Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 30 of 99

Alhaji Fatuhu kuwa bayan komawarsa gida su na hira da Fadila ya ce "Fadila yakamata ku je ku duba Yaya Sa'a, saboda tana jin jiki nesa ba kusa ba, duk ta rame ta fita daga hayyacinta. Ta bani tausayi sosai da sosai haryanzu tana jin raÉ—aÉ—in mutuwar nan"

Fadila ta ce "Allah sarki, har na tuna lokacin da na rasa Muhsin É—ina, da ta ce ba ni da tawakalli kamar a kaina a ka fara haihuwa, Allah sarki yanzu ta ji abin da na ji"

Ya tsuke fuska ya ce "A taƙaice dai, gaya mini magana ki ke yi"

Ta girgiza kai ta ce "Wace ni? Ai ban isa ba, kawai dai na tuna abin ne, kuma ya daÉ—e yana yi mini zafi"

"To koma dai mene ne yanzu ya wuce, zan gaya wa Suwaiba, yakamata ku shirya ku je ku duba ta, a yi mata sannu, idan babu hali ma ina ga gara ta dawo gidan nan da zama, wataƙila kai komonmu zai rage mata damuwa da kaɗaici"
Cikin sanyin ta ce "Ka manta ne? Ka manta mu ma a under notice muke, daga yanzu ko wani lokaci an ce mu fita mu bar gidan nan?"

Ya yi shiru ya tafi zancen zuci. Ta ce "Dan Allah kar ka É—aga hankalinka, mun samu Allah ya sanya ka farfaÉ—o da kyar. Ni da Maman su Janna za ta yarda da É—an abin hannuna da nata, mu samu ko karamin gida ne a saya, ni ba na son hayar nan ko É—aki uku ne mu koma"

Ya waro ido ya ce "ÆŠaki kuma? Ina É—aki uku zai ishe mu rayuwa? Ko sashenki É—akuna huÉ—u ne da falo biyu, ya yi mana kaÉ—an"

Fadila ta ce "Daddy ka manta wacece Fadilan taka ne? Sai dai ku ya yi muku wahalar rayuwa ai ni na riga na saba, gidanmu ma na da daka auro ni ai É—aki biyu ne ni da Umma"

Ya ce "Ki daina tuna abin da ya wuce mana, ni ba ga shi kin zamo mana alkhairi ba. Da na tsaya duba wani shrime da ƙyale-ƙyale da daga ke har Suwaiba ba na tunanin za ku kasance da ni, duk da halin da muka tsinci kanmu. Ina ƙara yi muku godiya sosai da sosai"

Fadila ta ce "Haba Daddy, ka cancanci fiye da haka daga gare mu, lokacin da ka ke da wadata ba mu ba, na kusa da mu ma ka yi musu, ka gatantamu ka kula da mu, sai Allah ya kawo mana jarrabawa kuma mu juya maka baya, da Allah bai barmu ba kuwa"

Ya ce "Ke dai a yi sha'ani masoyiyya, idan Allah yana ƙaunar bawa, idan ya jarrabe shi ta nan, sai ya sassauta masa ta can, da yawa idan larura ta same su, iyalan nasu barin su suke yi. Kin san wani abu kuwa?"
Ta ce "A'a sai ka faɗa Angona" Ya tuntsure da dariya ya ce "Ango ko?" Ta ɗaga masa gira tana murmushi. Ya ɗan ja kumatunta yana murmushi. Ya ce "Wannan rahar ma da nake yi da ke, ba tare da kin sauya mini ba saboda ba ni da lafiya, kuma ba ni da abin hannun yanzu ba, wallahi ba ƙaramin daɗi nake ji ba. Haƙiƙa larurar nan ta ƙara mini tsoron Allah da imani, ya ƙara kusantar da ni da Ubangijina, a duk lokacin da na motsa ambaton Allah kawai nake yi, gani nake rayuwata ce ta zo ƙarshe. Saɓanin lokacin da nake da dukiya da lafiya, ina ambaton Allah amma ba can sosai ba, ba kamar yadda na ƙara samun kusanci da Ubangiji ba lokacin da na rasa komai. Kuma a jikina nake jin wani tagomashin alkhairi yana kusanto mu in sha Allah"

Ta ce "Haka ake so Daddy, ina fatan kuma ka canza tunaninka a kan magungunan gargajiya da na addini yanzu"

Ya yi dariya ya ce "Na canza tuni, ke dai madalla da ke matar aljanna" Suka ci gaba da hira cike da nishaÉ—i.

*****

Kwanakin Nana uku tare da Hammad, jikinsa ya yi ƙalau abin sa, sai dai magana ce babu. Nana ta yi iya ƙoƙarinta gurin tana kauce wa duk wani abu da zai sanya faruwar wata mu'amala tsakaninsu. A ƙasa suke kwana, ba ta taɓa kwanciya sai ya yi bacci, sai dai wasu lokutan ta ji ya ƙanƙameta idan ciwon ya motsa
Sai dai tun da ya warware sosai, take ganin kamar ya canza mata, wani irin kwarjini yake yi mata yanzu, mussaman idan ya saka ta a gaba da kallo duk sai ta rikice. Ta kasa gane take-taken sa. Sai dai ta riƙi karatun Alkur'ani sosai da sosai. Sai dai tun wannan ganin na ƙarshe da ta yi wa Ƙaisar, ba ta sake ganinsa ba, ko a farke ko a cikin bacci ba. Duk ta damu shi ma ta na son sanin halin da yake ciki. Ga shi gaba ɗaya ta rikice, a kwana ɗayan da ta ga jinin nan, ba ta iya tantance wane jinin ta yi ba. Ɓari ko na haila.
Tuni aka ƙara ƙawata ɗakin da kayan alatu, da kayan wanka da shafe-shafe na Imam Hammad, da duk wani abu da za su buƙata.
Yana banɗaki yana wanka, ta gama cika cikinta da kayan marmari, dan ba ta fiye cin abincin da Mahmoudu yake kawowa ba, fruit take samu ta ci ta ƙoshi ta ci nama. Sai da ta fara tsorata kanta da tunanin anya ba cikin ne da gaske ba. Ta yi zurfi sosai da sosai a cikin tunani. Razana ta yi jin yadda ba ta ji alamun fitowarsa daga banɗakin ba, sai ji ta yi ya zagaya hannayensa a cikinta. Duk da ɗakin ƙato ne sosai da sosai amma duk ƙanƙantar motsi tana iya jinsa, amma sam ba ta ji motsinsa ba.
Tsigar jikinta ta hau tashi, ta ji jikinta ya fara tsuma, tana neman ta rasa nutsuwarta.
Ya ɗan yi murmushi ya cika ta, ya nuna mata gadon da yake ɗakin, alamar ta hau ta kwanta. Amma ta yi mursisi ta ƙame a gurin. Ya kama hannunta zai ja ta, amma ta ƙwace hannunta ta ja ta tsaya. Sai ya rabu da ita, yaje ya haye gadon ya kwanta.
Ta tsaya a gurin tana rarraba ido, sai da ta ga ya jima da hawa gadon, ta lallaɓa ta ɗauki fulo ta ajiye a ƙasa ta kwanta.
Kwanciyarta ke da wuya, ta fara jin sukuwar wasu halittu da ba ta san ko na mene ne ba, a cikin ɗakin. Hayaniyar  halittum ya ci gaba da yin amsa kuwwa a cikin kunnuwanta tamkar a filin yaƙi. Wani mutum ta gani ya shigo ta wata ƙofa, ba a iya tantance jinsinsa, ya rufe ko ina na jikinsa, yana shigowa ya nufi gadon da Sayyid yake kwance, ya ajiye wannan takardar, ya nufi wata ƙofa. Da azama Nana ta bi bayansa duk da yadda yake wani irin gudu kamar iska na kaɗa shi. Sai dai wannan sautin ƙarar ya hana ta ci gaba da bin sa.
Rungume ta ya yi a jikinsa, jikinta na ta rawa, duk ta toshe kunnenta da hannayenta biyu. Saboda yadda take jin hayaniyar kamar zata tarwatsa mata kai. Ta ɗaga kai ta kalli Sayyid, ta kalli ƙofar ta ce "Akwai wani abu a nan?" Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya yi gaba, ya buɗe ƙofar. Ya riƙo hannunta suka ratsa hanyar da take baƙiƙirin mai ɗauke da duhu, kai ba ka ce a cikin wannan katafaren ɗakin mai ɗauke da hasken fitilu hanyar take ba. Babu tsammanni ta ga sun ɓullo wani guri kamar corridor.
ShimfaÉ—aÉ—É—en yashin sahara ne a gurin, gurin ya bayar da wani ni'imtaccen sanyi, ga tsilla-tsillar bishiyu da suke a bushe a gurin hasken farin wata ya haske saharar. Ta waiwaya É—aya gefen, ta hango wani irin gini, mai kama da tsaunin dutse, hasken wuta na ci na tashi ta wata kafa mai kama da taga a jikin ginin Dutsen.
Bakinta na rawa ta kalle shi ta ce "Sayyid na san gurin nan, tun kafin na sanka nake mafarkin saharar nan, har na zo na sanka, ina mafarkinka a cikin saharar nan. Kuma a nan nake yawan ganin ka tare da Giyaz. A waccan bishiyar ku ke zama da su Habu ku sha shayi da wasu mutane ma da ban san su ba.
Ina ne nan, kuma meyasa abubuwan da nake gani a bacci suke dawo mini a zahiri, haryanzu ina da ayoyin tambaya da dama a kanka"

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.