Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 26 of 99

Nana ta ce "Habu, dan Allah É—an tsaya ka taimaka mini" Ya ce "To"
Bayan fitar su Nana ta ce "Dan Allah ka kawo mini kayana, sannan ka kawo mini kayansa guda biyu. Ka kawo mini Alkur'ani. Sai kuma Abincin nan dan Allah duk yadda za a yi kai tsaye daga hannunka zai zo, kar ya biyo ta hannun kowa. Sai kuma ina son ka kawo mini habbatussauda da tazargade, da ganyen magarya sai almiski ja"

Ya ce "In sha Allah ranki ya daɗe, yanzu kuwa. Sai dai su abin da ki ka lissafa ɗin nan, sai dai na shigo da su a ɓoye kar su ce wani abin za a yi masa"

Nana ta ce "Idan da matsala ba sai ka kawo su ba, kawo mini Abincin da kayan kawai, kar na saka ka a cikin matsala. Amma lokacin da hakan tana faruwa da shi da muna Nigeria, idan na yi masa amfani da su yana samun sauƙi sosai"

Mahmoudu ya ce "Kina nufin a Nigeria, yana irin haka?"

Nana ta jinjina kai ta ce "Har ɓarin jikinsa sai da ya shanye, ka kawo mini Abincin da sauri na ba shi"

Ya ce "To" Ya kalli Hammad ya ce "Sannu Imam, Ubangiji Allah ya sanya kaffara"

Sai da Mahmoudu ya fita sannan ta kalle shi ta ce "Cika ni na je na wanke jikina, ka ga ka yi mini amai a jiki" A hankali ya saki hannunta, amma har ta shiga banɗakin nan kallonta yake yi. Ta wawwanke jikinta ta fito ta ƙara goge gurin da ya ɓata da aman.

Matawalle ya ce "Anya abin nan ba shiri ne yaran nan suka yi ba, saboda ya ci gaba da zama da yarinyar nan ba?"

Sardauna ya ce "Nima sai da na yi wannan tunanin"

Sultan ya ce "Bana tunanin shiri ne, babu yadda za a yi ya kwana takwas babu ci babu sha, a kwance a guri ɗaya a ce shiri ne. Kai Matwalle ka manta abin da ya din ga yi, lokacin da aka gano shi a Nigeria aka dawo da shi. Ba magana ba cin abinci a sume kawai kuma aka rasa abin da yake damunsa sai da muka je faransa sannan ya dawo hayyacinsa?" Ya yi maganar yana ƙoƙarin hana kansa, yi musu cikakken bayanin labarin da Mahmoudu ya ba shi, mussaman cewa da aka yi idan aka dawo da shi Nijar, zai iya haukacewa ko ma ya rasa ransa gaba ɗaya".

Sardauna ya jinjina kai ya ce "To ai ita kanta yarinyar abar tsoro ce, ba ku ga abin da take yi ba? Ni abubuwan sun É—aure mini kai sosai da sosai fa"

Sultan ya ce "Tabbas lamarin akwai É—aure kai, da ayar tambaya, dama Hammad ya gaya mini wani abu, amma dai bari mu ga abin da Allah zai yi, sannan mu jira zuwan mai maganin da aka tafi nema"

*****

Mama ce take kallon Jamila cike da baƙin ciki da takaici. Kamar ta danne ta ta yanka ta ce "Jamila, so ki ke sai duniya ta san halin da muke ciki? Kin zaɓi mutuncinmu ya zube a rasa wanda zai aure ki saboda wannan abin kunyar. Tun kafin ya riƙa mu je a cire shi kin ƙi, Jamila kin fi son asirinmu ya tonu ko?" Ta yi maganar muryarta na rawa.

Jamila ta girgiza kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Mama ba zan iya zubar da cikin nan ba wallahi, ni tsoro nake ji, kuma kar zunubin ya yi mini yawa ba ki san adadin tarin zunuban da suke kaina ba. Ki bari na ji da wasu dan Allah, ki ƙyale ni kawai"

"Jamila ni ki ke cewa na ƙyale ki? Kin gwammaci ki durƙusa ki haife mana shege a gida, Duniya ta gani a shaida?"

Mama "Na duniya daga baya ne, Allah ya riga ya shaida ya ga komai, ni yanzu addu'ata Ubangiji Allah ya yafe mini. Wataƙila haifar ɗan nan ne zai sanya na samu nutsuwa ni dai dan Allah ki ƙyale ni"

Cikin takaici ta ce "Jamila kin san haihuwa kuwa? Kin san azabar haihuwar É—an sunna balle shege, tsaf za ki mutuwa fa"

Jamila ta goge hawayenta ta ce "Idan na mutu gurin haihuwa na yi shahada, wataƙila Allah ya yafe mini tarin kura-kuren da na aikata"

Cikin tsawa ta ce "Uban waye ya ce miki mai cikin shege za ta yi shahada"

Jamila ta ce "Mama ba ki san tarin zunuban da suke kaina ba, tuban da na yi sai Allah ya karɓi shahadata." Takaici ya sanya Mama fara rafka wa Jamila maficin hannunta ta ko ina. Jamila ta tashi da sauri, amma ta bi bayanta tana ci gaba da raɗa mata.
Baba ya kawo kai cikin ɗaga murya ya ce "Rabi, wannan wane irin rashin imani ne haka? Yaya yarinya ba ta da cikakkiyar lafiya za ki biyo ta kina duka, me ta yi miki?" Mama ta tsaya tana mayar da numfashi cike da baƙin ciki da takaici.
Suwaiba kuwa da take gefe, ta din ga tuntsura wata irin dariya mara daÉ—in ji, wadda ke bayyanar da rashin cikakken hankali ga mai yin ta.
Mama ta rasa ihu za ta zunduma ta ji daɗi, ko kuma me yakamata yi ta ji sanyi. Hutu da fatan arzikin da take da shi a kan 'ya'yanta duk ba ta samu ba, ga mahaukaciya ga karuwa Nasiru shi ma ya fara 'yan ɗauke-ɗauke, dan sau biyu 'yan vigilant na kama shi, da laifin satar tukwanen mutane da kayan ƙarafa ya sayar da sunan gwangwan. Dan tun da Jamila ta cire tallafin da take ba su, ta daina zuwa gurin Hajiya Sa'a, suka koma ruwa.
Baba ya ci gaba da yi mata faɗa a kan dukan da ta yi wa Jamila, ba tare da ya tsaya ya ji cikakken abin da Jamilar ta yi ba. Ji ta yi tamkar ta kama shi shima ta jibge shi, ko ta huce. Dan duk wannan masifar shi ne sila da ya tsaya ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa da wataƙila ba su shiga wannan halin ba.
Babban abin da ya ƙara ɓata mata rai, shi ne rashin zuwan Hajiya Sa'a ta duba Jamila, duk da taga kwana biyu ba ta zuwa maimakon ta neme su ta ji ko lafiya amma ba ta yi hakan ba. Ga Maman Khairat ta tashi daga unguwar da ta so zuwa a rakata gidan Hajiya Sa'a ta ji ko wani laifin Jamila ta yi wa Hajiya Sa'a haka?.

Hajiya Sa'a kuwa tana can tana fama da kanta, dan tun mutuwar Abba ta shiga wani mawuyacin hali, duk lokacin da ta zauna babu abin da take yi sai tunanin ko yaya Abba ya ji da dodon ƙungiya ya zuƙi jininsa har ya mutu? Ta daina bibiyar duk wani abu da ya shafi kungiyar. Kasuwancin ma ta tattara ta ajiye a gefe ta koma guri ɗaya kawai. Daga kuka sai kwanciya da dana sani. Ga shi da ta fara tunanin wani irin mummunan ciwon kai yake yi mata dirar mikiya, har sai ta daina gani sosai. Wasu lokutan haka zata kulle kanta a ɗaki ta wuni, sai dai mai aikinta ta yi ta sabgoginta itakaɗai. Ta ce ko mutanenta sun zo, kar a bar kowa ya shiga inda take, kaɗaici kawai take so.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.