Buzu Book 3 Complete Hausa Novel
Reading file: BUZU BOOK3.txt
Chapter 80 of 99
Ya ce "Bar ni Ummi, ni yanzu na shiga hankalina da al'amuran rayuwa, babu abin da ya kai kwanciyar hankali da nutsuwa daÉ—i" Nan ya bata labarin halin da suke ciki da Jamila.
Jikin Ummi ya yi sanyi sosai da sosai, ta ce "Baba idan ka kori Jamila ina za ta je yanzu? Ƙaddara ce Allah ya aiko dole a yi haƙuri da ita. Yanzu dai sirukanka za su ranar Lahadi idan Allah ya kaimu, sun kira ni a waya, an ce ba a samun lambarka. Mijin Nana ya sai duk wani abu da za a tarbi 'yan uwansa da za su zo. Kawowa kawai za a yi kafin su iso. Dan Allah ka kwantar da hankalinka ka bar batun Jamila mutanen nan su zo lafiya su tafi lafiya.
*****
Asal na kwance a gadon Asibiti, Hasna na gefenta ta riƙe hannunta, sai uban kuka take yi.
"Hasna wallahi ina son Hammad, ji nake mutuwa zan yi idan ya sake ni, ga shi haryanzu ban san a wani bugiren ya ajiye ni ba, bai sake ni ba, bai ce mini komai ba. Babanmu ne duk ya janyo mini da zigar Imam Omar."
"Asal ki yi haƙuri mana, kar ki illata kanki a kan sa, shi fa yanzu ya samu wata ne da yake rawar ƙafa a kanta, ke sai ki kashe kanki fisabilillahi"
"Hasna ba ki san me nake ji ba, wai ni ce nake da kishiya, wadda na ɗauka ƙasƙantacciya mara galihu na shiga uku"
Hasna ta rungume ta, ta din ga rarrashinta tana yi mata nasiha.
Kwanan Yusuf huɗu da mutuwa, tsufan Alhaji Zailani ya sake fitowa, duk ya fita hayyacinsa ya yi wani iri. Alhaji Zailani ya zo duba shi, yana ta rarrashinsa yana ba shi haƙuri. Mutane jefi-jefi na shigowa su na yin gaisuwa.
Wani mutum ne ya yi sallama, suka amsa masa ya shiga, duk suka bi shi da kallo, dan babu wanda ya san shi a cikinsu.
AREWABOOKS
Sai da suka Shukura ta biyo bayan mutumin, sannan suka rikice gaba ɗaya suka miƙe, banda Alhaji Zailani. Hajiya Amina ta nufi Shukura da gudu har tana neman faɗuwa, ta rungume ta cikin tsananin tashin hankali da manakin ganinta ta ce "Shukura, ke ce? Ina ki ka shiga aka din ga neman ki, ina cikin jikin naki?" Wani irin tausayin Hajiya Amina ya shiga ran Shukura, ta rungume Hajiya Amina tana kuka.
Alhaji Fatuhu ma cikin matsanancin mamaki yake faÉ—in "Ikon Allah, Allah da girma da iko yake. Sannu Shukura" Alhaji Zailani dai yana zaune yana kallon su, bai ko motsa ba.
Idanun Shukura suka sauka a cikin nasa, ta ji tamkar ta yi tsalle ta shaƙe shi, saboda wani abu mai ɗaci da ya tsirga mata.
Mutanen da ya sabauta rayuwarsu, duk ga su a tare da shi a zaune.
Ta ce "Mummy wai na ga rumfa a harabar gidan nan, me yake faruwa ne?"
Hajiya Amina ta ce "Ba wani abu bane ba, Shukura ina ki ka tafi?" Kan ta ba wa Hajiya Amina amsa ta durƙusa ta gaida Alhaji Zailani ya amsa mata cikin damuwa ya ce "Shukura kin sanya mu a tashin hankali, meyafaru wannan bawan Allah kuma waye?"
Shukura ta numfasa ta ce "Garkuwa aka yi da ni, wannan mutumin Likita ne, shi ne wanda ya taimake ni, a gidansa na ƙarasa jinya"
Suka gaisa da mutumin, Alhaji Fatuhu ya din ga yi masa godiya. Hajiya Amina ta ce "Daddy, ba ka ga Shukura ba, Shukura ce fa ta dawo" Ya sauke numfashi ya ce "Na ganta"
Alhaji Fatuhu ya ce "Haba Zailani, amma atleast yakamata ka yi farincikin dawowarta ko, yarinyar da ake ta nema ba a gani ba, ta dawo kuma ka yi fuska"
Alhaji Zailani ya ce "Ni yanzu ta mutuwar ɗana nake yi, dan Allah ku ƙyale ni" A burkice Shukura ta ce "Wane ɗan nasa?"
Tsit suka yi aka rasa mai yi mata bayani, Alhaji Zailani da kansa ya gaya mata Yusuf ne ya mutu. Shukura ta gigice cikin matsanancin tashin hankali ta hau kuka, tana faÉ—in "Shi ma ka kashe shi ko? Da ni ba a kashe ni ba sai ka kashe mini É—an uwa, wallahi ba zan yadda ba sai na tona maka asiri Duniya kowa ya san abin da ka ke yi" Likitan da ya rako ta, ya tashi tsam ya yi musu sallama, ya ce zai dawo.
Duk yadda suka so Shukura ta nutsu amma ta ƙi, ta din ga surutan da ba su gane kansu ba, kuma Alhaji Zailani ya yi mursisi ya yi shiru.
*****
Nana jikinta har wani sheƙi yake yi, ta yi kyau sosai da sosai, sai dai ganin Hammad ya yi mata wahala, saboda yana ta kai kawon shirin bikinsu. Yadda ta lura lamarin ba da wasa suka ɗauke shi ba, sai gayyatar mutane suke yi. Bangaren Sultan yana ta shan suka, da ƙorafe-ƙorafe, a kan ya ci mutuncin Al'adar da aka gada daga iyaye da kakanni. Bai tsaya a iya nan ba, ya ayyana rushe majalisar Imam da ake da ita. Ya sauke Tafawa, ya sauke Sardaunanda wasu daga cikin muƙarrabansa, tare da cewar za a ayyana waɗanda za su maye guraben su, a lokacin shagalin bikin Hammad da matarsa ta ɓoye da zai bayyana wa Duniya yanzu.
Nana a ranta take ƙara jinjina ikon Allah, sai dai tana ganin lamarin bikin nasu, kamar a ƙasar turawa, sun yi aure sun haihu har da ɗa, sannan za a yi shagalin bikinsu.
Gefe guda sannu a hankali take ƙara yi wa kanta fashin baƙin, bayanan da Ƙaisar ya yi mata a game da rashin lafiya da ya ce ruhin ɗan Adam yana yi. Kuma ga yadda ta fuskanta, babu wani magani tattare da hakan face ka yadda kana da ciwon, sannan ka tsananta addu'a Allah ya raba ka da shi.
Tabbas ko a kankin kanta ta ga misali, ta ƙara samun nutsuwa da yarda da komai lokaci ne, lokacin da take addu'a Allah ya kawo mata ɗauki a kan matsalolinta, gani take kamar ba za su wuce ba, kamar waraka ba za ta zo ba. Ashe wannan addu'a da take yi, ke ƙara samar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali, tabbas banda haka, da irin azabar da ta ci da tuni ta amince da al'amarin bori, ko ma haukace saboda wahala da yadda ratuwarta ke tafiya kamar ba ta mutane ba.
Ta kalli yadda a yanzu ba ta aikin fari bata na baƙi, sai dai kawai a kawo mata ta ci, ta yi ibada ta kwanta. Sai dai ta dage da roƙon Allah, kar Ni'ima ta sanya ta shagala da neman kusancinta da shi.
****
Gidansu Nana, Mama ta yi mamaki, ganin Uwani ta zo ranar Asabar, wai zata kwana, da azahar ma sai ga Ummi da uban kayan cefane, har ma da Yaya Atine.
Mama ta ce "Wai lafiya duk na ganku, meke faruwa ne?"
Uwani ta ce "Kamar yaya meke faruwa? Karɓar kayan auren Nana muka zo ayi da mu mana"
Ta yi saroro ta ce "Nana kuma, wace Nanan?"
"Nana wacce da wacce ku ke da ita a gidan nan? Ba dangin mijinta ne za su zo daga Agadez ba?"
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.