Trending Hausa Novels

Buzu Book 3 Complete Hausa Novel

Reading file: BUZU BOOK3.txt

Chapter 59 of 99

Ya tashi ya fita, ya ɗauki mota ya bar gidan. Ya yi tafiya mai nisa aƙalla ta awa guda sannan ya iso wani makeken katafaren gida. Bayan ya shiga da motar ya ajiye, sai gaishe shi hadiman suke yi yana amsa musu cikin girmamawa.
Ya shiga cikin gidan ya bi wata hanya ya hau kan bene.
Ya ƙwanƙwasa wata ƙofa, sannan ya saka kansa ya shiga da sallama.
Yana zaune ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya, yana cin inibi tare da wasu ƙanan yara su uku, jikin bangon ɗakin kuma ƙatuwar TV ce take yi, ana shirin cartoon.
Cikin nishaÉ—i yaran ke ta cin inibin su na zubarwa, É—aya daga cikinsu kuma yana jikin mutumin yana tana jagwalgwala nasa inibin cikin nutsuwa.
Sallamar da ya yi ne ya sanya su waiwayawa, Muhsin ya jefar da inibin hannunsa, ya nufi Mahafinsa da gudu. Hammad ya ɗaga shi yana murmushi ya ƙarasa shiga cikin falon sauran yaran maza su ma suka nufi Hammad.
Ya rungume su yana murmushi ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Kai ne ka ke wasan da su da sassafen nan?"
Zahradeen ya yi murmushi ya ce "To ya na iya, su wannan biyun sun hana mamansu sakat da rigima, shi ma Muhsin sai kuka yake yi yau, yana kiran Umma, duk sun rikitata, shiyasa na kwaso su muka dawo nan"
Hammad ya yi murmushi ya ce "Ina godiya sosai da sosai"
Zahradeen ya tsuke fuska ya ce "Da aka yi me?"
Hammad ya sake yin murmushi ya ce "Tuba nake baban Muhsin"
Imam Zahradeen ya zauna sosai ya ce "Yaya ake ciki ne? Sultan bai kuma ce maka komai ba haryanzu?"
Hammad ya girgiza kai ya ce "Ina dai jiran abin da zai ce, kawai dai yana yawan ce mini, sai abin da aka yanke na shawara"

"Ka ga Imam, ka tsaya ka nutsu da kyau ka duba makomarka da makomar wannan jaririn yaron naka. Yaron nan na buƙatar mahaifiyarsa, kuma ina ganin ka dawo da mahaifiyar Mahmoudu gidan nan, su zauna kafin komai ya daidaita, na ga ya saba da ita sosai. Ka san ba abu ne mai sauƙi su bari ka fito da ita daga gidan nan ba. Saboda ina tsoron shawarwarin da Matawalle da kum Sardauna za su yanke a kan matsalar nan. Ba dan kar na yi musu ƙazafi ba, da na ce sun fi mutunta Al'adar Agadez sama da addininsu."

Hammad ya ce "To ina nan dai ina sauraren su, na ji hukuncin da za su yanke É—in"

Imam Zahradeen ya ce "To, Allah ya sanya mu ji alkhairi"

Imam ya amsa da Amin.

****
Jikin Shukura ne yake tsuma, tana kallon Yusra a inda suke ɓoye, ga ta rungume da jariri da yake ta ƙoƙarin farkawa ya tsala ihu.
Yusra na riƙe da jaririn tana yi wa Shukura alama da ta kwantar da hankalinta.
ÆŠaya bayan É—aya mutanen suka fita daga cikin É—akin, É—ayan ya kira wayar Alhaji Zailani. Yana É—agawa ya ce "Yaya kun same ta?"

"Alhaji mun caje Asibitin nan kaf bamu ganta ba, ga shi sun yi mana barazanar kira mana jami'an tsaro kar su kama mu"

"An bani tabbacin ta na cikin Asibitin nan, a yadda binciken nan ya nuna, dole ku nemo ta ba sai na ganta ba ku kashe ta kawai, dan ba za ta tona mini Asiri ba"
Jaririn hannun Yusra ne ya tsala uban ihu, hankalin mutanen ya dawo kan É—akin, É—aya daga cikin su ya juya da sauri ya nufi É—akin.

*****

Nana tana tsaye a gaban mudubi, ta saka riga ta alfarma, gaba ɗaya jin ta take kamar a cikin tarko, ta gaji da zaman guri ɗayan nan, hankalinta na kan a ƙarƙare abin da za a yi, a bata ɗanta ta koma Nigeria.
Gefe guda kuma zuciyarta na ci gaba da wasi-wasi da son lallai sai ta ga mene ne a rufe a wannan É—akin na gidan tarihin Agadez.
Asal ce ta bankaɗo ƙofar ɗakin da ƙarfin gaske sai da Nana ta tsorata. Ta kalli Nana cikin doguwar riga mai maɗauri, ko 'yar uwatta mace zata sarawa kyawun dirin da Allah ya bata, balle ɗa namiji.
Wani abu ɗacin gaske ya taso wa Asal, Gimbiya Bilkisu ce ta biyo bayan Asal. Nana dai ta tsaya ƙyam tana kallon su.

AREWABOOKS

Da sauri ya dawo, ya buÉ—e É—akin jin kukan jariri, kawai ya tarar da Yusra a zaune a kan gado, tana jijjiga jariri.
Cikin tsawa ya ce "Ke, me ki ke yi a nan wace ce ke?"

Yusra ta ce "Kamar yaya? Nice a É—akin nan, lafiya suwaye ku?"

"Ya aka yi da muka shigo É—akin nan bamu ganki ba?"

Yusra ta ce "Ku na tsaye a bakin ƙofa na zo na wuce ku, na je na karɓo jaririna daga ɗakin jarirai ne, an sallamo shi daga can"

Ɗayan ya ce "Ke ƙarya ki ke yi, mene ne sunanki?"

Yusra ta ce "Ban gane mene ne sunana ba, suwaye ku tukuna me kuma ku ke nema a gurina ni ban sanku ba"
ÆŠayan ya dubi hoton cikin wayarsa, ya kalli Yusra ya ga sam babu haÉ—i.
Ya tunkaro Yusra ya ce "Ki gaya mana mene ne sunanki?"
"Yusra, sai kuma me?"
"Na ke ce wata mata ta tsinto, ta kawo Asibitin nan ba?"
"A ka tsinto kuma kamar wata kuɗi? Ni ban san zancen ba, mijina tare muka je na ɗaukko jaririna. Yanzun nan yayata kuma za ta dawo da take zaune tare da ni. Amma mene ne dalilinku na zuwa ku ritsa ni kuna tuhuma ta." Ta yi maganar cikin dakiya tana tsare mutumin da ido. Ƙasam zuciyarta fata take yi, Ubangiji Allah ya sa kar Shukura ta ce za ta fito ta tona musu asiri.
Ɗayan ya ce "Ba fa ita ba ce ba, mu koma mu gaya masa ba ta Asibitin nan, ba a ba shi bayanin daidai ba" Suka ƙara ƙare wa Yusra kallo sannan suka fice.
Abin da ya faru kuwa, Shukura babu yadda ba ta yi da Yusra ta tafi ba, amma ta ce babu inda za ta je ƙafarta ƙafarta, ba za ta tafi ta bar ta ba. Ga shi ta uzzura mata da tambayoyin yaya aka yi ta ɓata aka neme ta aka rasa. Alamu ya nuna mata haryanzu Yusra da saura kan babu daɗi dan haka ta ce mata sace ta aka yi, ta kuɓuta da ƙyar shi ne wata mata ta tsinto ta ta kawo ta Asibiti.
Yusra ta ce "Lallai kin auna arziki tashi mu tafi to"
Shukura ta ce "Ai ba a sallame ni ba, ba zai yiwu mu tafi ba, ba ni da cikakkiyar lafiya fa"
"To ba sai mu koma Asibiti a can cikin gari ba, kin ga yadda mamanki ma hankalinta yake a tashe, idan muka je da Baban Haidar ta yi ta kuka"

Wata Nurse ce ta yi sallama, suka gaisa da su Shukura, ta yi wa Shukura allurai. Wata ce ta sake shigowa da sauri, ta kalli Shukura ta ce "Ke ce Shukura ko?"
Ta jinjina kai.
"Wasu mutane ne suka zo, wai 'yar uwassu ce ke dubiya suka zo, amma yanayinsu kamar marasa gaskiya, mun ce babu mai wannan sunan, saboda mun san case É—inki, amma ga shi can ana ta faÉ—a da su sun ce sai sun caje Asibitin nan, 'yar uwassu ce ke dole su ganki"
Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskar Shukura.
Nurse É—in ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ai an kore su ma, kar ki damu" Bayan sun fita a rikice ta kalli Yusra ta ce "Ina ga wanda suka sace ni ne suka biyo ni nan, dan Allah ki tashi mu tafi "

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.