tana bani labarinku. In sha Allah ba zaka sake zuwa Mali ci rani ba, da yardar Allah  na gode sosai da sosai Allah ya biya ka"
Ya kalli matarsa ita ma ya yi mata godiya sosai.

Tare suka je Salla da Auwwal, Hajara ta yi nufin ɗaukar Muhsin, amma ya ƙi saboda ƙyuya.
Hadimai suka gabatar da Abinci, da abubuwan sha daban daban. Sayyid a dole yake ɗaga ƙafa a wasu abubuwan duk da azabar kishin Nana da yake yi. Ya yi iya ƙoƙarinsa a kan kar ya yi wani abu da ran su Auwwal zai sosu ko na Nene, ko dan albarkacin ɗawainiyar da suka yi da Nana.
Har da kyautar kayan wasan Yara, suka kawowa Yarima Muhsin. A hirar ta su suke gaya wa Nana haryanzu Allah bai ba su haihuwa ba. Ta yi ta musu nasiha da basu misalai masu kwantar da hankali.
Sai isha'i suka tashi tafiya, Hammad ya yi musu alkhairi, tare da jaddada musu godiya, ya kuma gaya wa Auwwal lokacin da zai zo MaraÉ—i, ya ba shi katinsa ya ce idan yaje ya nuna katin za a bari ya gan shi, zai ba shi abin yi.
Bangaren Nana ma, kyaututtuka ta ba wa Hajara sosai, da ta ce ba zata karɓa ba, abin da suka yi wa Nana, dan Allah suka yi mata, Nene ta ce mata ba a mayar wa da masu mulki kyauta.
Sai da Nana ta karɓi lambar wayar Hajara, ta din ga yi musu godiya kamar ta tsuguna musu. Hammad ya ɗauki Muhsin ya ce da kansa zai mayar da su har gidan da Nene take, kasancewar a gurinta suka sauka a Agadez. Daga can ya so wucewa gurin Asal da Muhsin dan yana kyautata zaton bata taɓa ganinsa ba, amma Nana ba ta sani ba, tsaf za su iya yin faɗa a kan hakan. Kuma da gaskiyar Nana kome nene Asal ce ta janyo, kuma duk abin da Nana za ta yi domin ta ba wa ɗanta kariya. Bugu da ƙari kuma ba ya son duk wani abu da zai kawo musu matsala, saboda wata irin kwanciyar hankali ya tsinci kansa a ciki. Ga taraiya da soyayya da yake samu daga gurinta. Duk da haryanzu Giyaz yana taɓa shi. Amma idan yana tare da ita, da ya gaya mata alamomin da yake ji, take yi masa addu'a ko ma muraran ta ga Giyaz ɗin tare da shi.
Ya tattara hankalinsa a kan Nana da ta nufo shi, ta sanya doguwar riga ta cika ta, rigar ta zauna a jikinta.
Ta ce "Wannan kallon sai ka saka na faɗi tukuna?" Yayi murmushi ya ce "Sai na riƙo ki kafin ki faɗin.
Ta yi murmushi ta zauna a kusa da shi, ta kai kofin hannunta bakinsa ya buÉ—e baki yana sha. Ta ce "Amma ka yi sauri fa"

"Eh, ina kai su na juyo ne, in sha Allah idan muka haÉ—u a MaraÉ—i, zan sama masa aikin yi"
"Gaskiya ka kyauta, Allah ya saka maka da alkhairi" Ta ci gaba da ba shi labarin irin taimakon da suka yi mata.
Ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Lokacin mu na Nigeria, ba wuya kin samu rabo, Allah ya sa Niger ma haka ne, Allah ya sanya ƙani ko ƙanwar Muhsin sun samu a cikin nan"
Nana ta tura baki ta ce "Sai Yarima ya shekara biyar"
"Wace shekara biyar kuma? Kowa so yake sai ya karɓe shi, Zahradeen nata masifa, ga Sultan ya ce gobe na kai masa shi, amma idan Allah ya sa ki ka haihu, ko an ƙwace shi mu na da wani ko?" Kawai ta yi shiru tana murmushi, dan ji take gara ta haifi wasu a ƙwace da a ƙwace mata Muhsin.
Su na hira ta É—auki wayarta, za ta nuna masa abu, sai dai tana buÉ—e data videon Alhaji Zailani ta fara cin karo da shi a dandalin sada zumunta.
Miƙewa ta yi tsaye jikinta na wata irin tsuma, kamar za ta zare. Ya karɓi wayar hannunta ya kalli videon. Ya ajiye wayar ya ce "Shiyasa wasu lokutan shafukan sada zumuntar nan duk ba su da wani amfani"
"Sayyid ba ka gane waye ba?"
Ya girgiza kai ya ce "Ni ban san shi ba"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.